← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 85

Sashe 53

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke Bibalo lafiyarki kuwa, ya da kyanki da wayonki kina Amarya me zaki yi da wannan abincin a cikin irin wannan katafaren gidan."? Na rasa yadda zanyi dasu dole na faɗa musu gaskiyar halin da ake ciki. Hmmm Mama tayi rantsuwar ban isa bata kunya a idanun kishiyoyi ba, dole in kashe auren in dawo gida. Amman kafin kashe auren tana so in mallaki manyan kuɗaɗen da zasu taimakama tafiyar zawarcina. Da zasu tafi Mama saida ta cika bako da kayan abinci, Sango shi kuma mutum ne mai bin diddigi da maƙon tsiya, yana shiga Kicin ya gane an ɗibar mishi abinci, kuma yaji labarin Mama ta zo. Ya shiga rashin albarka da gore_gore iri da kala bari in baku a taƙaice akan shinkafa mudu biyu dana aunar na siyar na sai nama na zuba a miya, ya sakeni da daddare misalin taran dare. Amman fa kafin wannan lokacin, da asiri, da ƙulunboto, saida na mallaki kuɗaɗe masu yawan ban mamaki. Asirine baya tasiri a kanshi, kasancewar malamin Mamana ya sanar mata, shima yana bin malamai sosai, sabida tafiyar kasuwancinshi, da gogayya da gaggan ƴan kasuwa. A daren na harhaɗa komai nawa na tafi, dama sutura kaɗai nazo dashi gidan. Na nemo mota ta kwashemun akwatunana kab, su Mama suna tsakar gida na shigo a lokacin Baba bai ma dawo ba ranar yayi dare sai washegari ya ganni, yayi ƙoƙarin sasantamu Mama ta buga kai a faranti tace bazan koma ba, ai Sango dukana yake yi, baya bani abinci, mane min matane, dukka baya ɗaya sharri ta bishi dashi. Kunji wannan, ashe Mama ta ja mun duk abinnan data lissafo shi zan tadda a gidan Alhaji Namadina ina kammala iddata washegari aka ɗaura aurena sai birnin taraiyya, Shima nayi rub da ciki kan dukiyarshi, na asirceshi, hatta uwarshi saida muka mallaketa, kishiyoyi da yaran gida ni Bibalo bana ma ta tasu sam, in suka ganni tsoro_tsorona suke yi. Yana duka, yana bin mata, amman dake ba zama ya kawoni ba, wallahi ko a gyalena na bashi dama yaje ya fantama. Ni dai kawai inji dumusu. Hala naita Aura ina saki, saida na Auri bakwai, waɗanda na dinga buga kansu a faranti wallahi. Na tara arziki sosai, na zama Hajiya, kyauna ya sake fitowa, na zama ƴar duniya ƙaƙas. Daga wannan mazaje bakwai sai ƙurata ta lafa, alkadarina ya karye. Amman nayi zamani. Unguwarmu kawai na shiga da mota ansan Bibalo ta shigo. Har mataimakin wani gwamnan wani garin na aura, bazan kama suna ba. Ina ya Allah, babu ya Allah. In gajarce muku labarin. Saida na zama ƙasƙantacciya wulaƙantacciya a hannun maza, saida na zama abar tausayi abar kwatance yau ina gidan aure gobe ina gaban Mama, abun duniyar na samu a hannun wasu, wasu na sata da kaina. Amman me duk wannan ya farune sabida talauci, da gasa ta iyayenmu mata kawai, sai muka ɗaura auren a turbar kwaɗayi, kuma masu iya magana suka ce in da kwaɗayi to da wulaƙanci. A aurena na takwas shine nayi aure domin rufin asirina ba domin kuɗi ba. Sabida matar da zata auri mazaje har bakwai, zawarci zai gana mata azaba sosai. Sabida ta saba da maza gaya. Da wannan dalilinne kuma, aka soma yawo dani, daga wannan zangon, zuwa wannan zangon baƙi. Daga ƙarshen _ƙarshe, mai tuƙa kurar ruwa ni Bibalo na aura a miji na takwas, kuma da gaske zaman auren zanyi jikina ya mutu, na fahimci muddin kace a kafaɗar ɗa namiji zaka jingina kina harin abun hannunshi, ba wai abinda ke kika mallaka ba a wannan zamanin, in ba zaɓaɓɓun maza ƴan aljannah kikai katari dasu ba zaman bazai yiwu ba. Inma ya yiwu dole ki haɗiye baƙin ciki da takaici kala da iri, duk macen da ta auri ɗa namiji da sunan kuɗi tana cikin matsala. A lokacin ga Mama ta rasu, Babanmu Allah yayi mishi rasuwa, babbar yarmu kuma miji ya shafa mata cutar ƙanjamau a sanadiyyar neman matan bariki. Kuma ta sani sarai tunda ba'a ɓoye yake yi ba, ta fifita son kuɗinshi sama da lafiyarta, kishi wannan bata yi. Amman kufa sani jahilci ya taka muhimmiyar rawa a cikin rayuwarmu sosai da sosai. Hmmmmmm dare yayi sosai ku bari zan ƙarashe muku labarinnan gobe da safe, dan ina kyautata zaton gobe zan fita a wajennan in sha Allah." Ajjiyar zuchiya na sauke tare da jinjina kaina. Wannan al'amarin babbane. Duniya ta cika tab da son abun duniya, ba mazan ba, ba matan ba, ba iyayen ba, ba surukan ba. Amman kamar yadda nake faɗa kullum ma ƴan uwana mata, haka Hajiya Biba itama ta faɗa. Duk rintsi ki nemi ilimi arabi da boko, in boko bai samu ba wajibine ki nemi na arabiyya ko dan ibadarki, in mijinki yaƙi barinki dole shi ya koya miki, in kuwa bashi da ilimin koya miki dole ya barki ki fita neman ilimi. Sannan duk runtsi duk bala'i ki riƙe sana'a, ko aiki ko duka biyun, kuma kisan darajar kanki. Ga sana'o'inan birjik, akwai na gida, akwai na shago, akwai na waya, ko wanne irine ƴar uwa ki faɗa. Wallahi matar da take juya kuɗi ba ɗaya bace da wacce ta zauna tana jiran abinda miji ya farauto ya bata ba. Hakaza matar da tayi ilimi ba ɗaya take da jahila ba, hakaza matar da tasan darajar kanta kuma, ko bata sana'a bata aiki, batai zurfin ilimi ba, tafi ƙarfin wulaƙanci a ko ina wallahi, mace mai kuɗin kanta ba ɗaya take da mace mai kuɗin miji ba. Duk yadda kuka kai da fahimtar juna kina da iyakarki a kan dukiyarshi, dukiyar da kika tara da gumin halak ɗinki babu wanda zai miki shamaki ke da abunki. Shi yasa ni Hindu zan sake zagewa in nemi kuɗi bakin rai bakin fama, zan kuma tsare kima da mutumcin addinina, ƙabilata, ƴaƴana, iyayena. Mata mu farka bafa lokacin bacci da miƙe ƙafa bane a gidan miji kina jira ya samu ya baki ba, duk ranar da bai samo ba shi zuru ke tagumi. Mazan yanzu kaɗanne masu zuchiyar ɗauke nauyin daya rataya a kansu, nace madallah da waɗannan mazaje ƴan aljannah. "Kash banso labarinnan ya tsaya a haka ba, Hajiya haƙiƙa na ƙaru matuƙar ƙaruwa, zan kuma dagewa akan sana'ata ta sai da omo, da sabulun wanki, da nake yi. Sha'awa da kwaɗayin komawa islamiyya ya kamani, ga islamiyya kusa_kusa da gidanmu in sha Allah zan shiga" Cewar Maman Junaidu kenan. Murmurewa nayi tare da jin wani ƙarfin guiwa akan aikina nace. In kika yi haka kin kyauta ke kanki zaki gyara abubuwa da yawa a zamantakewar aurenki, zaki san yadda ake zama da miji, kuma zaki san haƙƙoƙunki da kyau, zaki san irin haƙurin daya kamata kiyi, da irin wanda bai kamata ma kiyi ba, zaki san iyakarki, shima yasan nashi iyakar. Sana'a kuwa jigone babba, ita rayuwar dole sai da kuɗi take tafiya. To a matsayinmu na mata bai kamata ace mun zauna bama sana'a ba, shi juya kuɗi ai akwai daɗi, sannan kema zaki koyi yima kanki da yaranki hidima tun miji yananan ba sai ya mutu ya barki da yaran zaki koya a lokacin ba. Mata da yawa na sansu waɗanda suka samu damammaki mai yawa, Allah ya hore musu mazaje masu kuɗi, amman matan basui amfani da damarsu ba, babu sana'a wata babu karatun, sai dai taci tasha ta kwanta, ta ɗinka manyan suturu ta hau mota. Bata aikin fari bare aikin baƙi, bata san yadda ake juya kuɗi ba. Mazajen kuma suka mutu suka bar dukiya mai suna dukiya. Amman dake bata san zafin kuɗi da gwagwarmayar tarawa ba, sai kuɗin ya lalace harma kiji ana cewa ai dukiyar gado bata da albarka. Ta yaya zata yi albarka? alhalin zara akeyi a cinye ba juyawa ba, shi kuma zara baya barin dami. Sai kiga cikin ƙanƙanin lokaci komai ya ƙare ya zama tarihi, wahalar rayuwa ya soma, iyaka ƴan unguwa kiji ana yanzu yaran wane ke talla, ko kiji suna cewa Allah sarki rayuwa yanzu yaran wane ke gararamba a anguwa. Amman wannan yana faruwane kaɗai a ƙabilar hausawa, mu daure mu faɗama kanmu gaskiya, kuma mu karɓi gaskiya. In muka duba matan yarbawa ba haka suke ba, matan inyamurai, matan arago, matan ibira, matan yaruka da yawa, sana'a suke yi haiƙan. Kuma duk matsayi da muƙamin mijinta zaki ga ko ba ita zata zauna ba, tana da masu zama mata a shagunanta. A karɓa da haƙuri. To muyi amfani da lokaci da damarmu tun kafin mu zo muna cizon yatsa. Rayuwa bata da tabbas, gidan miji babu tabbas. Ki dogara da kan_ kin_ kanki, ki tsaya da dugaduganki bana wani ba, ki zama bangon da za'a jingina dake, ba wai ki zauna kina ganin wani a matsayin shine bangonki ba, daya faɗi zaki ci ƙasa. Ke Hajara kina son a shiga kotu a kwato miki hakkinki kuma Figo ya sakeki, ko dai a barki da mijinki ai muku iyaka akan wannan duka?" Ina da dalilai da yasa kuka ji inata nanacin zance, ku tambayi masu gulɗa da matsalolin aure, zasu baku labari sai ka dage ka tsaya ma mace daga ƙarshe sai tace a janye ƙarar ita tana son mijinta. "Haba Anty wallahi na haƙura da auren Figo saki kawai nake buƙata, in koma gida in nutsu. Makaranta zan shiga in samu ilimi, da gogewar rayuwa a hankali Allah ya ɓullo mun da wani mijin in yi aurena, miji nagartacce" Murmushi nayi na dafa ta. Hajara kinyi kyan kai, zan tsaya miki har ki samu takaddarki. Amman kiji tsoron Allah a duk abinda zaki saka a gaba. Kina take dokar Allah kin kaɗe har ganyenki. Ki sani sai kin girmama kan ki duniya zata girmamaki gwargwadon yadda kika ɗauki kanki da mahimmanci, gwargwadon muhimmancinki a idanun al'ummar dake kewaye dake, da waɗanda zasu tsallako su shigo rayuwarki." Gaga gaga haka muka kwana cikin sauro da kuɗin cizo gabaki ɗaya zarni muke yi wallahi, bacci ɓarawone su ya kwashesu ni kam kwana nayi ina ambaton Allah, tare da istigifari ƴar uwa kinsan sirrin istigifari kuwa? Matso kiji a duk bala"in daya tunkaroki, ko wata buƙatar kike nema Allah ya dafa miki, ko ma babu komai so kike rayuwarki ta yi inganci, tayi albarka komai ya dinga zuwa miki cikin sauƙi? To ƴar uwa ga
Chapter 53 · 0% Book details