← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 85

Sashe 45

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

zata yi maka girki, har kana ikrarin kuma dukanta a tunaninka baiwa ko Jaka ce Hajara? Girki ba zata yi ba, asibiti kuma dole saina kaita ko aman wuta kake yi wallahi. Hajara wuce muje" Wata dariya yayi tare da yin kasaƙe yana kallona. Ina jan hannun Hajara, tana noƙewa tana son bina tana tsoron me kaje kazo kunji irin tsiyar da irin baƙin cikin da muke ƙunsa ko. Fisgeta nayi muka ratsa matan gidan muka wuce. "Wallahi na rantse miki da Allah kika kaita asibiti dake da'ita duk sai kun kwana a sell, ke har kotu saimun shiga saina ƙulla miki sharrin da baki zata ba, makirine ni na gaske wallahi. Ke kuma kinsan gamona dake." Da Hajara da Maman Junaidu duk sai sukai turus a bakin ƙofar fita. Juyowa nayi na dubeshi ina murmushi nace dashi. Wanda ya fasa abu ta kazanshi ni da kai. Baka san waye Hindu bane. Ke Hajara kin shirya da duk abinda zai biyo baya, da fatan ba zaki ba dani ba ko? " Kai ta ɗaga mun halamun i duk da jikinta har rawa yake yi. Fisgarta nayi muka fice na sakata a bayan mota Maman Junaidu ta shiga gaba muka je asibitin Malam Aminu Kano. Saida na tabbatar an basu gado na basu kuɗi a hannunsu, na yi musu sallama tare da ba Maman Junaidu lambar wayata Da ba dan an sanni a asibitin ba, bama zasu karɓemu ba sai da hukuma dukan da Figo yaima Hajara dukane na sa'a. Ina zuwa wajen aiki na fita ɗakko rahoto, amman sauƙinta a cikin garine taron siyasane da aka gayyacemu ɗakko rahotanni. Mun jima muna jira tare da ƴan jarida ƴan uwana daga mabambamtan gidajen yaɗa labarai. Saida taro ya ƙare kana muka yinƙura muka soma aikinmu. Wato aikin ɗakko rahoto aikine mai wuya da haɗari ga ɗiya mace sosai, yawancin masu ɗakkon rahotannin dai mazaje, kana waɗanda zasu bada bayani akasari mazane. Dan wannan taro har gwamna yayi magana damu duk da ba wannan bane farau ba. A gajiye tulus na dago gidan Rediyo a hanyar dawowane na samu zarafin kiran Maman Junaidu dan jin me ake ciki. Kafinnan, naje kotu, mun yi magana da alƙali akan kes ɗina da mijinyawa, bazan sako Saudatu a cikin lamarin ba, sai dai in ɗauki lauya daban gaskiya. Bayan nan, na je wajen Baban Jamila na nuna mishi hoton Mijin Salamatu. Kuka kawai ya fashe dashi, yanata furta. "Allah ya'isa Allah ya isa, bazan yafe ba. Duk da nasan nina cuci kaina. Amman yarinya ya akayi kika gano hotonshi? " Baba wannan da kake ganinta Babanmu ɗaya, itace nan da ƴan kwanaki zata aureshi. Mu a Katsina ya nuna mana yake. Kuma da dukkan halamu a wannan karon yayi amfani da iyayenshi na gaske. Sabida sunzo an gansu, akwai kama. Sannan anyi bincike ɗan manyan mutanene, ya fito a familin yawa, kuɗi, da muƙami. In sha Allah zamu ƙwato hakkin Jamila da izinin Allah Baba. Duk sauran bayani zaka ji." Da haka mukai sallama kafin na kira Maman Junaidu. Wannan ƙasar tamu wallahi akwai gyara, Wai a asibiti an sallamesu an mata duk abinda ya dace basu wuce ƙarfe uku a asibiti ba suka koma gida. Figo ya ɗakko ma Hajara ƴan sanda harma sun tafi da'ita, nima wai suna hanyar zuwa wajena. Bata da lafiya, da ciwuka a jikinta, a haka aka wuce da'ita. Illahirin mamaki da ƙyar ya barni na shiga ciki cikin ɓacin rai na miƙa aikina na ranar, ko zama bam ba sai ga kira wai ana nemana ƴan sanda suna waje. Luba hankalinta duk ya tashi ta shiga ruɗu tare da tambayata dalilin neman. Dariya nayi ina jinjina rashin daraja irinta Figo. Miƙewa nayi nace da'ita. Kar ki damu akan kare hakkin wata baiwar Allah ne mai miji ɗan hau, Luba bari inje ayi duk wacce za'ayi." Ina gama faɗin haka na suri jakata na fita suna harabar gidan rediyon har ma'aikata sun soma leƙe, harma da masu kai kawo kunsan dama a wajen aiki baka rasa maƙiya duk yadda kuka kai ga haɗin kai. To ina da tulin maƙiya sosai. Ba fa kuma dan komai ba, sai dan jajircewata a fannin aikina ne kawai lefina. Sai cancantata data kaini landan kuma. "Mun kamaki da lefin sa matar Figo yi mishi bore, sannan kin fitar da'ita daga gidan dan ki koya mata bariki a bisa wannan dalilan zamu kamaki. Kofur Aisha ki kamata muje" A'a basai ta sha wuya ba. Bazan gudu ba muje babu damuwa" Muna kan tafiya zuwa wajen motarsu sai ga Luba ta ƙaraso da sauri. Kin motata ta zare da jakata a hannuna wayata kaɗai ta barmun. "Nazifi zai tuƙomu mu biyoku a baya Hindu" Dariya nayi mata. Lallai Luba kiyi tafiyarki gida, wannan ai ba wani abu bane, ni da ba da laifin kisa aka kamani ba. Waɗanda sukai kisanma a wannan ƙasar tamu wanne hukunci mai gamsarwa akeyi musu daya wuce aje a adanasu, gwammati ta dinga ɗaukar nauyin ci da shansu, da lafiyarsu." Kofur Aisha ta daka mun tsawa tace. "Ma firen shiga muje kina ɓata mana lokaci" Motarsu na shiga gaban motar ta zauna a gefe na sai direba, ragowar suna baya aka wuce dani. Su Luba na biye damu har zuwa ƙofar gidansu Hajara. Hmmm ashe Maman Junaidu muka zo ɗauka. Haka aka tuso ƙeyarta tana kuka da ihu, sanadin da yasa unguwar ta cika ta batse kenan. Sai mayafina nasa na rufe fuskata sabida darajar ƴaƴana. A bayan mota aka watsata muka wuce ofishin ƴan sanda na wajen. Aka sakamu a bayan kanta Hajara na zaune a benci bacci take yi a zaunen kasancewar jikinta babu ƙarfi. Kunji wata ƙaddarar kuma, wannan labarin in ya shiga gidanmu ai na zama nama, ga su Nanno suna garin suma labari zai karaɗe jama'are da kunnauwansu uwatale, in suka ji. Sai dai lallai babu mai jin wannan lamarin. Ni abubuwane ma cunkushe a kaina, musamman kes ɗin Mijin Salamatu yafi bugani. Yanzu a wanne matsayin ƴan gidanmu zasu ɗauki lamarin sai Allah, sai kuma su.
Chapter 45 · 0% Book details