← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 85

Sashe 35

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hmmm wai kunsan me Auwalu yake faɗama Amarshi suna zaune a falo? " Su Luba suka amsa mata da "Aa" Ni kuma na yi ƙur ina kallonta kawai ina nazartarta. "Cewa yayi da'ita" "Ai a kwana ɗaya da nayi dake Amarya kin mantar dani komai in faɗa miki. Yau ɗinnan nasan nayi aure na san kuma na kwanta da cikakkiyar budurwar data tattalamun tantanin budurcinta, ta kawo mun ɗakin sunnah na alkinta abuna." Sai naji gabana ya faɗi ras sabida a iyakar sanina nasan Auwalune namiji na farko da ya taɓa tarayya dani. Saina shiga tunanin to me ya tauye mun nawa budurcin Auwalu yake nufi? " Amarya sai ta sauwaƙemun ta hanyar cewa. "Bazawara ka Aurane Diya, naji a batunka kana maganane kamar bata kawo budurcinta bane, ko bazawarace, ko dai tsalle_tsalle tayi?" Idanuna na lumshe hawaye suka zubo mun masu ɗan karen zafi. "Budur bazar ce. Abinda yasa nace dake hakan, ta jima batai auren ba, sai kuma ta zama likita. To kinsan ni'ima da albarkatun jikin mace tana girma suna ja baya. Sai da abokaina suka ce in inaso in more Aure in ɗauki ƴar sakandare wacce take kan ganiyar balagarta masassaƙin budurci hankalinshi ya dawo kanta. To a lokacin yarintace bana so, saida na aureta sai na gane yarintar da shagwaɓar tana da matuƙar amfani. Ko gidanmu can Bauchi naje in naga su Nazifa suna ma Dadanmu shagwaɓa sai abun yai ta bani sha'awa auren yara duniyane. Kema harda shawaɓarki a cikin abinda ya sake gigitani. Kinga wannan kukan shagwaɓar? Ba dama ne" Dariya suka yi, da jin amon muryarta tayi farin ciki sosai da jin wannan labari daga bakin Auwalu. Bakin da a tunaninta bazai mun ƙarya ba. Ni bansan ma ya iya hira da mace hakan ba, dan ko zamanin da muke budurwa da saurayi bamu yi fiye hira ba, yadda na sanshi baida sakewa kullum a ɗaure yake, ga saurin fishi, da maida ƙarami ya zama babba. Abun mamaki sai gashi muryarshi zaƙwai_zaƙwai, yana hira shine harda sharri, da aibatani a gaban matarshi, matar tashi ma wacce kwana ɗaya tayi kacal a cikin rayuwarshi fa. Hmmmm ya salam. Da ƙyar na jawo ƙafafuna na fito bayan na saisaita kaina, na share hawayena. Murmushi na ƙaƙaro na yafa a fuskata muka gaisa da Amarya ina daga tsaye. Shima gaisawa muka yi ina ƙare mishi kallo hannunshi a sagale ana Amarya yana ta wasa dashi. Inda ranka dai zaka sha kallo. Abun almara. "Dama ke muke jira mu yi kalaci Maman Abba" Cewar Amarya dake nuna mun dainin ɗin babban falon. Ayya ayi kalaci lafiya ni inna je ofishina nayi acan ni sai na dawo" "Ahh dama inaso in haɗeku muyi ƴar maganar da akeyine jiya babu lokaci" Kallonshi nayi na dubi agogona nace. Ita ƴar maganarnan a barta zuwa in dawo bana wasa da aikina. Amarya saina dawo a kula da gidan da mai gidan" Na kwashi yarana muka tafi. Hmmm wasa farin girki tun daga lokacin har izuwa yanzu zuchiyata bata huta ba, Auwalu ya tsiro da abubuwa iri_ iri abinci wannan ya dena ajjiyewa, yana dai kulawa da yaranshi. Ni ɗinma zaman jiran lokaci nake yi kawai. Bayan ya gama kwanaki bakwai yazo neman daɗi, wai tafiya umara yake so yayi da'ita in suka je suka dawo sai nima muje yayi mun alƙawari wa ya mutu wa ya dawo. Abinda yasa zai soma tafiya da'ita akan wannan alƙawarin ta amince da aurenshi. Babban abinda yake ƙaramun mamakinshi. Yadda ya sauya tamkar ba shine wannan auwalun me ɗaure fusa, shiru_shiru, saurin fishi, gaba ba?" Ya warware annurin fuskarshi baya ɓoyuwa sam. Ba sai ka kaini ba Allah ya huwace mun abun biya, dama na riga da na biya faɗamane banyi ba, sai yanzu dai data kama, amman lokacin tafiyar kawai nake jira in yazo ƙila kafinnan ka shigo wajena sai in faɗama. Batun ƙara kwana wallahi Allah ni sumayya na yafe mata kwanan, tunda dama ni dai lallaɓawa akai ta tayi dani, zan mayar da hankalina a kan tarbiyyar yara da kulawa da aikina. In kuma sallamata zaka yi duk ɗaya Auwalu. Tunda sai inga zamana kamar zai iya takura muku. Ni dai kaga ba amfanin komai zanyi ma ba, daga nan har duniya ta naɗe" Kunji wannan? Kuma a lokacin ban biya kuɗin umara ba wallahi, biya dai nayi bayan fitar Auwalu, dake ina da fasfo ɗina a ajjiye. Na kira abokiyar aikina ta haɗani da egen. Azumi na goma sha bakwai jirginmu ya ɗaga zuwa umara ta kano ni na tashi, ta ina suka tashi can ta matse musu dan ban sani ba, na dai san Allah ya dafa mun na rigasu tashi. Babban abinda zaisa kisan mata basu da kirki da yaya_yawansu. Wai wannan bushasshiyar Amarya saita tsiri rigima da Auwalu akan wai damme zai biya mun umarah, alhalin ita yayi ma alƙawarin zata soma zuwa, wai take ce mai da ta san yana son matarshi da yaranshi ai da bai aurota ba. Ita taga inna dawo aiki duk sai ya sha jinin jikinshi, alhalin ya faɗa mata zaman haƙuri kawai yake yi dani hmmm. Naje umara, nayi ma Allah kuka, nayi mishi kirari akan ya dubeni, yana kallon Auwalu yai mun maganinshi. Shikenan Aurena ya zama haka inje aiki in dawo, in ma yarana girki mu ci mu kwanta aikina kenan. Auwalu ko ɗakina bai ƙara shigaba, Shekara data zago shi da'ita suka tafi aikin hajji wata shekarar na tafi nima to ina da kuɗina, amfanin neman kenan, rayuwata nake yi fes dani, Auwalu dai ya jingineni kamar yadda Sunusi ya Jingine Luba, amman gara Luba sau biliyan. To su fa amman dangi gani suke duk Auwalu ke mun komai, suturu, motar hawa, hajji, da umara, duk ni naima kaina da gumin halak ɗina. Amman sai albarka iyayena suke bashi, yana karɓa. Kaje biki a ganka kayi firesh, kasa kaya mai tsada, ga mota, ga gudunmawa mai tsoka duk tunaninsu miji dai. Dangishi ma haka suke gani kamar ma a kaina ya ƙare suke gani. Dan wulaƙanci an san kuma kana aiki fa. Kwatsam yace ni da yara mu dawo Kano a lokacin yaro ya samu gurbin karatu a Kano. Shikenan muka dawo gidanshi daya gina a Kano ya tashi ƴan hayan fat ɗaya muka dawo. Watanshi bakwai ban sakashi a idanuna ba, mukan fi sati bamui waya ba dan daga wannan ranar ban sake ɗaga wayata na kirashi ba, in ya matsu shi yana kirana. Da Amarya ta haihu banje ba, yayi juyin duniya naƙi fur haihuwa ta biyun dai naje ana gobe suna nayi mata barka a ranar na juyo. Amman zama tsakanina da Auwalu babu bazan yi ba in shine Autan maza. Kuma yaronnan yana kammala jami'a, ƙanwarshi lokacin tana mataki na biyu a jami'a, to lokacin sai in nemi takaddata auren ya ƙare, in ci gaba da rayuwata, dan nasan zaice bazan riƙe yara ba. Shi yasa naita turawa har zuwa wannan lokacin. Allah yasa nima bani da ra'ayin riƙesu, kuma Allah bai yini da ƙulafacin yara ba sam. Hmmm wannan shine labarina, iyakar wanda zaku samu" Kaina na shiga girgizawa kawai, Saudatu ce tace. "Kenan ke babu wani hira ta fahimtar juna a tsakaninki da Auwalu?" Kina ji fa tace ita bata sanma ya iya hira da laluma ba har saida amarya tazo" Na tari Saudatu. Sumayya kuma tace. "Ai dariya wannan zan iya ƙirga sau nawa yayi mun tun farkon aurenmu. Amman bayan zuwan amarya kullu yaumun suna babban falo suna hira nake dawowa in taddasu. Wallahi Auwalu ashe har dariyar mugunta yanayi irin ta Uzairu zuchiyata." Murmushi nayi ma Sumayya tare da cewa. A hangena ke da Auwalu ruwan kashe gobara kuke nema a lokacin da iyaye suka ɗaura muku fireja. babu haƙiƙanin soyayya da dacewa da juna a tsakaninku, balle fahimtar juna. Ko ko dai ke kina sonshi Sumayya a lokacin? Sabida in akayi la'akari da yadda aka haɗun da kuma yadda komai ya tafi banga soyayya ba gaskiya, ni ko ku kun gani Luba? " Luba tace. "Gaskiya shi dai Auwalu bana jin yana sonta, kawai ya amshi Sumayyane domin faranta ran iyayenshi" Saudat tace. "Ba za'a rasa son ba tunda ba dole sumayya tayi mishi ba, ba kuma dole iyayen nashi suka yi mishi ba" Sumayya tayi dariya duk ta bibbimu da kallo kafin tace. "Auwalu ya soni ne sabida kawai iyayenshi wa'adi suka bashi akan in wa'adin ya cika za'a aura mishi ƴar uwarshi, har yarinyar na sani a Bauchi take duk wani sha'ani inya tashi na famili muna haɗuwa da'ita, tayi aure harma Auren ya mutu yanzu haka zawarci take yi. Harma naji labarin Auwalun na zawarcinta. Nayi kuskure mai girma dana amince mukai Aure da Auwalu a irin halin ko in kular da yake nuna mun gaskiya. Amman ko babu komai ai na soshi kuma na kula dashi, na ciyar dashi, na tufatar dashi, na rungumi aurena a lokacin da bashi dashi. Na shanye abubuwa da yawa sabida bakin mutane bana so yayi tasiri a kaina tunda sai cewa suke yi idona ya buɗe bazan iya zaman auren ba ma" Ai kinji irinta ko Sumayya? Nifa bana yin komai dan in burge kowa da komai. Duk yadda kika so ki burge mutane baki isa kin burgesu ba. A lokacin da kike ganin kin ƙure burgewarki, a lokacin zaki ji kushe daga wajensu. Bazan kashe kaina sabida ku ba wallahi " "Ai ke Hindu zuchiyarki na da jumurin kawar da kai daga komai ma. Nabi shafinki ai naga yadda maza suka saka miki jakar tsaba sunata caccakarki kamar me" Dariya muka saka dukkanmu nace da Sumayya. Kuma ni kinga bana ma karanta kwament bare in gani ba. Ko lokacin da nake dubawan, nifa zagina da akeyine yasa na gane abinda nake yi saƙwan na isa. Yarane ma suke damuwa musamman ɗanki Azgar. To shima na huta da mitarshi tunda nace ya dena bin shafin nawa ya sakama zuchiyarshi risilama. Hukuncin da kika ɗauka yayi daidai na rabuwa da Auwalu, nayi farin ciki da baki taɓa yadda kun kuma sake haɗa jiki dashi ba. Kinga batun rigasu zuwa umarannan? Ya tafi dani Sumayya. Amman kinsan da kece kika jingine Auwalu, kika hanashi kanki shekara da shekaru. Da yanzu an jaki an jefaki a wuta, amman fa mutane. In
Chapter 35 · 0% Book details