← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 85

Sashe 25

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

yasan irin halakar da iyaye suka sanya yaransu a ciki, a kan dalilin da ba addini bane yazo dashi ba. Da yawan iyayen mutuwar Auren basa sone sabida kar ace sun gaza wajen tarbiyya. Ko kar a ce wance bazawarace. Su kuma matan suna tsoron in sun fito wacce tarba iyayen zasu yi mata, sannan suna tsoron irin ɗan kiran da al'umma zasu dinga musu. Bazawara_bazawara dai Su gani suke yi wannan sunan ƙasƙancine sun mance fiyayyen halitta Arrasul saw matanshi in aka cire uwar mumunai Aisha ɗiyar sayyadina Abubakar al siddik duk zawarawane matanshi. Nana khadija Uwar Ƴaƴan ma'Iki Arrasul wacce harta mutu, yace da Aisha wallahi Allah bai musanya mun da wacce tafi Khadija ba, sabida girma da matsayinta, da irin yadda ta ma Musulunci hidima. Allah da kanshi ya aiko mala'ika da saƙon gaisuwarshi zuwa ga Nana Khadija. Duk da an tambayi ma'aiki Arrasul saw a duniya wa kafi so yace Aisha, akace a maza fa yace Abukakar mahaifinta kenan. Kunji mata masu asalin kafacity ko, muce Allahu Akbar dan Allah. Jama'a Musulunci fa addinine mai sauƙi da daɗi, mu ne dai muke ɗaukan duman magaji da nishi wallahi. Ina cikin wannan safa da marwan mijinyawa ya shigo harda neman waje ya wani zauna. "Hindu zauna muyi maganar da nace inaso muyi dake. Na fahimci baki da lokacin komai da kowa a yanzu aikinki kawai kika ba mahimmanci, sama da komai da kuma kowa." Wani kallo nayi mishi daman kuma a wuya nake da maza ji nake kamar in karkashesu kowacce mace dake ƙarƙashin zalunci ta samu ƴanci. Bani da lokacin magana kaina ya ɗauki zafi kaɗaici nake so ka barni" Sai kawai ya zabura cikin fishi da zare idanu. "Baki isaba Hindu nagaji da wannan ƙananan iskancin naki. Mai kika ɗaukeni ne lusari wanda baisan abinda yake yi ba kome? Kina matsayin matata amman bani da iko dake kullum kina tafe baki nan baki can taimakon mata, amman kin kasa taimakon mijinki ki yafe mishi laifin da yayi miki. Ya kamata mu kawo ƙarshen wannan rikicin kin kasa bani damar da zan nemi yafiyarki bare ki yafe mun" A'a ya'isheka Mijinyawa. Harma kana da bakin cewa kagaji da ƙananun iskancina. Ai baka ga komai ba indai kana riƙe da igiyar aurenane wallahi. In so kake komai ya ƙare ai sai ka sauwaƙemun. Fita kuma ina da ikon fita duk inda zani ba dole saina faɗa maka ba. Tunda a baya kasan yarjejeniyar dake a tsakaninmu, ka bani dama inje duk wani lungu da saƙo domin in yi aiki, ko in taimaki mata, ka barni in dinga zuwa gida a duk sanda buƙatar hakan ta taso mun, ka yarjemun in yi tafiya ko wanne gari in buƙatar hakan ta taso mun. Ka mance kaine inna tambayeka zani wani wajen kake fishi harma kake cemun na wuce haka a wajenka. Ka mance da izininka nake komai, ka bani duk wani lasisi. Shekara fin ashirin a haka muka shinfiɗa rayuwar Aurenmu, kai ka sani? Ohh naganoka da kai da magoya bayanka ai dama abinda kuka riƙa kenan a matsayin hujjar da zaku kafa abun kunya. Batun aiki da kake yi shi nasa a gaba, kamar ba kai ka nuna mun in ba aikina mahimmanci ba a baya. A da na tsaya na kula dakai, na kula da yarana uku, na basu tarbiya, ko ƴar aiki ban taɓa yi ba, aikina daban, kula daku da nake yi daban, ban taɓa tauye hakkin aikina, ko hakkinku ba. Duk wuyar aikina bakwa kuka da komai, inayi da lokacina, ƙarfina, dukiyata. Asalima kai gatane, da soyayya tayi maka yawa shi yasa ka zama ɗan iska irin yadda ka zama" " Aure ba abun wasa bane Hindu, nifa mijinkine. Akan laifi ɗaya jol sai garani kike, kin haukatamun nutsuwata, kina farautar rayuwata Hindu. Tabbas ni na baki damar zuwa duk inda aiki ya kama kije, da duk inda aikin agajinki ya kama kije, kiyi haƙuri dan Allah ruɗewa nayi ne. Sannan baki taɓa tauyeni a komai ba, in nace gata inda kika gaza na miki sharri. Amman taurinki yayi yawa" Murmushi nayi ina kallon yadda yake faɗa yana ɗaga murya. A daki mutum a hanashi kuka kenan. Ga mari ga tsinka jaka, wani iskancin sai maza. Wayata na wawuro na shiga manhajar WhatsApp, na ciro wannan hoton chart na nuna mishi. Wallahi babu shiri ya zauna daɓas a kujera, shine harda dafe zuchiyarshi, yana haki tamkar zai mutu. Kunsan meye abun farko da yayi? Fsshewa yayi da kuka, yana ta ambaton Allah kawai. Ni kuma ina tsaye babu inda baya rawa a jikina, haƙorana sai haɗuwa suke da juna. Zuchiyata kuwa tamkar zata faso ƙirjina ta fito, ta faɗi ƙasa ta fashe haka sak nake ji. "Hindu ki mun rai, ki tausayamun, ki taimakamun dan darajar Allah. Haƙiƙa naci amanar da kika damƙamun, na zalunci ƙaunar da kika nuna mun. Wallahi Allah baki gaza tako ta ina ba. Ina jin daɗin rayuwar aure dake, kina mun biyayya, kina gyara jikinki, kullum cikin ƙamshi, da gyaran jiki kike, ta ɓangaren kwanciya babu ta inda wallahi kika gaza. Tarbiyyar yara wallahi Hindu nasan kin basu tarbiyya, ni na ɓata komai. Alƙawarinki da kika ɗauka kin sauke. Wallahi nine na gaza. Hindu ki dubi raunina ki yafe mun, raunine dani. Kinga Talatu wallahi ita ta neme ni, ni kuma rauni gareni wallahi, Asama'u ma ita ta neme ni. Ki yafe mun, haƙiƙa na cutar dake, naci amanarki Allah bazai barni ba. Hindu ki yafe mun ki yafe mun baiwar Allah Ki yafe mun" Ya sake fashewa da kukan iskanci. Hmm da gaske kaine ko dai Mijinyawa Babbane ka dai duba" A zabure cikin ɗimuwa yace. "Nine Hindu, nine wallahi nine, a ina kika samu? " Halima surukarka uwar Asama'u itace ta turomun. Abinda baka sani ba, har gidan Talatu naje, ashe har kwana kayi a gidanta, kuka kwana kuna aikin ashsha. Da matar Aure Magawata hmmm" Wani ƙwallo na haɗiye. Kanshi na ƙasa kawai, jikinshi sai rawa yake yi. Hmmm mijinyawa kenan. Kana maganar sanin darajar aure ko darajar miji. Shin kai kasan darajar matarka da ka kai wata ɗakin baccinta ka turmusheta kana shan ƙirjinta kana sambatu a kunnen matarka. Kana kwanciya ka tura tsaraicinka zuwa duniya. Itama ta turo maka, ku biya ma kanku buƙata kuji daɗinku, ka ɗauki yarinya zango_baƙi_zangon_baƙi ku gama sheƙe ayarku. Yarinyar da haihuwarta ne kaɗai ni da kai bamu yi ba, yarinyar data rayu a tsakankanin cinyoyina da kafaɗarka. Yarinyar dana ɗaga darajarta fiye da darajar Ƴaƴana. Yarinyar dana fifita sonta fiye da son ƴaƴana. Ita ka Aura mijinyawa kuka ƙarashe abinda baku gama ba. Talatu ma ka game gane komai nata, kaje har sau biyu ka kwana a wajenta, kune kwararo_kwararo, harma ya yawonku Asama'u taci karo daku, saika yima Talatu ritaya, ka ɗauki Asama'u ka ɗaura daga inda wanda yake kaita zango baƙi ya tsaya. Ubangiji shine shaidata duk wata tarbiyya na ba Asama'u, daga Jami'a take ɗiban jiki ta tafi yawon bin mazanta, acan ta haɗu da ubanta, mijinta kuma. Wai rauni ne dakai ko, ashe watarana zaka hakkema Sabira tunda kana da rauni, duk wacce tayi ma tayi, shikenan ciniki ya faɗa ko. Na rantse maka da Allah saika sakeni, na gama da babinka tuni, ba zajen bane wallahi. Meya rage a mutumcinka a idanuna ka faɗamun, nace ka faɗamun ka faɗamun" Cukukeshi nayi na shiga ihu ina nanata kalmar. Ka cuceni ka shayar dani guba abadan bazan yafe maka ba, bazan iya zaman aure dakai ba wallahi. Ko zaka mutu sai mun rabu, ko kaine Autan maza sai ka sakeni" Dukan ƙirjinshi nake yi cikin rufewar idanu, da fitar hayyaci. Shi kowa yana durƙushe kamar dutse. Wani ihu naji daga can nesa nake jiyoshi ashe ni nake yi."
Chapter 25 · 0% Book details