Sashe 75
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
LAMBA TA ASHIRIN DA ÆŠAYA (21)
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/F5JwhdwbtCQ6qdo4LA4kyE
Adashen hijabin Æ´an gayu É—inkin Æ´an kaduna kike so Hajiyata?
Ga masoyiya, aminiyar da bata da tamka, Ummu inteesar kenan farar aniya laya.
Ki shiga group É—inta zaki samu yadukan hijabai Æ´an gaske na kaduna, wanda zaki ta da taro.
Kaduna sune Hijabi an bar musu kayansu.
Ummu inteesar hijabs and more, mai adashen gata.
Gaga gaga haka Mariya Habibu ta bamu nata labarin ya ƙare, zuchiyata fal da tunanuka.
Nana Kabiru kuwa sai dai san barka.
Lallai tana daga cikin matan da a duniyarta sai dai tace Alhamdulillahi. Allah ya azurtata da miji kamili, adali, mai mutumci, da dattijantaka. Mai bin koyarwar ma'aiki arrasul S A W, madallah dakai Ibrahim. Na jinjina maka, da kai da ire_iren maza natijajju kamarka dama waÉ—anda suka fika.
Saudat ce tace. Allah yasa mu dace.
Lallai Nana na jinjinama Ibrahim gaya. Kin samu sa'ar rayuwa. Domin farin ciki a gidan Aure shine duniyar ma'aurata."
Murmusawa nayi tare da kallonsu nace.
Ni labarin Mariya Habibu, da yadda ta dinga ƙona kanta danta haska al'umma. A wajen Hindu kuskurene babba.
Yanzu wacce riba dai za'ace ta tsinta a zaman auren da tayi, in banda guzirin ciwuka, kana wannan suna da bata so lallai a kirata dashi, kalmar Bazawara, sai da ta amsata.
To ni ina ganin mu daure mu dinga yin abu domin Allah, domin kanmu, domin gobenmu. Ba wai domin gudun maganganun al'umma ba.
Kinga mutum? Allah ke iya mishi badai mutum ba. Duk yadda kike son ki burge, ko ki fahimtar baki isa an fahimceki rabi ba, dama duka bai samuwa. In dubu sun gamsu dake, dubu biyu da É—ari biyar basu gamsu ba, ya zaki yi da su waÉ—annan É—in?
Ga aure zaki kuma yi, nayi tunanin nutsuwa zaki yi ki gyara kusakurenki, ki gina rayuwarki, ko dan tsallake maimaita halin da kika shiga a gidajen aurarrakin naki.
Ki duba Shanono yadda aure ya bata wuya. Yara nawa ta haifa kafinma ta koma karatu, kafin karatunma ai kinga kayan gwari take siyarwa a cikin gida tana kuma ciniki.
Yanzu barista ce mai zaman kanta, yaranta duk sun yi Aure sai matasa biyu a gabanta kawai, mijinta Jega ya tsaya mata, suna rayuwarsu mai kyau.
Ke me yasa ba zaki koya daga gareta ba, auren kika fi son ki kuma ne?
Ni ina ganin ki huta, banda gaggawa"
Ajjiyar zuchiya Mariya Habibu tayi.
"To Hindu a hakan ai na gyara. Kuma ina É—an sana'ar takalma da mayafai. Kuma babu laifi ina samu arziki gaskiya. Inaga zanci gaba da sana'ar. Kinsan Allah kona shiga makaranta, kaina ya riga yayi tsatsa, babu abinda zai iya shiga"
To amman ki tabbatar kin koma Islamiyya, ai wannan kanki zai É—auka. Dama ni bance lallai sai boko ba.
Sannan wannan koke, koken Saudat, Mariya Habibu a rageshi dan Allah"
Dariya suka yi dukkansu, ni kuma na jefesu da harara cikin sigar wasa.
Saida na sauke ajjiyar zuchiya, kana nace.
Allah ya dafa mana, ya kawo ma ko wacce mace farin ciki da nutsuwa a gidan aurenta. Amman akwai gyara da aiki jajawur a gabanmu, akan zamantakewar aurenmu.
Kuma aure a arewa duk kwanan duniya mutuwa yake yi, É—aura wasu akeyi.
Komai da ka akeyi ba tare da neman ilimin abun ba. Musamman Aure, yana da kyau maza, da mata, ace su dinga zama a aji ana koya musu yadda ake aure a addinance, ba a al'adance ba.
Kowa yasan hakkokin ɗan uwan rayuwarshi, Tunda ba kowa yake da ilimin da za'ace yasan tarihin ma'aiki arrasul s a w yadda yayi zamantakewa kamila, tsaftatatta, da iyalanshi ba. Da kuma koyan dabarun zama da mata, da musalai masu tarin yawa. Musulunci addinine na adalci wanda ba'a tauye komai ba, duk yadda muke tunanin canji da murɗewar zamani, da duk abinda ake ciki Qur'ani ya riga ya zo mana da komai, kuma komai yana faruwa daki_daki. Bafa da ka muke rayuwa ba, shi yasa ko wacce al'umma tana da manzo wato ɗan aike. Mu kuma aka aiko mana manzo, Annabi mafi girma da ƙololuwar daraja. Aka saurar mishi da littafi mafi girma da tsarki, shine annabi daya karɓo mana sallah. Allahu Akbar. Aure tafiyace mai tsayin da ake fata, burin mutuwa ce kaɗai ka iya rabawa.
Ai kuwa shine a haƙƙu da aje aji a koyi iliminshi, a wajen masana.
Wai wanne irin tunani a ƙwaƙwalenmu ne?
Ko da yake jahilci da rashin wayewar addini, da wayewar rayuwa, da gogewa kusan shine wasila.
Wallahi in bamu koma tafarkin koyarwa ma'aiki arrasul s a w ba yanzu muka soma shiga tasku.
Dangane da makaruntun koyon auren, naga yanzu gaskiya babu laifi a nan kano akwaisu, naga Malama Zara'u tana da makatantar koyon yadda za'aiyi zaman aure da aji, na maza daban, na mata daban, ga koyon girki.
Tana da gogewa sosai, kunsan itama tana daga cukin madubaina, shigarta ta lafaya irinta mrs Bukhari tana burgeni sosai.
Akwai wata makarantar a Gombe wacce Anty A'A NafaÉ—a tana daga cikin malaman makatantar.
Tananan a cikin Taskar Badi'at Ibrahim anan ma in an gama littafi suna gabatar da shirye_shirye na gyaran aure da hulhu tsakanin ma'aurata.
Ga Hajara Aliyu ( mamanmu Adala kamila) itama tana cikin malaman gyaran Auren. Sai mrs Bukhari itama tana ciki farar aniya laya kenan ( afwan amman ni ƴar koyo ce, yanzu ne nake ƙara faɗaɗa karatun zamantakewar, tare da risach mai zurfi akan zamantakewar aure, musamman na Arewa, a taya ni da adda'a domin Allah)
Akwai Anty Zee musa kolektshon, mai kayan Æ´an gayu, kama daga tufafi, kayan Kitchen, kayan jira_jirai komai akwaita. Itama malama ce cikin taskar Badiat. Muna da Maman Safwan, itama malamace, maman Muhseen, Ga Maman Inteesar, mai Hijaban matan manya in dai marsidi ne a bar miki kayanki, tana da gogewar rayuwa, gata da tsinkaye. Akwai Mum khairi itama malama ce nagartatta. Ga kuma Hajiya Nabila mrs Bash fara duma_duma, itama malama ce jajirtacciya, gogagga, mai hangen nesa sosai.
Madallah da dukkanninsu, madallah da aiyukansu na alkhairi, Taskar Mrs Bukhari taskar Alkhairi.
Gasu da Malama Maman muhibba, mace mai ilimin addini, da baiwar tsara zance.
Saudat tace.
"Wato Hindu ina girmama tunanin ki sosai, in dai aka zauna dake dole sai an ƙaru sosai.
Zanso ace ina aiki tare dake.
Dariya nayi sosai, ni a tsarina bani da sha'awar aikin haɗin guiwa, sai dai a taimakamun da abinda ya sauwaƙa, sai dai dole a tafiyar da nake son yi ina buƙatar mutane amintattu da zasu raka tafiyar gidauniyar matan da zan buɗe. Amman ace gundarin kuɗi, da sunan gidauniya, da komai na kuɗi, nafi so ni kaɗai na kasance akai, bawai ace namu bane, a'a nawa nake so ace mallakina.
To Saudatu tunda ke lauya ce, ki zama lauyana mana, da kuma lauyar Gidauniyar da zan buÉ—e. Luba da su Habiba duk sai su taya ni aiki ai, kinga ita Mariya fuskarta a matsayinta na jaruma zai taimaka mana abun yaje inda zato ma bai zata ba.
Amman mai kuka ce?
Sai dai inaso in juya akalar abun ta hanyar tallafama mata da jarin da zasu ɗan dinga jujjuyawa, shine babban jigon Gidauniyar, sai basu shawarwarin yanda zasu san darajar kansu, da yadda zasu juya kuɗin sana'ar da zan ɗan dinga basu. In akayi musu wannan da kansu zasu iya tsayama kansu. Zan je Katsina wajen Maman muhibba mu tattauna ta ƙaramun kalan nasu dabarun yadda suke tallafin mata da jari, da yadda aka ɗaurasu a hanyar juya kuɗin. Sai dai kash ita a tim ɗin Mijinyawa take, sai dai abinda zai kaini dabanne"
Take duk kowa ya amince da tayin da nayi mishi, mun tsaya akan zamu sake haɗuwa ta musamman, amman in sha Allah sai komai ya girma ya tsaya da ƙafafunshi tukunna. Tunda da kaɗan zan soma, ofishi zan kama da ba zai wuci ɗaya ba, da ma'aikata da basu wuce biyu zuwa uku ba. Komai kuma zai biyo baya a hankali in sha Allah.
Da wannan muka tsaya akan sai wani lokacin in muka sake haÉ—uwa zan basu nawa labarin, tunda dai lokacin bai bamu wannan damar ba.
Har wannan lokacin jama'ar gidan suna sunanan, sai dai raguwa da suka yi. Da dukkan alamu kishiyar Luba Æ´ar dangice sosai, duba da irin taron da akayi na suna. Sunusi kuwa yayi bajinta irinta kere sa'a. Sallar la'asar muka gabatar, kana muku sake cin jallof É—in shinkafa mai hanta.
Kafin mu fita Luba ta kaimu ɓarayin mai jego mu mata barka, mun shiga mun samu Sunusi a kan gado da yaran a hannunshi, yayi zaman daɓaro a tsakiyar gado, shi da maijego ankon shadda ce a jikinsu iri ɗaya sak, ga yayu da yannen maijego suna cin tuwon dare. Dan magriba a lokacin ta kusan kawo kai.
Luba tayi kyau fiye da maijegon ma gaskiya, kuma lesirinta ya danne kuÉ—in shaddarsu, gezna ce ta tsakiyan suka É—inka.
"Ahh Hajiya Hindu kun fito kenan? "
Idanu Luba ta ƙura mishi irin kallon Allah wadaran naka ya lalace ɗinnan.
Wallahi ka ganmu mun fito shine muka ce bari mu ma maijego barka kafin mu tafi" Na faÉ—a kadaran kadahan.
"Ayya ai kuwa nagode sosai. Maman Sadiq naga atampopi da kayan yara an gode. Yaya ku ma Maman Sadiq godiya"
Cewar Amaryar Luba kenan data ƙarashe tana kallon ƴan uwanta. Tana wani magana taɓa_taɓa, tare da karkace baki gefe.
"Ayya ai dama zamu shiga har ɓarayin mui mata godiya ma. Maman Sadiq muna godiya sosai wallahi kayan Tubarkallah. Allah ya kauda shaiɗan a tsakaninku."
Nan suka soma godiya wannan ta ja ta cika ta ba wannan.
Kuɗi na ƙirgo dubu goma sha biyar na ajjiye akan gadon.
Gashi a siya musu ƙunzugu"
Dukkanmu muka ajjiye mata kowa da nata. Nan suka sake kaurewa da godiya harda Sunusi fa yana cikin mata ƙaƙas haka muka fito.
A waje ma mun jima muna ta faman hira, da ƙyar dai muka yakice mukai ma juna sallama na shiga motata na nufi gida.
Ina jujjuya sitiyari amman ƙwaƙwalwata na jujjuya mini rayuwar su Saudat da Mariya, da irin dacen da Nana Kabiru tayi, a haka na isa gidan.
Mijinyawa:.