Sashe 6
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Laa ai baki ma sani ba, da sai shi Sunusin ya shigo ƙebe_ƙebe yazo yana ɗan wasa da yaranshi, tunda ai bazan hana ba. Sai kawai ta biyoshi sai su shantake a falona, wani sa'in harda kunna Tv Sunusi kenan mai gida ba. Dana gane fanka suke zuwa sha, wallahi ana magriba nake datse ɓarayina bugun duniya bazan buɗeba shine tayi zuchiya rannan tai ta maganganunta a tsakar gida. Shi kuma yana ta aikin rarrashinta, ba kiga yadda take ɓarje shagwaɓa ba, Sunusi gotai_gotai har wasan gudu suke yi fa, abun kunya wallahi, lokacin bata da ciki" Dariya muka kuma sakawa ni da Luba harda tafawa tab. Maza kenan, da yawansu gani suke yi isace, ko fin ƙarfi suke mana, shi yasa muka sanya hannu a ragamar kulawa da gidan. Basu san kyautatawace, da tausayi irin namu na mata ba. Amman gani suke isarsu ce ke sa ayi dole, sai randa su kai gar_gar aka janye musu tallafi, su dawo abun tausayi na gan_gan. Yanzu dai baki ga yadda na baro su Sunusi ba, zafi na neman rayuwarsu ba" Kai kawai ta girgiza tace. "Hmmm" Shiru nayi ina dubanta. Sabira ce ta shigo mun da abinci da wani soɓon wanda yake hannuna ma ban sha ba. Sai da na zuba lomar abinci a bakina nace da'ita. To wai bakwa rabon kwanane naji a labarinki kullum Sunusi yana can ko? Na dai san kin basu wata shida suje su gama ƙananan iskancinsu. To kinsan hirarmu a taɓa nan a taɓa canne, inajin bamu sake taɓa hirarta ba." Hannu luba tasa ta ɗauki lokacin dana ajjiye ta ɗebo abinci ta saka a bakinta tana taunawa tana cewa hmm, saida ta haɗiye tace. "Hindu kinga tunda Sunusi ya auro wannan aurakar bai raba kwana yayi na wata guda a tsakaninmu ba. Ta soma laulayin cikinta daya zube. Sai yake cemun zai koma wajenta ya kula da'ita sabida yarinyace ita tana laulayi sosai. To kinsan yanayin aikinmu yadda yake da wuya da cin lokaci. Wallahi Hindu na mayar da kaina sosai akan aikina na watsar dashi kwandon shara ƙaƙas. Bayan tafiyarki na jajje ɗakko rahoto na wakilceki aikin rahoto aikine mai wuya da ƙalubale ga ɗiya mace ga haɗari. Saina zama bani da lokaci sam, na kuma sake ƙirƙiranma kaina rashin lokacin sabida sam Sunusi bazai kai ni ƙasa ba. Gaga_gaga yaita jinyarta tsakaninmu dashi da asuba yana shigowa ƙofa a hannu mu gaisa kafin in tafi aiki. Ya bani kuɗin cefane ya tafi har dai ciki ya zube tayi jinya kamar zata mutu, kullum in zani aiki ina leƙawa in mata sannu, lokacin ƙanwar Sunusi tazo tana jinyarta. Kinsan Allah saida yayi wata shidda kafin shi a_ _kan _ karan _ kankin _ kanshi rannan da daddare ina kwance sai kawai ya shigo harda siyo kaza yadda kika san an kawo ango" Dariya na saka nice harda ƙwarewa da shinkafa saida na kora da soɓo. Naita dariyar mugunta Luba na taya ni. "Ƴar iska dariya ma abun ya baki dan nace kamar an kawo ango. Na dai taya shi muka ci kaza na kora da ruwa yayi kwanciyarshi yadda kika ga ruwa, har da makara. To kinga shekarar amarya ɗaya fa kenan. To ana haka da wata ɗaya cib muna rabon kwana babu abinda ya shiga tsakaninmu duk da ya nema sau babu adadi ina nuna mishi bazai yiwu ba. Mu kaita rikici. Ke Sunusi harda banƙareni yayi wai zai ƙulleni a katagon gado. Zo kiga damben tsiyan daya kaure a tsakaninmu" Katseta nayi ina cewa. Ai ba wajen bane, taya ma jikinki zai zama arha bayan duk wannan ƙasƙancin. Luba ni gani nake yi duk macen data sha wuyar zama da namiji da daɗi babu daɗi anfi wulaƙantata. Kesa_kesan da suke zuwa wajena wallahi Luba a cikin ɗari zaki ji iyayen gida da suka zame ma miji garkuwa a lokacin talauci su suke rubuto saƙo suna neman shawara cikin halin uƙuba. Da wuya kiji Amare a cikin uku. Bawai ba'a samun iyayen gida mugaye bane ko marasa son a zauna lafiya ba. Ana samu suma sosai, masu amfani da daɗewarsu tare da miji, da sanin abinda yake so, da akasin haka su danne Amare. Amman fa da wuya kiji haka amaren sunfi rawar kai da nuna su sunfi kowa son miji da kwantar mishi da hankali. Ko da yake da yawan mazan su ke zuwa musu da labaran ƙanzon kurege akan gazawar ta gidan. Kuma fa ƙaryace ruwa_ruwanta. Su kuma yaran a tunaninsu an aurosune su cike giɓi. Luba nifa ɗiyar da nono nane kawai bata sha ba, wai itace kishiyata abinda akeyi mun shi za'ayi mata. Yadda na haihu haka zata haihu, yarana da nata su zama wa da ƙani. Ai ya zama dole mijinyawa ya sakeni yaje ya ƙarata da abun kunyarshi, ko da yake maza babu ruwa a idanunsu sam hmmm" Wani mikine mai ciwo ya famu a zuchiyata. Ina yawan jin zafi sosai a zuchiyata musamman inna tuno mijinyawa da abinda suka aikata mun, ina jimawa a cikin yanayin zafin zuchiya da nauyinshi. "Hinduwa ko ni aka mun irin abinda akayi miki narantse da Allah in duk duniya zasu taru a kaina wallahi bazan taɓa yin auren ba na gama ya ƙare. Ina kai ki labari" Ina sha Luba duniya" "Sai kwatsam ta samu wannan ƙaddararren cikin nata. Shima nan nazo na sameshi na dawo aiki, na shawo gajiya, ranar rahoto naje na ɗakko a wudil. Yana haɗa kan ƙananun kayanshi a jaka. A nanne yake shaida mun zai koma wajenta da zama har zuwa lokacin da Allah zai sauketa lafiya. Labari fa yake bani, ba wai yana faɗamun in yadda ko kar in yadda bane. Shine aketa fama tutur har yanzu, wani sa'inma shi ke mata girki in jikin ya matsa mata, dan tabbas laulayi sosai take yi, ta kwanta a asibiti ya kai sau biyar inaga, tattalin arzikinshi yana ta yin ƙasa. To ai ita dole yayi mata, dan wataran ma ciwon bai kai wani ciwo ba zata kira ƴan uwanta a wuce da'ita asibiti. A hakanma yaso yace in taimaka in dinga zuba mata abinci. Wallahi baiga fuska bane shi yasa. Ya ɗan yi ƴan kame_kamenshi ya ɗakko taliya da kayan miya, wai in taimaka in girka mishi zai kai musu asibiti. A lokacin ma farfesun naman zabbi na sauke, ai ina jin yace haka na buɗe farfesun ƙamshin su citta ya daki hancinshi, na mayar da murfin na rufe. Na faɗa mishi ɓaro _ ɓaro cewar bazan iyaba, na gaji ban jima da dawowa daga aiki ba ya siya musu abinci a bakin titi ya kai musu, wannan hakkina bane. Wallahi yafi minti goma sha biyar a tsakiyar kaina yana surutai kinsan har zungure mun kai ya dinga yi. Wallahi kusan sau biyar fa. Ana shidanne dana juyo na kalleshi shine ya fita ba shiri. A yadda na ƙunannnan ai ba wajen bane Hindu. Kinji abinda yake faruwa fa, ina gefe na zuba idanu lokaci kawai nake jira, sabida yara gaskiya. Ina kan adashen da zan biya miliyan ɗaya da rabin da zan zuba zubin farko a bani kin gida fa. Saura wata uku ɗaukana ya zagayo. Bazanma shiga gidan ba har sai na mayar dashi haɗaɗɗe na zuba komai. Abinda yayi mun ya mun ciwo bazan mance ba. Amman jiya ya kuka ƙarke da mijinyawa tun safe naso in kira inji gulma kinsan Allah. Nace irin kallon da yake yi miki kamar zai haɗiyeki anya bai yi miki fyaɗe ba kuwa? " Harara na zuba mata na riga na cika bakina da shinkafa ina kan taunawa, ita kuma sai dariya take babbakawa tare da buɗe tsarabar da nayi mata tana dubawa. Wato ma yai mun fyaɗe? Ai wallahi ba wajen bane, wata fuskar tafi gaban mari. Yadda nake jin zuchiyata a soye bazan fyaɗu ba Allah Luba. Ai shima yasan sauran ya kusanto hannunshi jikina yaga yadda zanyi wasan kura dashi. Ai bazai ma soma ba kinga, yadda yake jin wata iriyar kunyata ta munafurci? To munafurci mana tunda ya iyayin ruf da ciki akan yarinyar da haihuwartane kawai bai yi ba, to kunyar ta mecece inba ta munafurciba. Anan falo ya kwana wallahi banma sani ba yazo dai ya buga mun ƙofa sanda suka dawo masallaci da Azgar" Nan na kwashe duk yadda muka yi na faɗa mata. "Da kin sani kin bashi dama ya fesar da duk abinda yake zuchiyarshi ba dai shikenan ba in kika ji ba Hindu?" Luba kefa kinsan ni inna gama na gama bana dawowa baya, ba wajen bane. Bazan ɓoye miki ba ni ko sunanshi naji an ambata sai zuchiyata tayi duhu wallahi. Bashi da abinda zai ce mun sam. Kuma bazai sake kwana mun a gidana ba ato Luba in tsaya ma in saurari ƙananun ƙarairayinshi ai wallahi bani da aji ma kenan. Sai kace wata jaka?" "Hindu a sassauta ma Mijinyawa haba ƙawata" Harara na sakar mata, ta tuntsure da dariya dama nasan tsokanace kawai. To ke ki ba Sunusi dama ta biyu mana Luba. Ki tausaya mishi, naga duk ya zama wani iri" "Ina ba wajen bane" Dariya muka sake sakawa muka tafa tabb. To zamu mutu ne? Mun daɗe muna hira har kusan goman dare. "Hindu ki tashi ku tafi gida. Ji yadda kika shantake sai kace wata bazawara. Ba wacce miji ke jiran dawowarta ba" Dariya muka sa dukkanmu. To menene marabar dambe da faɗa Luba?" Ba dan rai yaso ba mukai ma Luba sallama na kama hanyar gida Sabira sai bacci take yi a mota. Ina ƙarasowa ƙofar gidan naga motar mijinyawa a gefen gidana. Ƙwafa nayi nace. Zan kuwa kuikuyama mijinyawa. Bazan ɗauki wannan zaryar ba, haka siddan zai sa yarinya ƙarama ta rainani tayi tunanin kwana yake raba mana abinda yake yi mata shi yazo yi mun nima. Yazo ya kwana jiya, yauma ya dawo me zata yi tunani? Yana mana rabon kwana kenan fa hmmmmm subhanallahi. A zuchiyata nake wannan maganar inajin zafi a ƙirjina. To ko dai sabida Mijinyawane Azgar ya ƙi biyoni? Hmm in kuwa hakane yaronnan zai ga ɓacin raina. Ƙararrawa na matsa sau biyu a jere ina jiran Azgar ya buɗe mun. Sai ga mijinyawa yazo ya wangale mun get ɗin mamaki ya kamani na irin ƙarfin halin maza. Yana saye da wandon