← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 85

Sashe 21

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 1 min read

dai akace miki Saudatu har kuka kike yi" Na cabke da cewa. Wani sa'in har da kai ƙara wajen malama Aisha take yi. Wataran kuma aci uwar dambe. Rayuwa gashi yanzu duk mun zama iyaye." A nan tsaye mun yi hira tayi ta minti ashirin, da ƙyar muka yakice muka shiga har zuwa ɗakin da Khadija take kwance. Muka tarar da baƙi sun zo duba jikin nata. Gaggaisawa muka yi tare da duba jikin Khadija yau dai idanta biyu tana kwance shiru duk tabi ta rame. Maman khadija muje daga waje muyi magana" "To Hajiya. Rabi'a dan Allah ki kula mun da Khadija" Kallon Rabi'a nayi na maya. Itama duk gata ga kamarta dai abun gwanin tausayi. Gefe muka samu Batista Saudatu Mustapha ta yi mata tambayoyin da zata yi mata duk ta amsa mata. Kana muka wuce wajen Diktan daya dubata zuwanmu, amman shi akace aikin dare zaiyi sai dai gobe da safe mu dawo in lallai dai muna da buƙatar ganin nashi. Mun bari akan gobe da safen zamu dawo domin Saudatu Mustapha tace lallai akwai tambayoyin da take son yi mishi a matsayinshi na likitan daya soma taɓa Khadija a halin da aka kawota. Mrs Bukhari Jama'a jikina yayi en ob diskoshon😆
Chapter 21 · 0% Book details