← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 85

Sashe 82

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

nayi kurum. Ai ba wani abu bane. Babban abinda zaku yi mun shine wannan tarbiyyar da muka baku ni da mahaifinku, kar kuyi fatali da'ita. Ku tsaya tsayin daka kuima mahaifinku biyayya da matar da zai auro muku ta shigo rayuwarku a matsayin matar uba. A duk inda kuke ku wakilceni, me nake nufi da wakilci shine ku nuna ma duniya an baku tarbiyya kuma kunsan girman nagaba daku. Kunga ibada? Ku riƙe sallah, ku kiyaye dokokin Ubangiji, ku dinga sanya Allah gaba gareku akan komai na rayuwarku. Ku riƙe Azkhar safiya da maraice, ku riƙe sallar dare, walha, da nafilfilin da muka saba gabatarwa kafin azahar, bayan azahar daf la'asar, bayan magriba, data bayan isha. Kana in kukai sallar dare ku cika da wutiri. Duk rintsi ku dinga karatun Qur'ani kamar yadda kuka saba kafin kwanciyar bacci, da kuma kafin sallar asuba. Sabira ke macece kina da rauni sosai. Ki riƙe kimarki da darajarki ta ɗiya mace. Menene wannan daraja taki budurcinki, matantakarki shine mutumcinki da darajarki. In kika baiwa wani namiji dama ya lalataki tun kina waje bata hanyar aure ba, kinma rayuwarki giɓi kin cuci kanki da kanki, akwai azzaluman mazan da aikinsu kenan kawar da budurcin ƴan mata. Ta hanyoyin yaudara da dama. Sai kin nutsu sosai kin zama mai wayo, da ɓoye wayon kafin ki gane mayaudarin namiji. Kai Azgar namijine, kada ka sake ka zama daga cikin maza masu kawar da budurcin matan da suka yarda dasu. Zuchiyarka ta zama mai taushi da sanyi, da tausayin ɗiya mace sosai. Kar ka bari a gabanka ka zalunci ko wacce mace, bare kai da kanka ace kai kayi zaluncin. Kuyi haƙuri naga kuna ta jin kunya sabida maganar tana da nauyi ko? Ni uwace in ban wayar muku da kai ba, wa zai wayar muku dashi abokai? Ai nasan ba yau na saba yi muku irin wannan nasihun ba ko? Azgar tun kana yaro inayi maka irin wannan nasihar na kada ka bari ko abokinka ya kalli al'aurarka. Akwai abinda ya taɓa faruwa dakai a makarantar Islamiyya ba zaka iya tunawa ba kai. Amman ni gashi nan ina kallo Wani malaminku ke saka muku hannu a al'aura yaita wasa dashi, amman kai a ranar da ya saka maka kana dawowa gida bazan manta ba ina wanke wanke, sai ka faɗo jikina kana kuka zazzaɓi kau a jikinka. Kake faɗamun malaminku ne ya taɓa ma gabanka. Hmmm ranar munga tashin hankali ko da muka bi ba'asi ashe wannan malamin ya lalata yara a makarantar fin goma, yara maza ya kwanta dasu ta baya, harma yaran sun saba sanadiyyarka alkadarinshi ya karye. Sanadiyyar barinka makarantar kenan, kuma sanadiyyar haka a lokacin saida ake kulle makatantar sakamakon shige da ficen da Baba sojanmu ya dinga yi. To yanzu da ban koyar dakai ba, kaima da ya lalata mun kai an cuceni a banza. To dan Allah ku kula da kanku, kuma duk runtsi kuima mahaifinku biyayya akan duk abinda zaice ku yi, to kuyi. Abinda duk yace ku bari, to ku barshi kar ku tambayeshi dalili. Kamar yadda bana son ku tambayeni dalilin da yasa ba zan biku ba. Kuma ku sani ba lallai mu dinga waya ba. Bama lallai ku sake ganina nan kusa ba. Amman nasan duk daren daɗewa watarana Allah zai sada fuskokinmu da alkhairi. Innah mutu kuma ba tare da naga wannan lokacin ba, ina mai neman yafiyarku. In kuma kun dawo kun sameni zanyi farin ciki gaya. Kuyi haƙuri ku yafeni, nima na yafe muku har abada. Na yafe muku, kuma ina roƙon Allah yaima rayuwarku albarka, ya ɗaukaka darajarku. Ke Sabira Allah ya baki miji nagari adali, ki rayu dashi da farunciki, ku zauna lafiya kamar yadda kika buɗi idanu kika ganni ina zaune lafiya a gidan mahaifinku, kafin wannan abun ya lalata komai. In mahaifinki baiso kizo wajena da mijinki ba, ki yi biyayya. Azgar kaima Allah ya baka mace tagari wacce zata maye gurbina a rayuwarka. Kaima in mahaifinka bai yadda kazo da matarka wajena ba, shikenan kar kuyi gaddama kuyi biyayya. Ban yafe muku ba in kuka zo ba da yawunshi ba." Carab Azgar ya cabkemun hannayena yana kuka tamkar ƙaramin yaro. Murmushi nayi na sauke kaina ƙasa kurum. Bansan me zance ba tausayinsu tamkar ya halakani, musamman Azgar nasan yafi kusa dani, ya kuma fi nuna mun ƙauna gaya. Sabira dai hawaye naga tana sharɓewa ta ɗago ta kalleni ta kasa. "Ammi dake zamu tafi, babu inda zamu je sai tare dake Ammi. In kuwa ba zaki je Katsina ba Ammi muma babu inda zamu je. Ammi kiyi haƙuri kinji? " Murmushi nayi na janye hannayena tare da rungume hannun nawa a kirjina. Dame zanyi haƙuri Azgar? " Sai yayi ƙasa da kanshi yace. "Ammi nima ina jin zafi da ciwon Auren Asama'u da Baba yayi. Kuma wannan abun shi ya tarwatsa mana nutsuwa da farin cikinmu, kuma na kasa dena ganinsu a idanuna. Ammi bance ki yi haƙuri ki zauna dashi ba, nasan ba zaki iyaba ba zaki iyaba. Ammi ni na kasa manta komai a cikin kaina. A gabana a makaranta Asama'u take waya da Baba ba tare da mun sani ba, a gabana take maganganun soyayya dashi. Ammi ina tuno lokacin da nake riƙe hannunta muje Islamiyya, in tayi tsokana ta gudo bayana in bata kariya. Kika rene ta reno na haƙiƙa amman yau ace itace ta taɓa Auren Abbanmu suka rayu na shekara guda a tare. Wallahi har gobe ina mafarkan abubuwa da yawa. Ammi amman ba zamu rabu dake ba, duk inda kike ana..... " Azgar kar ka dinga kuka kai namijine inaso ka zama jarumi, sai dai kashbSabira ce ta kwaso jarumtakata, saurin kuka zai kai ka ƙasa fa" "Ammi zan zama soja kamar yadda kike so, jira nake in kammala Digirina tukunna, duk da na gama kusan zance bautar ƙasane yanzu a gaba. Wataran zaki ga Azgar a gabanki da kakin sojoji yana muzurai" Dariya muka yi harda Sabira mai share hawaye. "Ammi ki yafe ma Abba. Ki yi haƙuri ki bar komai ya wuce, kamar yadda Asama'u ta zama tarihi a rayuwarmu. Rashinta da abinda tayi miki duka yana taɓamu.' Kiran sallar Magrib ya katse mana zancan. Azgar yayi alwala ya tafi masallaci. Ni da Sabira mu kai sallah a ɗakina da Azgar ya dawo ya zubo mana abinci muna ci a tire. Duk sai mukai shiru dukkanmu abu ɗaya muka tuno, tunani ɗaya muke yi shine tunanin Asama'u a irin wannan da'ira ta cin abinci da muke samun yi jifa_jifa. Wannan dalilin yasa hirarmu batai armashi ba. Azgar ma tashi yayi ya fita, ina kiranshi ma bai juyo ba kamar kuka yake yi. Hmmm Sabira na ƙoshi in kin gama kije ki rufe a Kicin, ni zan kwanta sai da safe in mun haɗu kafin ku tafi ko? " Magana zata yi na hanata dole ta haɗiye maganar a cikin lomar abinci. Tana fita, na jiyo muryar Mijinyawa yana rakaɗa musu kira. Dama naji buɗe get ɗinshi. Ni dai ina zaune, da ƙarfin ikon Allah nayo wanka na fito na sake komawa kan sallaya ina jiran isha tayi. Ana kira a masallaci kuwa na miƙe na ta da kabbara na sallaci isha, sai na yi tagumi a kan sallaya ina tuno abubuwa masu dama na rayuwarmu ta baya. A da in akace haka ƙarshen soyayyarmu labarin zai tsaya, wallahi ko waye ya faɗa sai mun ƙaryatashi. In nace kowa ina nufin kowa. Sai gashi yadda ƙarshen ya kasance. Ƙila a daren yau in karɓi takaddar saki ta kwana a hannuna ƙila kuma zuwa gobe ne zan karɓa. Bayan na sauke ajjiyar zuchiya, saina ɗaga hannu nayi kutse cikin sunayen Ubangijina kyawawa na dinga ragargazo mishi kirari. Nayi tawassali da aiyukan jin ƙai da nake yi nace In dai dominka nake yi ya Allah, ba dan neman suna ba. Ubangiji ka haskamun sabuwar rayuwa mai cike da aminci, ka sanya hannu a lamarina kasa nayi murmushi, murmushi mai kyau wanda babu kuka a gabanshi. Allah kai ka halicci Hindu, ka halicci zuchiyar dake gaban ƙirjin Hindu, Ubangiji kaine Ubangijina kasan bazan iya zama da Mijinyawa inci gaba da yi mishi biyayya ba. Na kuma san sakamakon da zan samu in nazo gabanka a matsayin mace maras ɗa'a ga mijinta. Shi yasa na zaɓi rabuwa domin in rabauta. Ubangiji Allah kai riƙo da hannayena, ka sanya mun nutsuwa, tawakkali, haƙuri, ƙarin juriya, ka haska mun. Yarana Allah ka kula mun da rayuwarsu, Allah ya basu matar uba ta gari wacce zata zame musu uwa, Allah ka gani ban ma yarinyar dana riƙe mugunta ba, saima itace ta ƙulla mun cutar da abadan zafinta nanan daram." Na dinga magana da Ubangiji na ina bashi labari cikin salon adda'a, domin ni a nanne nake feɗe duk cikina, sabida nasan ina wajen maganin. Hannayena ina saukesu, wallahi sai ga ajjiyar zuchiya wacce ita tayi kanta da kanta. Sai naji kamar an zare mun wani dogon nannauyan abu daga ƙirjina. Naji na dawo sakayau wanda ada nauyin da nake ji kwatankwacin mai ɗaukar dala da gwauron dutse ne nauyin.
Chapter 82 · 0% Book details