Sashe 33
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Ya ilahi rijalu suna sharafi" Dariya Sumayya tayi tare da share hawayenta da dabara bata barsu sun kai da sakkowa ba, hakan ya burgeni, kunsan ance bana ji, kamar yadda nace Ummin Mama bata ji😉. Saida ta nutsa hannunta a cikin shinkafa ta gutsiri ƙaton nama ta saka a bakinta ta tauna ta cinye, mu kuma illahirin nutsuwa da hankulanmu suna kanta. "A lokacin Lubabatu da za'a tsaga jikina ba za'a tadda jini ba. Maganarnan ta dakeni ta mari rayuwata. Wallahi nafi awa uku a tsaye a gaban mudubi tsirara ina duba zatin da Allah yaimun, ina hasaso tsabtata, iya girkina, kula da muhalli, kula da gida da gyaran gida, tallatin dukiyar miji, bada gudunmawa ta kuɗi a lokacin da ake buƙatar hakan, na hakaito fuskar Auwalu a lokacin mu'amalarmu bazan iya tuno komai ba. Ni ba ƴar ƙauye ba bare ace ban iya sarrafa miji ba, ko ban iya sarrafa jikina yayin mu'alamar bane, ni ba ƙazama ba bare ince da datti nabar jikina da muhallina. Ni ba wai bana shan magungunan matan bane, duk da ban yadda dasu ba a matsayina na likita akwai abubuwa na musamman da jiki yake buƙata domin ƙarfafa sha'awa da tada komaɗa, ina haɗawa dasu zogala, alayyawo, rama, kayan ganye da irinsu kanunfari, citta da sauransu da sauransu. Kuma ni ba kasalalliya bace a ko da yaushe Auwalu in yazo da buƙatarshi ina biya mishi ko da wanne irin gajiya nayi sabida gudun ƙorafi da kiyaye abinda zai iya harzuƙashi, akan aikina muzo afi wata ɗaya ana rikici, tunda dai na fahimci shi irin mazannanne masu tattalin rikici da janjanin kar ya ƙare. Akan kalma ɗaya tak sai afi sati biyu yana ƙorafi da ƙoƙarin ƙera maganar ta dawo garma. Kuma ni likitace, nasan lafiyata ƙalau, ni'ima dai in tana ma mace yawa to ni Sumayya tawa tayi yawa. Ina tara buƙatuwa sosai kafin Auwalu ya waiwayeni, hakan yasa da zaran munje sama jannati, sai in ta yoyo kawai. A baya ina nemanshi, sai ya gwadamun ba haka yake ba, saina ɗauki ido na zuba mishi. Hmmm a cikin kwana ukunnan tunanukan da nayi sai wanda na mance, ga kuma aiki inna fita shima babu sauƙi. Ga masu son ganin faɗuwarka musamman a wajen aiki, dama haularka, abinka da ƴan dangi in magana ta shigo haularmu to a rufe ƙofa kawai. Bamu sake magana ta fatar baki da Auwalu ba satin duk aikin kwana nayi, ranar asabar da safe muka haɗu a wajen cin abinci da yara kamar kullum. Doya da miyar kwai nayi mana, sai ruwan bunu da lemun tsami sabida danne maiƙon abun suya da muka ci, in akasa madara a shayi ga kayan soye soye tayar mun da zuchiya yake yi, maiƙon ai sai yayi yawa gara shayi mai lemun tsamin yafi shiga. Yara na gamawa suka bamu waje. Sai kallona yayi mukaima juna murmushi. "To ya ake ciki da fatan kin rubuta musu takaddar barin aikin kafin ki baro wajen ko, ko sai monday zaki rubuta musu? " Dariya nayi nace dashi. In har na zaɓi abinda kake tunanin ba? To ban zaɓi barin aikina ba. Auwalu in mata uku zaka auro bana jin zai shafeni bare aikina. Ai gara ka auro wacce zaku ji daɗin rayuwar auren da'ita, tunda anan baka samu ba, bazan tauyeka ba, ta yiwu halittatace hakan, shi yasa baka gamsuwa. Shari'a ta ba da wannan damar ni Sumayya bana jayayya. Amman kafinnan, inaga akwai buƙatar ka soma shan magungunan ƙarfin maza kafin tazo, inaga basir ko cutar sanyi sun cinyeka faɗamane banyi ba. Kar ka kawo yarinyar mutane a haka, tunda kana kallon kanka a matsayin gogarma" Ina gama faɗin haka na suri kwanon abincina da kofin shayina na ƙule ɗakin yarana. Maganar bata ƙara tashi ba, naci gaba da aikina shi kuma yaci gaba da shirin aurenshi da gyare gyaren inda zai ajjiye ƴar mutane, wallahi ko a jikina kamar an tsikari kakkausa. Bai mun kayan faɗar kishiyaba ban tambaya ba, ya gyara ɓarayin amarya ya tsarashi fes, nima na zuba kuɗi na gyara nawa ɓarayin fes. Kuma naci alwashin, na bar ma Amarya Auwalu Abadan. Bai isa duk ranar da yazo in saurareshi ba sam. Ranar wata Juma'a aka ɗaura auren, asabar Amarya ta tare naga gulma da makirci irinna dangin miji ashe haka suke babu kyau babu daɗi. Shikenan ranar lahadi ango ya tare a ɗakin Amarya, da ta kwana ɗaya ban santa ba babu wanda ya kawota wajena. Ashe shigowar Amarya cikin gidannan a lokacin ne zan gane ainihin mijin da nake aure, da duk bansan waye Auwalu ba. Hmmm da safe ranar monday na buɗe ɗakina zan fito cikin shirina na zuwa wajen aiki. Sai nake jiyo tashin maganar Auwalu a falo da Amarya suna magana a hankali yana bata labarina. Dan tabbas jin sunana daya amtaba ya jani da son laɓewa inji me yake faɗa mata. Namiji namiji tuwon ƙaya miyar allura. Ya ilahi. Mrs Bukhari