Sashe 41
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
wannan lissafinne ace lafiya muke zaune, babu wani tarnaƙi fa, da fatan kun gane. Kishiya bana tsoronta, bata gabana wallahi, amman azo ma mutum da irin wannan maganar kamar rainin hankaline ai. Ajjiyar zuchiya nayi naji a raina shikenan Nanno ta nemamun hanya mafi sauƙi da mijinyawa zai sakeni salin alin, in tace zata tsine mishi zai sakeni ai ko? . A fili kuma sai nace. Nanno inaga kin mance nice a ƙasanshi ba shi bane a ƙasana ba. Sannan kece a samanmu dukka aljannarshi na tattare da yi muku biyayya. In yaji yana da ra'ayin ƙara aure sabida tara yara, shi namijine zaiyi ko da ba'a sakashi dole ba. In kuma yana jin bashi da ra'ayi shima babu dalilin da za'a sakashi aure dole. Ni a nawa ɓangaren duk abinda yaga yafi mishi shi zaiyi, shi yasan kanshi zai iya riƙe mata biyu da ɗawainiyarsu, ko bazai iyaba. Wannan ba hurimina bane kiyi haƙuri cikin girmamawa. Gashi naga baki da lafiya ma" Yaya Jamila jira dama take yi sai kawai ta dira a kaina da zagi harda zagin iyaye a wannan karon lamarin daya sake dagula kan zancan kenan da yasa su Mijinyawa saka baki. Akul Yaya Jamila da wasa kada ki sake zagin iyayena ko aibatasu wannan ya zama na ƙarshe. Aurene ya kawoni Haularku so ba zai zama ƙiyayya ba" Mijinyawa Babba da mijinyawa nan suka saka baki. "A'a Yaya Jamila bai kamata azo har gida aci zarafinta ba, sannan ke kanki ba zaki so ta rama zagin da kika yi mata ba. Gaskiya banji daɗin wannan kaifafan maganganun naki ba" Mijinyawa Babba ya cabke da cewa. "Abi komai a sannu dan Allah su Azgar ba zasu rasa jin halin da ake ciki ba. Irin wannan ke wargaza kan haula kuga yaran can ɗakin na jin haushin wane da wance." "E lallai babu shakka. Wuyanku yakai yanka. Yau ni mijinyawa ke ma iyaka da iyalinshi ni ɗinnan dana saɓaku a baya, naci kashinku da fitsarinku, kar ka mance da dukkan abubuwan da nayi maka a rayuwa yayin ƙuruciyarka, amman yau har lalacewata takai kaimun iyaka. Ke kuma ki ƙarama bokanki kuɗi aikinshi kamar yankan wuƙa. Amman ki sani in ana tafiya tsirara tsabar fatara tabbas saina rabaki da mijinyawa, rabuwa irinta har abada mu zuba" "Babu mai rabani da matata sai mutuwa Yaya Jamila, ke ya kamata kisan iyakarki bafa ke kika haifeni ba. Baki da aiki sai zuga Nanno kije kiyi mulkin da kika saba a cikin gidanki mana kuma...." Tas Nanno ta matso ta ɗaukeshi da mari da bahagon hanunta, kuma ba bayan hannu. Bata da lafiya fa wallahi. Aini a lokacin jina nake yi a sama, tsigar jikina tashi kawai suke yi. Dafe kuncin yayi kanshi a ƙasa cikin rawar murya yace. "Allah ya huci zuchiyarki" "Ashe haka rashin ɗa'arka ta tumbatsa mijinyawa a gabana kake ma Yayarku wannan ɗiban albarkan, akan matarka wacce ita da juya bambamcinsu ƙalilanne? Babu shakka harni nan gaba zaka zaga. Hindu burinki ya cika. Ke taso muje mu kwana wajen uwatale kinji. Bazan kwana a cikin gidannan ba, bama zata sake ganina ba" Tace da Yaya Jamila da take ta huci tana cika tana babbatsewa. Ni kuwa Allah nake ambato ciwonane yake ƙoƙarin tashi dukkan tsigogin jikina a tashe suke, iska ke ratsani har ɓargona hakan ya haifarmun da rawar jiki hantata gigir_gigir take kaɗawa ina ji. "Ina wallahi muna nan Hindu bata isa ta koremu daga gidannan ba. Ta nan kuma bokanta ba zai ci nasaraba Nanno, munanan har sai kin gama ganin likita mun gama duk abinda muke yi zamu tafi. Ai dama ita ba son zamanmu take yi ba. In so samu ne bata ƙi ace ita da mijinyawa da ƴaƴansu bane a duniyar kaɗai ba." Ajjiyar zuchiya ta sauke. Ni kuma da zuchiya ke cewa in shaƙe Yaya Jamila in ɗagata in nuna ma Allah in saketa tamkar an yi mun wahayi, sai na miƙe jikina babu ta inda baya rawa. Tana cikin wannan hargagin sai taji na riƙeta mata hannu gam. Daga haka bansan komai ba kuma.