Sashe 78
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
asali dake yammacin cikin birnin katsina ta dikko ɗakin kara. Unguwace mai dogon tarihin gaske sabida yana da alaƙa da lokacin mulkin sarautar Fulani ( Dallazawa) da kuma farkon mulkin turawa. An kafa unguwarne kusa da gidan yari na garin, inda manyan bayin sarki da masu riƙe da madafun iko ( kamar wazirin katsina na da) da suka gina gidajensu na Alfarma a lokacin. Misali manyan mutane kamar mahaifin shahararren attajirin nan Dr. Lema jibril. Dama tsofaffin janar_janar na soja suna da tushe a wannan yanki har ila yau Kusancinta da fadar sarkin katsina ( gidan korau) wanda aka gina tun ƙarni na goma sha huɗu hakan yasa ya zama babban mazaunin masu daraja da dukiyar gado A wannan unguwa ƙarƙashin wani babban gida mai kyau Salamatu zata zauna. Ba sabo bane gidan ginine irin na masu kuɗin da, gidan akwai yalwar tsakar gida da shuke_shuke masu tarin yawa gaskiya, duk jama'ar biki muka fito muna kallon gidan gamu da yawan gaske wasu motocin ma suna waje basu shigo ba, mata ne dai suke shigowa. Haka muka ɗunguma zuwa cikin ta wata ƙofa babba data sadamu da falon Salamatu. Nan muka tadda dangin mijinta, da su khadijan gidanmu, ƴan gidanmu dai su biyar harda Innar su Dije matar Baba dogaranmu kenan. Mu dai a falo muka ya da zango, Amarya kuma su Innarmu sukai ciki da'ita gida kam tubarkallah. Nan akai mana saukar girma ta manya, munga karamci gaskiya babu laifi asuwaki mukaita yi da kaji. Da daddare akayi Dinner mai nutsuwa ta macuwat mutane.. A gajiye tulus muka dawo gidan amarya wajajen sha biyun dare sai bacci Washegari na farka na tadda kiran Luba kusan sau bakwai. Ina kan sallaya nan inda na idar da sallah a ɗakin Salamatu na manta wayar. Luba Allah yasa lafiya, wallahi nace zan kiraki in muka dawo daga Dinne nadawo a gajiye. Ya mai jikin to amman kaddai jikinne" "Hmmm wallahi Hindu jikinne ko kinsan yarinyar nan abu kamar wasa a asibiti muka kwana. Idanunta ɗaya ya samu matsala gani ma bata yi a sakamakon naushin da yayi mata. Sunce dai in akayi mata aiki akwai yiwuwar ganinta ya dawo. Ɗayanma bata gani da kyau fa. Ni kam gaskiya Hindu ki makashi a kotu ya saketa kawai. Tunda tace ta haƙura da Auren har abada". Ajjiyar zuchiya na sauke tare da ambaton Hmm maza kenan. Shikenan Luba yau zamu dawo da wuri muna karyawa. Duk abinda ke akwai zamu yi magana. Zan yi magana da saudat ma ta shiga lamarin in yaso sai a tsayar dashi a kotu in yaƙi sakinta ta laluma. In kuma ya saketa zamu rabu dashi da halinshi, duniya zata yi mai karatu. Amman fa sai da yadda da amincewar iyayenta, da ma danginta. In babu amincewar wasu daga cikin danginta, luba haka zan tsame hannuna, in nema mata lafiya ta koma ɗakin aurenta ato. Ita baiwar Allahn ta na sana'a ko aiki ne? "Tana koyarwa a makarantar firamare da dibloma. Nata kinga bazai bamu wuya ba zata iya kulawa da rayuwarta. In ta samu tayi digiri ma kinga shikenan zata nemi wani aikin. Ta jingine auren agefe a yanzu ta maida hankali akan aikinta, da saita shiga makaranta da izinin Allah miji nagari zai zo ya aureta a lokacin itama tana da madafa. Zaluncin yayi yawa. Ba yau ya saba dukanta ba, har sumar da'ita ashe yake yi, to gashi yayi mata sanadin ido ɗaya, dan wannan ido da ƙyar zai yi aiki gaskiya. Gaba inta koma ba'asan me zai mata ba kuma. Macen da bata da madafa ke fakewa da zaman ƴaƴa. Kinsan Allah talaucine yawanci da rashin sanin inda za'a dosa. Ba ilimi, ba sana'a, ba aiki ba dole a zauna zaman yara ba. Yana lasa mata abinci yana zaginta ya zagi ahalinta. Tana ji tana kallo an maidata juji, an jingineta ana soyayya da wata matar. Hmmm Luba sai mun iso asibitin zan wuto kai tsaye, kafinnann Saudat zata zo." Da haka mukai sallama. Nan aka soma gaishe_gaishe da juna a falo kuma su Yaya Soja da Azgar da Qazzafi ina jiyo muryoyinsu. Su Yaya Saratu da su Jinjin anata raba kayan kari da aka aiko daga gidan iyayen miji dake saman layin da gidan salamatu yake. Zuwa tara mun gama komai har mun shisshiga mota Salamatu da mijinta sunata ɗaga mana hannu har muka fice a jere a gidan. Ni kuwa sai kallonsu nake yi ina mayawa. Haka kurum nake ganin tamkar ganina da Salamatu na ƙarshe kenan wallahi. Ƙarfe ɗaya muka shiga gida, kowa a gajiye yake ga gidan cike da baƙi musamman ɓarayinmu, ni inayin sallah ma na tarkace yaran suka kaini asibiti wajen Luba anan na tarar da labarin wai mijin Kaltume ya saketa ta waya ya turo da sakin. Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Duk da haka ya kamata kamar mu tsaya a kotu dashi sabida lafiyar idanunta bai dace ace sunci bulus ba Luba. Luba abun yayi yawa" Wallahi haka akayi muka maka mijin Kaltume a kotu dake mun tattara hujjoji ƙwarara kuma mun haɗu da ƙwararriyar lauya da alƙali adali. Zama uku akayi kacal shari'ar ta ƙare. Shi zai ɗauki nauyin komai na asibitin ta, sannan in akayi aikin idonta bai buɗe ba za'a hukuntashi hukunci mai tsauri harda ƴan uwan nashi ma. Bayan mun fito kotu iyayenta sukaita mun godiya mamanta har tana kuka dan jin daɗi. Ranar da aka saka na aikin ya zagayo ban bar asibiti ba har saida aka fito da'ita. Dr kuma ya nemi ganawa dani, naje na taddashi a ofishin shi, ya nuna mun waje na zauna. "Hajiya Hindu an yi aiki dai muna fatan ta samu lafiyar gani in sha Allah. Duk da dai dole zai kasance mai raunin gani sosai, da rashin jure haske mai ƙarfi. Nan da kwana bakwai zamu buɗe bandejin in sha Allah, mu ga yanayin aikin muna fatan samun nasara. Amman nace faɗuwa tayi ne ko kuma garin yaya hakan ta faru? " Garin zaluncin wasu maza, azzaluman maza inji Lubna michika. Ka ganta mijinta da danginshine suka naɗa mata na jaki gata nan dai ka ji ka kuma gani ai" Shi kanshi ji nayi na tsaneshi, ai shi kanshi ma ya gane hakan shi yasa yayi muƙus da bakinshi. Gaga_gaga haka dai Barira sati ya zagayo aka warware idanunnan wallahi ya mutu fa bata gani saida ɗaya dishi dishi shi ɗinma take gani, amman an yanka mata tabarau da kuma bata magunguna, harma da sake saka ranar sabon aikin da za'a kuma jarabawa. Ina rufe wannan kes sai ga sabon kes na wata mata Haule wacce miji garin neman matan banza ya kwasa mata ciwon sida wata ƙanjamau HIV. Tazo da safe ranar asabar muna gida dukkanmu mijinyawane ya buɗe mata ƙofa ta shigo. Da safen yazo wai yazo ganin yaranshi, kamar wasu masu shan mama, tana falo tana jirana Azgar kuma yana ta haɗa musu kayan tafiyarsu gobene tafiyar, inaji mijinyawa na ambaton sassafe zasu tafi, yana waya da Qasimu. Shine dalilin zuwan nashi, zai taimaka ma yaran su harhaɗe kayansu waje guda, washegari kuma su kama hanyar katsina. Ni kuma in yi firi. Mrs Bukhari To mu kwana anan sai kuma gobe in Allah ya kaimu.TSUREN TSIRIN... TSANDAURI... LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI