← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 85

Sashe 72

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Subhanallahi kinga ma kin zo a gaɓa ai kamar naƙuda take yi ma? " Asabe ta iso a guje wajena tana wani tarairayata, yadda kuka san zaman lafiya muke yi haiƙan ɗinnan. Inna Mairiga dai hijabin jikinta ta cire tazo ta kamani, tana kwatantamun in dinga ambaton summas saliba yassara. Saina kama inata nanatawa ciwo ya ƙi ci, yaƙi cinyewa. Asabe na kaina tayi kane_kane. "Inaga kije Uwargida zan kula da'ita, kinga in banda abu na lalura babu yadda za'ayi kishiya ta tsaya kan kishiyarta yayi naƙuda, ko ba gaskiya ba? Kuma wannan dalilinne yayi sanadin zuwana ma. Amman kiyi haƙuri ƴannan" Ga ciwo na cina amman sai naji daɗi. Asabe ta fita ba guiwa To haihuwa in yita a gida abu ya gagara. A asibitin ma da suka ga dugu, dugu wajajen asubahi kawai suka ce a saka hannu aiki za'ayi mini. Ina miji, bayanan wayarshi a kashe, sai lokacin Asabe take cema Innah mairiga ai tafiyace ta kamashi ta kwana huɗu. Ni dai bammasan inda kaina yake ba, ita ta saka hannu a takadda aka ciromun yarona sunkucece lafiyayyen gaske. Asabe ce ta biya duk ɗawainiya, ashe ita ya danƙama kuɗi uba_uba a hannunta. Kwananmu huɗu a asibiti aka sallamemu. Dake na jigata gaya. A ranar da muka koma oga ya dawo daga tafiya ana jibi suna, na kira anyi mun kitsona, gobe nake so nayi ƙunshi. Muna zaune da daddare Innah Mairiga tana zaune tatusani gaba inacin tuwo miyar kuka, yaji manshanu ga yajin daddawa an gabzamun, wanda Innata tayo mun. Sai kunun kanwa a gefe ina korawa. Muka jiyo sallamarshi ya shigo kadaran kadahan. Innah mairiga ta miƙo jariri ta bashi ya karɓa. Duk da jaririn shine jaririnshi namiji na farko baisa ya samu salama a fuskarshi ba, bani ba hatta Innah mairiga ta tsinke da wannan lamari. Miƙewa tayi ta shige ciki ta bamu waje. "Gashi nayi mishi huɗuba da sunana. Allah ya raya. Dukkan abinda kike buƙata sai ki ma Asabe magana. Kuma washegarin suna a bisa al'ada da yamma zaki tafi gida wanka kuma. In kika gama sai in zo in ɗakkoku" A jikina nake ji ba lalle in sake dawowa ba, haka na dinga ji har zuwa ranar suna. Ragone aka yanka ma yaro Haruna, dake kudune kuma danginshi ba yina suke yi ba. Shinkafi mudu uku kacal aka dafa da lemun kwalba, shima sabida kara da maƙota suka yi ne. Ni ina kwance ma babu lafiya mamana ya suntuma kan yana tsagewa harda jini_jini, gashi a haka nake cirowa in ba Haruna zafi kuwa har maɗigata nake jinshi. Zuwa bayan magriba Innah mairiga ta dinga tattare mun kayayyakina tana adanasu, ni kuma ina haɗa akwatin kayan Haruna da abubuwan buƙatana. "Naga duk kin sakko da akwatunanki dasu zaki tafi ne" A, a atampopina masu tsada zan cire da dai duk wasu abubuwa masu tsada Innarmu, kinga cewa yayi aba Asabe kin ɗakin" Shiru tayi taci gaba da aikinta can kuma meta tuna oho sai ca tayi. "Ki ɗauki duka kayan akwatin naki, da duk abinda kika sani mai tsada. Kinga kayan sawanki na ciki? Kada ki bar ko ɗaya jiƙaƙƙun ƴan kamfanki da kika wanke ɗazu ki zuba a leda mu tafi dasu. Amman taya za'ace aba kishiya kin ɗakin Kishiya ne ma? " Allah ya kyauta kiyi haƙuri aure babu da irin turka_turkar da baya xuwa dashi. Matsalar wannan daban da matsalar wannan. Wama ya zaci ƴar wasan kwaikwayo dake zaki yi irin wannan haƙuri, ku da ake cewa zaman aure na gagararku. Sai gashi ke baki da fada a gidanki, kishiya ke mulkin gidan, amman kin daure kin... Burum Asabe ta shigo babu ko sallama da jakar buhu kano ta ɗau zafi a hannunta. Ganina da akwatuna na baje su a gaba sai tayi turus. Me ta tuno_ me ta tuno, ohon mata sai ta yashe baki, ta gaishe da Innah mairiga itace har da zama a bakin gadona. "Mai jego irin albarka ga kayan suna inji Baban boi. Atampa uku, sai mayafi da rigar yaro biyu da pampas me takwas. Wallahi kunji rantsuwar ɗan musulmi, shikenan abinda aka bani na suna. Sai atampa da sabili da dubu hamsin na Innah mairiga. Wannan ma kam tace ita tayi ma Innar ba Haruna bane yayi mata ba." Fasali Mariya ta ja tare da ɗebe hawayen dake fuskarta a ƙoƙarin ganin ta danne damuwar, amman ina sai kawai ta fashe da kuka mai gunji. Duk dana dubesu hawaye suke taya ta sharewa. Ajjiyar zuchiya na sauke kawai tare da cewa. Duk wacce kuka gani tana da labarin bayarwa a rayuwarta. Mata muna ganin rayuwa a hannun mazajen da basa jin tsoron Allah. Waɗanda suka more ire_iren Nana Kabiru kuwa, su da rijalu sai son barka. Matan da suka auri masu koyi da Arrasul SAW, ku gode ma Allah, kuma kuyi musu biyayya. Har kullum ina daɗa jaddadawa mata a nemi na kai, kar ki sake da wasan _wasa ace baki da sana'a a hannunki. Wacce taji ba zata iyaba, ga waje tayi zaman daɓaro. Sannan a nemi ilimin sanin Allah, kuma ayi ilimin boko. Ko kuma ki kasance ma'aikaciya, sannan banda raina sana'a ko riba." Ajjiyar zuchiya na sauke kafin nace. Mariya bayan kin dawo gida, Haruna baizo ba sai takaddarki ya turo miki ko? " Na tambayetane sabida ta dena kukan haka. Tun kafin ta kaini wuya. "Kamar kin sani Duwaf. Daga wankan gida shikenan Aure sai ya ƙare. Kafin auren ya mutu maƙota da ƴan unguwa tuni sun soma gulmammaki, labari ya baza unguwa kan doron jita_jita, a lokacin wata uku nayi a gida kunga ai wanka ya ƙare. Tun anayi a ɓoye har aka soma shigowa tambayar yaushe zan koma, dangi suma suka matsa sosai, akan batun komawata, musamman Dangin Babanmu. Dana cika wata na huɗu. Sai ƙanin Babanmu yace in bashi adareshin gidan namu na can Lagos, tunda wayar Haruna bata shiga sam. Na rubuta mishi adireshin, a ranar ya kama hanyar Lagos kwananshi biyu sai gashi da yamma sakaliya ina tuƙin tuwo a tsakar gida. "Ke Mariya zo mu tattauna a gurguje." Muciyar na ajjiye na nufeshi yana zaune a tabarma a ɗakinmu. "To naje Lagos yadda kikai mun kwatance, na tarar da kishiyarki Asabe ko? " Eh kawu Asabe" "To shi Haruna sanda naje baya gidan, Asabe tayi mun tarbar kirki har Harunan ya shigo muka tattauna. A yanda yace wayarshi ce aka sace mishi shi yasa kika jishi shiru. Kuma akwai tafiya da zaiyi na wata biyu in ya dawo dakanshi ma zai zo ku tafi. To Amman ni Kattume saina fahimci ba lallai yaronnan yazo ba, a yadda ya tarbeni. Ke Mariya me kika yi mishi ki gayan gaskiya, dama ku ƴan wasan ƙwaiƙwayo baku fiye zaman Aurenku ba. Shi yasa mu dai bamu so wannan sana'ar ba. Nifa a unguwarmu wallahi har nuna ni akeyi, ga uban ƴar fim" Haka dai Kawu yaita sababi, kafin yayi mana sallama. Ni dai a ranar akan sallaya na kwana. Bana so Aurena ya mutu sabida yadda Dangin Babanmu suke zuwa suna matsama ummanmu, har kuka take shigewa ɗaki tai ta yi. Nima inna jiyota tana kukan ranar haka zan wuni a ɗaki cikin damuwa matsananciya. Ranar da muka cika wata shida sai ga kiran Haruna ya shigo wayata. Da gudu naje ina nuna ma Ummanmu. "Maza ɗauka Mariya. Allah nagode ma. Abinda tace kenan ina ɗauka bayan mun gaisa sai cewa yayi. " Na sakeki in kin samu miji kiyi aure. Yarona kuma in kika yayeshi zan zo in karɓeshi in haɗashi da ƴan uwanshi" Mama ta karɓi wayar a hannuna ta kashe. Mukai shiru a tsaye a wajen a haka Innah mairiga tazo ta taddamu cirko cirko, wallahi munfi minti talatin a tsaye kafin zuwan Innah Mairiga. Da ƙyar Mama ta labarta mata halin da ake ci. "Mairiga babbar damuwata shine ki duba da yadda akayi Mariya tayi Aurennan. To yanzu gashi ya mutu, dama anata cewa ba zata zauna ba. Dangin mahaifinsu laifina suke ta gani. Kawunsu kullum cikin sunturin jin ba'asi yake. A unguwa an takura mana da gulma, Mairiga ki tafi da Mariya dan Allah. Kuma ban yadda ta koma harkar film ba." "Yaya ki dena damuwa da maganar mutane mariya zan tafi da'ita. Kuma mu yadda da ƙaddara, mu sa a ranmu ba sabida ta kasance ƴar film bane Aurenta ya mutu ba. Ke Mariya haɗo kayanki muje ba shikenan ba ne. Haka na haɗa kayana sanadiyyar konawata hannun Innah Mairiga kenan. To bafa ni na fita idda ba sai bayan shekara ɗaya tim da sakina da Haruna yayi. Sabida saida na yaye Haruna kafin na soma al'ada na sauke iddata. Sai rayuwa taci gaba gaga_gaga, ga maneman amman ba batun aure sam. Zamam waje ɗaya ya dameni, ba karatu, ba sana'a, kwatsam za'ayi wani shiri sai ƙawata ta kirani tace inzo odishon gashi_gashi. To Mama da ƙyar dai ta yadda sai na sake tsintar kaina a masana'antar a karo na biyu, akaci gaba da damawa damu rayuwa ta yi kyau fiye da lokacin farkon ma. Masoyana basu mance dani ba, anata murnar ganin dawowata. Akaita ɗaurani akan fina_finai alhamdulillahi ina samun na rufin Asiri. Haruna kuwa yana ganin fina_finaina yazo ya karɓe yaronshi, harda faɗamun da yayi niyyar barmun shi, amman a yanzu tsoron kar in sakashi harkar fina finai yasa dole ya rabamu. Luba tace. "To yaya kika yi kika sake Aure, ya fitowar taki ta kasance?" Katse Luba nayi ta hanyar cewa. Ni a wannan lamarin Asabe tafi bani mamaki a matsayinta ta mace. Itace matsalar auren kacokan. Ina mamakin abinda mata suke yi akan maza wallahi. Sai mace ta cutama ƴar uwarta mace, mace ta hana ƴar uwarta mace zaman aure, kuma ita tana so ta zauna akan nata auren, tana so kuma a Auri nata yaran suma su zauna. Dukkannin matsalolin ƴan uwa mata da sanya hannun mace a ciki. Mata wai yaushe kukai irin wannan lalacewarne? Ko da yake Manzon Allah yayi gaskiya da yace yaga mata danƙam a wuta." Saudat tace. "Gashi Asaben ƙware sosai. Amman duk yadda akayi Asabe bata aiki, bata sana'a ko Mariya? " "Bata yi, nima banayi. Shi Haruna gani yake yi aiki ko sana'ar mace na da alaƙa da gazawar mijinta, wannan itace fahimtarshi gaskiya. Kuma dani da
Chapter 72 · 0% Book details