← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 85

Sashe 67

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

samuwar ciki, shi kuma sai ya ɗaure fuska yayi tamau dashi har muka iso gida bai kulani ba, ni kuma a lokacin ko ƙwaƙƙwaran motsi tsoron yi nake yi sabida kar wani abun ya samu cikin jikina. Muna shiga ciki na nemi waje na zauna kusa daf da Nazifi domin naji menene damuwarshi. "Damuwata shine wannan cikin a zubar dashi Saudatu, bana buƙatarshi yanzu kuma kar ki manta makaranta zan mayar dake inata fafutukar nema miki gurbin karatu, kinsan da kin samu ciki kika yadda kika haihu shikenan cikar burinki ko? Ni kuma bazan iya zama da macen da iyakarta digiri ɗaya ba, kinsan gidanmu ƴan bokone sosai, matan yayyene daga me mastas sai masu phd bazan kasance a ƙasa dasu ba, ni da nayi karatuna a waje, nake aiki a waje kuma. Dan haka dole a zubar da cikinnan" Ai sai na fashe da kuka sabida bani da abun cewa, ni gashi bani da kowa a ƙasar ya hanani kuma mu'amala da kowa yace baya so. A kusa damu akwai wata bahaushiya mai yara dana taɓa ganinta ta taga, hausa sosai suke yi harma da zanenta na uku_uku irinna kanawa a hagu da daman fuskarta, tsoron fishin Nazifi yasa na kasa fita mu gaisa. Nayi kuka tamkar raina zai fita wallahi ko uhum Naziru bai ce ba, saima fita da yayi ya barni a zaune a wajen kawai. Ni na rarrashi kaina na ƙwarara jikina na tashi na gyara gida, nayi mana girki. Haka na wuni sukuku saida na kira gidane ma na ɗan samu sassauci a raina amman na rasa ya zanyi da raina ni dai inason cikina, kuma inason mijina ina, kuma son karatu, shi kuma yace sai dai in zaɓi ɗaya ko a zubar da ciki in ci gaba da karatuna kuma babu ni babu kishiya, ko kuma in haihu in koma gida najeriya, kuma bazai barni aiki ba bazai barni karatu ba, sai dai inta haihuwa in kula da yara shi kuma ya auro wata macen mai ilimi. Satinmu biyu muna rikici duk na rame na fita a hayyacina haka dole na amince zan cire cikin shine fa muka samu zaman lafiya. Allura yayi mun ta zubar da ciki. Nayi ciwo nayi ciwo har shi a karan kanshi ya ɗauka mutuwace zanyi in faɗa muku." Fasali ta ja tana share hawayen da suka wanke mata fuskarta. Luba ce ta miƙo mata tishu ta amsa ta yago kaɗan ta goggoge fuskarta kana taci gaba. Na jima babu lafiya a jikina nafi shekara bana jin daɗi sam, ga magunguna kullum Naziru yana bani jiki dai babu daɗi ga yawan ciwon mara. A haka harna samu gurbin karatun digiri na biyu a Jami'ar Georgetown university center Wacce take a tsakiyar birnin Washington DC kusa da koton ƙoli ta Amurka (u.s supreme court) da kuma majalisar dokoki wanda hakan na taimakawa mu samu hoton aiki cikin sauƙi ( internships) haka na soma karatuna cikin aminci, harma da tafiya tayi tafiya nafi ƙaunar makaranta sama da gidana, dan Nazifi ya tsiro da sabon ɗabi'ar yawon dare koma ince kwanan waje ya kan shigo gida a sanda yaga dama, ko na ɗaga waya na kirashi baya ɗauka amman baya bani hutun mu'amalar aure madamar ba jinin al'ada nake yi ba, ko rashin lafiya nake yi sai ya kwanta dani. To karatunmu yana da wuya, in nace zan ɗauki matsalarshi in saka a zuchiyata zan samu matsala da karatuna, ni kuma bana fatan abinda zai bani matsala a karatuna sai na ɗauki lamarinshi na watsar na mayar da hankali sosai akan karatuna. Gaga_gaga karatu nata tafiya na saba da mutane sosai, a makaranta maƙociyata maman Haifa itama muka saba sosai takan shigo gidana nima in shiga gidanta, harma in yi bacci ba tare da sanin Nazifi ba, ina shekara ta ƙarshe a makaranta sai ga ciki nayi farin ciki nayi murna. Na muku tsallake ashe daga cikin magungunan da Nazifi yake ɗurkamun kullum akwai na hana ɗaukar ciki a ciki bansani ba. Gashi bai amsheni ba ashe shine yake ta muƙurƙusan jikina ranar da asirin zai fasu, maman Haifa ta shigo mun ni kuma na ɗakko magunguna zan haɗiɗiya duk na ɓalla sai tace. "Lallai matarnan ashe maganin hana ɗaukar ciki kike sha sabida karatu, ba zaki haihu ko da sau ɗaya bane, yarannan watarana su zasu tagajemu a lokacin da mukai rauni, me zai sa ki sha maganin hana ɗaukar ciki" Ai sai naji gabana ya yanke ya faɗi ras, to a lokacin naso ɓoye mata halin da nake ciki amman ruɗun dana shiga sai gani washegari a gidanta, na zayyana mata halin da kab nake ciki kab nan tasa hannu ta tsamemun maganin hana ɗaukar cikin. "Kibi a hankali maza da yawa suna cutar da matayensu da suka ƙetare wata ƙasar dasu. Ni ɗinnan da kika ganni babu irin abun da ban fuskanta ba, kainane ya waye na daina ɗaukar komai, shi yasa na samu lafiya. Amman a da lokacin da ban samu aiki ba ina zaune ba kuɗi, da iya miji na dogara ga matsin lamba daga iyaye da dangi, su gani suke yi wani kuɗine a ƙasar waje basu san wahalarta tafi daɗin yawa ba, jibi a wajen da muke rayuwa. A hakanma mu ƴan gata ne sosai. Ki kwantar da hankalinki ki lulluɓeshi baibai kawai ko cikin kika samu kada ki sake ki sanar mishi har sai ya bayyana kanshi, a lokacin da bashi da abinda zai iyayi sai dai kawai ya zubama sarautar Allah idanu" Maganganun maman Haifa su suka ƙwararani sosai har na kammala karatuna na mastas sakamako ya fito mai kyau Alhamdulillahi, harma Nazifi yayi mun alƙwarin zai tuntuɓi abokinshi Alex baturen Burtaniya ne lauwa anan Washington DC ɗin akan batun aiki. Shiru aiki yaune gobe ne shiru in nayi mishi magana sai yace samun aiki a wata ƙasa ba abu bane mai sauƙi ba, in sa haƙuri watara kwatsam aikin zai samu. To haka dai naita jiƙawa ina matsewa da daɗi babu daɗi inata turawa da ƙarfin ikon Allah. Cikin ƙudurar Allah sai da cikina yayi wata bakwai kafin Naziru ya gane ciki gareni shima ya farune ta dalilin na fito wanka ina tuɓe ina shafa mai ya shigo bagatatan shine ya gani. Wai kunsan sai da Nazifi ya dokeni da wannan ciki duka tamkar Allah ya aikoshi, ya dinga ma cikina mahangurɓa, ya fice a gidan ya barni ina murƙususu ga jini ya ɓallemun bani da mai tagazamun in taƙaice muku dai sanyin asubane ya farfaɗo dani na ganni cikin jini mai yawa daskararre. Da dabara na iya shiga bayi nayi wanka na kintsa na tafi asibiti yaro lafiyarshi ƙalau galabaita yayi shi yasa baya motsi, amman yana lafiya haka likita ta ce mun. Na kaɗo kaina na dawo. Nan na shiga sabuwar rayuwa sai in fi sati bansa Nazifi a idanuna ba, in zai zo ma sai in ganshi a bige yana tumɓele wallahi. Akwai sanda aka buga mun ƙofa ina buɗewa naga matan turawa biyu sun dawo mun da Nazifi, babu yadda yake, dare daga cikin darare masu muni kenan a rayuwata a daren na soma naƙuda sai Maman Haifa na kira ta kaini asibiti na haifi yarona Ahmad. To a lokacin sai na samu gata mahaifiyar Nazifi da Anty Kulu sun tawo kafin suna basu tafi ba sai da na gama wanka tas, kafin suka tafi. Naso in bisu amman Nazifi yaƙi fur. Haka naita murzawa Nazifi ya bayyanamun ɓoyayyen halinshi da ya ɓoye mun a baya. Mane min mata, mai shaye_shaye, mata har gida yake kawosu su zauna a ɗakinshi, abun takaicin mata kala_kala yake kawowa duk wacce ta tafi ba lallai kiga ta dawo ba, sai dai gobe ya kawo wata. Watsewa dai tamkar ba ɗan musulmai mai tarbiyyar islama ba. In zan tsaya baku labarin irin azaba da uƙubar da nazifi ya bani kan ku bazai ɗauki duka ba, da ilimina da wayewata amman na taku na daku sosai, zuchiyata ta samu ciwo hawan jini da ciwon zuciya duk suna tattare dani, yanzu haka kafin Allah ya kuɓuto dani na dawo gida Najeriya da zama a lokacin yarana biyu suna karatunsu mai inganci na haƙura na zauna sabida gobensu, ilimi acan ya bambanta da ilimin nan gida magana ta domin Allah kenan. Kwatsam yace in tattare dani da yara zamu koma gida aimun magani a gida tunda ciwona yaƙi ci yaƙi cinyewa. To ta yaya zai cinye alhalin kana ji kana gani miji ya ajjiyeka baya ta taka, sai ta karuwanshi kawai danma taimakon da Allah yaimun da yaran suka tasa sai karuwan suka dena zuwa gidan, sai dai shi ya fita ya same su kamar dai lokacin amarcina. Kullum da irin ƙalubalen da zan fuskanta, hakan yasa ciwo yaƙi ci yaƙi cinyewa. A lokacin da muka tawo ni da yara babu ɗigon so ko ƙaunar Nazifi a zuchiyata asalima zaman na dole kawai nake yi sabida Hajiyarmu da take jaddadamun in riƙe mijina hannu bibbiyu, in dai inason farin cikinta to in farantama Nazifi ita na sallameta. Kunsan sabida me?" "Sai kin faɗa Saudatu" Cewar Mariya Habibu kenan wacce take shara ƙwalla. "Sabida ya gama siye dangina da nuna karamci. Hatta gidanmu saida Nazifi yayi musu gyara ga kuɗi da yake yawan turama Hajiyarmu, sannan duk abinda ya faru a dangina aka faɗamun shi da kanshi zai buƙaci lambar asusun bankinsu ya tura musu kuɗi mai tsoka. Ya toshe duk wata kafa da zan tsugunna in kai ƙorafina shi yasa ma ban gwada kai ƙorafin ba na haƙura na zauna a kan yarana. Na gina rayuwata na samu aikina, ina zuwa sai ya zamemun farin cikina. Duk sanda Nazifi ya kirani in ɗauka, in shekara za'ayi bai kirani ba inanan aiyukan dake gabana sune a gabana wallahi. Ya jingineni tsawon shekaru, yadda kuka san babu hakki." Ajjiyar zuchiya ta sauke tare da jawo jakarta ta ciro mana tulin magunguna bature ta zubesu a gabanmu. Waɗannan dasu nake rayuwa Nazifi ya illatar dani, ya salwantar mun da lafiyata, ya ɗagamun rayuwa a haɗari. Ribar aure na samun yarana biyu ne kawai sun girma sunata karatu. Mrs Bukhari. Mu kwana anan sai zuwa gobe.
Chapter 67 · 0% Book details