Sashe 65
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI
LAMBA TA GOMA SHA TAKWAS (18)
ZUCHIYAR DA BATA NUFIN KO WACCE ZUCHIYA DA SHARRI.....
Kuna neman ƙamshin da zai riƙe zuciyar maigida kuma ya sa gida kullum ya kasance cikin sanyaya da soyayya? Ga samfurina ni mrs Bukhari na musamman, da kowace mace mai aji ya kamata ta mallaka don burge miji.Ƙamshin Ɗaki da Jiki: Feshi kaɗan a jiki bayan wanka ko a cikin tufafin barci yana ba da ƙamshi mai taushi da ratsa zuciya.Dorewa na Tsawon Lokaci,
Yana daɗewa a jiki yana fitar da daddaɗan tattausan ƙamshi mai sanyaya rai, wanda zai sa maigidanki kullum yaji yana son zama kusa da ke.
Aji da Kwalliya,Kwalba ce ta alfarma (50ml) mai kyawun gaske wacce za ta ƙawata wurin kwalliyarki.
(Farashinshi 25k ne.)
In kika fesama tufafi har sai in an wanke zai fita, in kuma fesawa kika yi a kayan, baki wanke ba kika mayar cikin sib, da kin buɗe ƙamshi zai daki hancinki, kuma zai harbi kayan sib ɗin.
Wannan garanti ne in sha Allah.
"To tunda kun bani dama bari in soma labari mai taɓa zuchiya. A zahiri duk macen da kika ga ta taka wani bigire ba'asan irin gargadar data fuskatanta a hanyarta ba.
Shi yasa nake mamakin masu faÉ—in Allah ya samu a danginki. A haka gani sak cikin walwala amman a baÉ—ini ba lafiyayya bace ni kwata_kwata, godiyar Allah ce da salatin ma'aiki Arrasul s.a.w"
Muka haÉ—e bakunanmu wajen faÉ—in sallalahu alaihiwasallam. Kana ta tsunduma cikin tafiyar labarinta mai ban tsoro da firgitarwa ya salam.
Duk muka yi shiru kowa Saudat yake kallo kawai.
LABARIN SAUDAT:.
"Mun yi Aure da Nazifi a lokacin ina aji matakin dubu biyu ( 200 level) ina karanta fannin shari'a wato ( low) a harshen nasara.
Ranar da muka haɗu ruwan sama akeyi kamar da bakin ƙwarya, ni kuma inason zan koma gida Mama nayi mun kiran gaggawa daga makaranta, haka na fito a cikin ruwan zuwa titi ruwa na gudu a titi ina ɗiga haƙorana sai kakkarwa suke yi. Nazifi shi kuma yana cikin napep shi kaɗai a baya shi yaba mai adaidaita sahun da yazo wucewa izinin tsaiwa a ɗaukeni, duk da hanyarmu ta saɓa. Amman sai yace a soma kaini tukunna. Ashe shi a lokacin shigowarshi Najeriya kenan ya kammala karatunshi na digiri na biyu a tsantsayar Amurka, babban likitan fata ne kuma ƙwararre, jajirtacce, jajircewarshi cema tasa suka ji suna son yin aiki dashi a can Amurkan.
Nan aka saukeni a ƙofar gida nayi godiya na shiga gida a guje, kuɗin ɗan sahun ma ca yayi in barshi harda sake mun murmushi mai kyau.
Ni wannan kulawar da wannan murmushin a yayin rabuwa, shine abinda ya soma jan hankalina gareshi. Kunsan mace raguwar zuchiya gareta, sannan da yawanmu abu ɗaya zuwa biyu kaɗai ya ishemu wajen zaɓin mijin aure, sabida a lokacin bamu san meye aure ba balle musan yadda lamura zasui ta jujjuyawa bayan mun shiga auren, sai daga baya ake gane zaɓen tumun dare akayi, wasu kuma nasu zaɓin ya zame musu na alkhairi. Suma mazan sun iya ƙirƙirar halin da ba nasu bane su yafa, a ƙoƙarin ganin sun mallaki mace, ita kuma in wannan abinda ya ƙirƙira shine sababin zaɓarshi da tayi, sai anyi aure sai taga akasin hakan, daga nan ake soma samun matsala. Ina da ƙawar da muka haɗu da'ita a Amurka gidanmu ɗaya bafulatanace ita sabida barkwancin mijinta kaɗai yasa ta aureshi, kada ku daɗa kada ku raga.
Amman ita duk yadda mace takai mai sa'a wallahi Allah ya bata. Akace wai ko wacce mace da irin tata matsalar a gidan Aurenta ko? Harma ake cewa duk wacce tace bata da matsala ma ƙarya take yi.
Akan wannan bafulatanar na gane wannan maganar ba haka take ba.
Duk yadda ake neman miji kamili, adali, salihi, mijin baiwar Allahnnan ya kai, kuma ya cika gwarzon namijin da yasan kima da darajar matarshi. In dai a gidan aurene bata da matsala ko wacce irice, salamun_salamun suke zaune, sun shinfiÉ—a rayuwa tartibiya, sun gina yara masu tarbiyya, nutsuwarsu ma dabanne, kai ilimin addini, da kuma aiki dashi a aikace yayi a rayuwa."
Mariya Habibu tace.
"Ai baki san baɗinin rayuwarta ba. Kinsan fa akwai fek lib Saudatu, anya a wannan marrar, da wannan ƙarni za'a samu matar da take zaune bata da matsalar komai a gidan miji kuwa, namijin wannan zamanin kuma? Kai ina"
Kallon Mariya Habibu nayi, tare da yin murmushi nace da'ita.
Haba Mariya akwaisu fa bila adadin billah. Kinsan matsalarmu itace, mun fiye raki mu mata. Sannan in kina da matsala a naki gidan auren, sai ki haÉ—a mata ki musu kuÉ—in goro kice duk wuya ake sha. Mazan duk basu da halacci, azzalumaine, basu san darajar mata ba.
Wannan ƙarara zaluncine, kuma kuskurene mafi girman gaske. Kinga na Allah ba zasu taɓa ƙarewa ba. Azzaluman Maza akwaisu, Salihai ma akwaisu basu da iyaka. Ni sai ince miki ma Salihan maza natijajju sunfu na banzan yawa.
Matane suke sake tura lamarin fa. Matsalarmu shine in ke mijinki mazinacine misali, ko ɓarawo, ko madokine. Sai kawai kice maza ai ƴan iskane, duka maza fa. Gaki da mahaifi, mahaifinki na da mahaifi, mahaifiyarki na da mahaifi, kina da Baffanni, kina da yayu, kina da ƙanne, ke kina da Ƴaƴa mazan ma.
To duk kin haÉ—a dasu, da malamanmu, da manya_manyan bayin Allah. Wannan kalmar hatsari gareta.
Kuma mata suna so in mijinki azzalumi kika samu wai dole kiyi shiru hanyar shiga aljannarki kenan. Sannan in in kika koka, sai kawai mace ta dubeki tace.
Nawa yafi naki, an mun abinda yafi naki, ke wacece da ba zaki haƙura ba. Ko anma wance' an ma wance kema kiyi haƙuri, ya zama ruwan dare.
Sun mance Allah maÉ—aukakin sarki shi ya yimu mabambanta.
Wasu masu sanyi, wasu masu zafi, wasu masu sauƙi, wasu akasin hakan.
To ke kina da sauƙi, gaki da saurin sakkowa a yayin fishi. Ba yin kanki bane, bake kika zaɓa ba. Ubangijin daya halicceki shi ya yoki a haka.
Ba kuma ki isa kice kowa sai ya zama kamarki ba, kuskurene.
Ga wata mafaÉ—aciya, mai saurin hasalace, haka Allah ya yota. Sai wata tace wai dole sai ta zama mai sanyi, da taushi. Alhalin ba ita tayi ta ba, itama ba ita tayi kanta ba, haka Allahnnan yaso ganinsu.
Babu damar ɗaya ya tanƙwara ɗaya ta ƙarfi, sai da nasiha, da nuni. Kama da wane akace bata wane. In Allah yaso sai ya juya lamarinshi yadda yaso.
To dan Saudatu tace ƙawarta na cikin Nutsuwa, baya nufin fek lib, sai fa mun cire waɗannan dattin a cikin kayukanmu. Abinda kika samu, ba kowa yake dashi ba. Naki naki ne, na wani nashi ne. Allah yasa mu gane mu karɓeshi a haka, ko da zamu karɓa da haƙurine"
Ajjiyar zuchiya duk suka sauke.
Nana Kabiru tace.
"Madallah dake Hindu Duwaf. Wannan bayanin naki cike yake fal da ilimi sosai.
Ko ni Nana ganinan. In aka zauna dani akace namiji ba É—an goyo bane, to Allah zai iya saka ma maza.
Wallahi Mijina duk inda ake neman miji ya kai. Shekararmu ashirin da shidda jiya jiyannan cib da Aure.
Cin amana, zalunci, tauye hakki. Ban taɓa kamani da ɗayan wannan ba. Rayuwace muke yinta mai tsabta. Rayuwar sanin darajar kai. Ni dashi mun zama abu guda, wallahi ya washeni na washeshi. Bari in muku ta mahaukaci. Ban taɓa kuka ta sanadinshi ba wallahi. Muna saɓani a farko, farkon aurenmu a lokacin muna kan karatun fahimtar kawunanmu. Da kuma lokacin da yara suke ƙanana haka, ni mai duka ce, shi kuma sanyi gareshi.
Bari dai kar mu haÉ—e labarin, Saudatu tace gaba.