Sashe 14
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na iso lafiya malama Hindu. Ina cikin damuwa bani da uwa bani da uba bare inje su share mun hawayena. Mahaifiyata ni kaɗai ta haifa a gidan Babana, ina da ƴan uwa wanda ta haifa a wani gidan, su kuma babu shaƙuwa a tsakaninmu kasancewar bamu rayu waje guda ba. Kinsan irin wannan sai dai a hankali." Ajjiyar zuchiya na sauke nace da'ita. Yanzu dai abinda ya kamata kiyi sallah, kici abinci in kika ɗan samu nutsuwa sai mu tattauna" "To shikenan nagode Allah ya ƙara haɗe kanki ke da mijinki. Ya yara miki yaranki Malama" Hmmm Sabira'Sabira" Na shiga kiran Sabira. "Na'am Ammi" Ta amsa tare da zuwa da sauri" Ki kai baƙuwa ɗakinki tayi sallah ki bata abinci taci ko?" "To Ammi, taso muje bari in riƙe miki goyon" Sabira ta sunce goyonta na yarinya mace sai ƙarni suke yi daga ita har ɗiyar. Tishet ce a jikinta sai zani ballagaza a tsaye da hula komai dai daban hijabinta duk jurwaye. Ohh irin wannan matan da gaske suna kiran kansu da mata, wannan ƙazanta da me tayi kama. Haka suka wuce ɗakin Sabira. Jin sallamar Azgar da Mijinyawa yasa na tashi nayi komawata cikin ɗaki na zauna ina bin tattaunawar yadda bikin Salamatu zai kasance da ranar da zamu wuce katsina kai Amarya da su batun anko namu yaran gida dai. Sabida ƙarya irinta Salamatu leshi ta fitar na dubu hamsin a matsayin anko tasan a cikin gidan akwai marasa ƙarfi da yawa, waɗanda a wahala zata saka su, in ko ana ha maza ha mata zasu siya, sai dai a barsu da biyan bashi. Bamu taɓa cire anko mai kuɗin wannan ba sai dai ku cire iyakar ɗakinku kuyi da ƴan uwanku ku ƙara mai tsada yanda kuke jin ƙarfinku ya kai. Na fahimci za'ayi ƙarya sosai a bikin inaji ana batun gobe za'a kawo akwati da yamma ana buƙatarmu a gidan. Shigowar Sabira yasa na ɗago. Ta ci abincin? " "Taci Ammi sai kuka take yi" Da sauri na fito ina hango mijinyawa a Kicin yana zuba miya baƙin cikine ya turniƙeni akan abincina daya taɓa mun. Tsayawa nayi na dubeshi da kyau. Yana da kyau ka sani cewar nan ba gidanka bane, kuma ban siya dominka ba, balle danginka ba. Ɗazu sun zo sun ɓata mun gida na ƙyalesune sabida bansan sun ɓata ba sai da suka tafi. Sun ɗebi abinci wannan bai dameni ba sabida kai ka siyo in da sun so sun kwashe duka ma babu abinda zai dameni. Abinci yaranka ka siya ma, kuma su na girka ma sabida haka bani" Na miƙa hannuna ya ko saka mun kwanon a hannuna. Zai yi magana na runtse idanuna nace. Kul ba wajen bane, kada ka sake ka ce mun komai." Tuwon na mayar cikin kula, miyar na juye a tukuna, daga tsayen na saki kwanukan suka tarwatse dama faɗi ka mutu ne. Shiga nayi na sameta tana ta sambatu tare da ambaton Baballe. Zama nayi kusa da'ita na dafa kafaɗarta. Wannan kukan da dogaro da ɗa namiji shike halaka matan zamaninnan, sabida mazan wannan zamanin ba duka bane masu zuchiyar imanin tausayama mace ba. Mu kuma mata mun dage ko da daɗi ko babu daɗi sai mun yi zaman aure. Mun mayar da kanmu ƴan a mutu ma Aure duk tsanani. Jibi rayuwar Shanono yadda tayi kyau har ta zama lauya bayan rabuwarta da Kaila Ita kaɗanta abun buga misalice ga mata ire_iren masu zuchiyar dole sai sun yi zaman auren dole ko da cutarwa. Bama musulunci bane akwai haƙurin da cutarwane ba haƙuri bane. Ki dena kukannan ki faɗa mun ni abinda ke tafe dake kar mu ɓata ma kanmu lokaci, ina da abubuwan yi, ga aiki ban jima da dawowa ba ga hidimar gidana. Kin tusani gaba da kukan banza akan wani azzalumi da bai san daraja da kimar hawayenki ba. Wai me kuka yake amfanar muku ne?" Raina dama a ɓace yake tana neman ƙaramun fireja. Na hasala nazo iyakar wuya. Na tsani inga mace tana kukan banza kukan da babu mafita a cikinshi. Shi yasa inna tuno Sabuwan Babangida kaci gari sai inji tamkar in damƙota in hayeta yadda take hawaye akan komai. "Kiyi haƙuri malama abinda Baballe yayi munne da ciwo wallahi. Shekararmu ashirin fa da aure yara goma cib nake dasu sai dai dukka mata Allah ya bani. Tsangwamar dangin miji da shi kanshi mijin iri daban daban babu wanda ban fuskanta ba. A hakan lokacin haihuwata ta shida mahaifina ya rasu aka raba mana gado miliyan ɗaya ce na gada Baballe ya saka mata rani yai tamun barazana iri_ iri da saki akan sai na bashi wannan kuɗi ya ƙara a kasuwa. Takalman roba yake saidawa a baro a bakin kasuwar kwari. Haka na bashi ko kwandala bai bani ba Malama. Rayuwar taci gaba a haka. Yanzu kayan ɗakina kab ya kwashe ya siyar katifa ya jefar mana ni da yaran kawai. Bance mishi komai ba sai yau ɗinnan da yamma sanda na kiraki wai masu jerene suka zo jere a ɓarayin gidanmu da aka gyara ya lashe kuɗaɗe yai ta ce mun ƙaninshi ne zai dawo da iyalanshi, ashe Baballe aure zaiyi ranar Juma'a za'a ɗaura Auren da kuɗin kayan ɗakina ya biya sadakin. Wannan shine abinda ya faru bani da kafaɗar da zan jingina in yi kuka a share mun hawayena" Sai ta kuma fashewa da kuka harda jiniya tana fyace majina da bakin zane. Ƙur nayi mata a zahirance ita nake kallo a baɗinance kuma nazari nake yi tare da rarrabe kalmomi da haɗewa domin in gane kan labarin da kyau in san kuma a wacce gaɓar ya dace in tambayeta in akwai tambaya. Nisawa nayi nace. Naji duk abinda kika ce. Inna lura na fahimta danne miki hakkinki da yayi na miliyan ɗaya kuɗin gadonki, bai dakeki kamar kayan ɗakinki da ya sarayar ya kai sadaki ba ko? " Sai tace cikin rishin kukan iskanci. "Kishiya fa malama zai mun ya siyar mun da kayan ɗakina ya ƙara a hidimar shirin bikin fa. Duk baƙar wahalar da nasha a gidan Baballe ina zaune yayi gini mai kyau zai saka mace fa" Kina da Sana'a a hannunki ko wani aiki da kike yi ki samu kuɗi, ko da babu yawa ɗan taro da dai sisi? "Bana aikin komai da a baya nayi wankau sai ciwon ɗan kakkare ya tusoni gaba ba wuya nayi dole na haƙura. Ita babbar ƴar tawa kafin tayi aure ta ɗanyi suyar Awara a ƙofar gida, kuma ana samu amman jarin ya durƙushe tunda a ciki muke matsaltsalunmu. Komai fa in banyi ba, shima bayayi tunda yaran matane, yace duk wahalace zai yi a banza dasu" Inna fahimceki Baballe baya baku abinci wadatacce? " Kai ta girgiza tace. "Baya bamu sai sanda yaga dama, ca yake wai rayuwarmu bata da amfani na kama na cika mishi gida da yara mata. Sai yaso zai kawo masara ko dawa ko gero a tsabarta, ni zan nemi na niƙa da kuma na miya ko da kaɗa ƙwarya ce in mana" Hmmm makarantar yaran fa? " "Suna islamiyya itama wani bawan Allah ne yake neman marayu zai taimaka musu shine na fita na roƙeshi ya saka mun su a islamiyya, a bar bokon ma su samu na muhammadiyya. Shine suke zuwa. Babbar dai mijinta ya sakata a makaranta tana yin na bokon" Hmm to inna fahimta da kyau, kuma lissafin nawa yayi daidai. Kishin Baballe kike yi kenan, mutumin da baisan kimarki da darajar Ƴaƴa mata ba, har yaran da Allah ya bashi? Tabb akwai aiki a arewa mai girma, ko yaushe mata zasu gane ba'a zaman aure da zalunci oho' ko yaushe mata zasu gane sana'a ko aiki na da matuƙar mahimmanci a rayuwarsu oho. Ko yaushe mata zasu gane rabuwa da miji azzalumi bashi bane ƙarewar rayuwarsu ba oho. Ko da yake sai da ilimi ake aiki. Amman sana'a ba sai da ilimi akeyi ba. Ko dan na taso na tadda mahaifiyata ƴar gwagwarmaya ce oho. Yanzu ke madadin ki nemi yadda hakkin dukiyarki zai fito sai kika ruɗe a ƙarin aurenshi mutumin da baisan mutumcinki ba, baya son yaranki, baya baku wadataccen abinci shi kike runtumama kuka ƙaƙas dan zai ƙara aure, ashe ba zaki iya dakewa in duk matan duniya zai aura ba. Ƙila ma a gabanshi da zubewar aji da girma kin yi kuka tunda mu mata mun ɗauki kuka wata hanyace ta karya zuchiyar ɗa namiji ko? Su kuma suke ganin kamar logonmu kenan. To ya kamata ki farka ki dawo cikin haiyacinki ki yi watsin ruwan tsarki da sha'anin Baballe da aurenshi ki fuskanci tarbiyyar yaranki da sana'a, ki kama girma da mutumcin kanki, ki ja gefe a rayuwar Baballe. Dan tunda kince baki da kowa bazan ce ki kashe aurenki ba yara goma kam kinci gida, amman ki dinga kallon Baballe a matsayin Yaya ko Kawu kin huta. A na me zaki ɗaurama kanki hawan jini a kan aure, ku kuke bayar da mata wallahi, ku kuke sa a raina mata sama da ƙasa. Wallahi banga ɗa namijin da ya kai ya isa in yi mishi kuka ba, ko da kuwa shine wa. Sannan dan Allah ki dinga tsabtace jikinki kiyi wanka a ƙalla ko alim ki dinga gogawa a hammatarki, ko farar hoda yana ɗauke gafin hammata. Jibekki yarkace _yarkace babu yadda kike, daga ke har goyon naki babu fasali kamar ba mace ba. To yanzu ma me kike so ayi miki kina so in shiga kuɗinki ya dawone ko kayan ɗakin ki? " "In so samu ne duka biyun" Na nisa nace da'ita. To kinsan in akace za'a tafi da Baballe ofishin ƴan sanda a tuhumeshi akan kayanki da kuɗinki zai iya zuchiya ya sakeki, shin kin shiryama hakan ko da ya faru? In kin shirya babu komai tunda ko sakin ki yayi to ya zame mishi dole ya kama muku haya ya biya, kuma ya baku abinci ya kula da duk ɗawauniyar yaran, ko yaƙi ko ya so." Sai tayi jimm tana tunani. Ki bari ki nutsu kiyi nazari zaki iya kirana a waya ko ki zo ai kinga gidana duk abinda kikace za'ayi miki in sha Allah. Kiyi sallah sai muzo mu kai ki gida kuma" Na fita na barta tana