← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 85

Sashe 44

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

na watsa ruwan zafi a jikina tare da ɗauro alwala na fito na shiga sallah kamar dai kullum. Na faɗa na sake faɗa muku ƴan uwana mata. Dukkan abinda kike yi a rayuwa ko minti sha biyar ne ki tashi kiyi alwala, ki faɗama Allah damuwarki ko buƙatarki, muddin kika ga buƙatar taki bata biya ba babu alkhairine a cikin abinda ke baki da sani akai, kike roƙon Allah ya baki. Sallah dare makamine babba wanda ya kamata mu riƙe. A lokacin da kowa ke bacci, kin ɗauke haƙarƙarinki a ƙasa, in fuskanci alƙibla kuna faɗama Allah damuwar da ta dami rayuwarki. Kina godiya bisa ƙofofin ni'ima daya buɗe miki. Ki riƙe salatin Annabi saw, da istigifari. Ko su kika yi, bakya buƙatar sai kin jeroma Allah buƙatun da kike ɓoye a zuchiyarki, Allahn shi ya halicceki, ya halicci zuchiyar dake gaban ƙirjinki, shi yafi kowa sanin rauninki. Kiran sallar farko mijinyawa ya buɗe ƙofar ɗakina ya shigo, dake a buɗe ta kwana, tunda ya fita ban kulle ba. Juyowa ban ba, inata jan jarbi abuna. ", ashe kin tashi, nayi tunanin ko nauyin jikin zai hanaki tashi ai" Shiru. Mun tafi masallaci Tutar so" Har ya juya, ya juyo ya dubeni. "Rabon da inyi bacci mai ni'ima, harna mance, ƙamshin Humrarkinan mai sirri yayi tasiri jiya a jikina, iskar dana shaƙa a cikin ɗakinan, cakuɗe da iskan numfashinki da wannan Humra taki harna manta yaushe na jini a irin wannan yanayin. Ina kewar komai daga gareki inaji inama mafarki nake yi zan farka ace duk komai a mafarki ya kasance. Inama ki kasance mai yafiya, mantuwar zunubina dana nayi farin ciki. Allah ya shaida na tuba, mala'ikun Allah sun shaida nayi tuban gaskiya. A kullum na kai goshina ƙasa ina roƙon yafiyar Ubangiji, ina roƙon Allah ya sanyaya miki zuchiyarki, ki yi haƙuri mu ƙarashe ginin da muka gina ya rage ƙarashe kawai" Kallonshi nayi zuchiyata na tunzura inaji tamkar in zazzageshi a ƙalla ko na ɗan huce. Wallahi bazan taɓa iya ci gaba da rayuwa da mijinyawa ba. Amman naga halama so yake ya kaini bango, shikenan zan ɗauki matakin rabuwa dashi a shariance, dama mutumcin shine a gaban yaranshi bana so ya zube, amman na lura tonuwar asirin yafi so, zai ko ga sammaci. Masu ganin na zafafa, ko naƙi in yafe ma mijinyawa, ku dakata har zuwa lokacin da kuka gama jin ƙarashen labarin rayuwarmu ta baya. Sannan ni nace na yafe mishi, ko ban yafe mishi ba, in yayi tuba mai kyau Allah zai yafe mishi. Ku fahimceni zamanne bazan iya ci gaba dayi dashi ba wallahi. Kuma banyi laifiba. Kin taɓa rainon ƴa mijinki ya nemeta sukaita aikata aikin ashsha, kin taɓa renon ƴa mijinki ya gama zageki a gabanta, ya kuma aureta da ranki. Kinsan raɗaɗin, kinsan zafin? Nayi imanin matan da suke maganganu akan Hindu ta zafafa wallahi in watace saita mutu, ko hawan jini ya doketa, ko ta ƙona gidan, ko tayi musu terere bankaɗa musamman a lokacin data kamasu akan gadonsu na sunnah hmm. Fita yayi dama baya buƙatar jin abinda ke bakina, yafi kowa sanin bazan taɓa tankawa ba. Bayan na idar da sallah nayi azkhar, sai nayo wanka na shiryo fes na fito dan mu gaisa da yara. Saida na tsaya a kicin na jona ruwa a buta, nan naga ƙwai da biredi sinƙin_sinƙin mijinyawa ya ajjiye. Ƙwai Azgar ya soya mun, ni kuma na dafa shayi, a kicin ɗin muka gaggaisa, naji lafiyarsu. Musa ya leƙo ya gaisheni, na amsa mishi kadaran kadaham tare da miƙa mishi kayan kari. A gurguje nake komai inayi ina kallon agogo. Shida da rabi na fice ba tare dana yi sallama da kowa ba. Na dai faɗama Azgar ya tabbatar sun fita da Musa sun kulle gidan. mijinyawa a waje na wuce shi yana motsa jikinshi, da kallo kawai ya bini, kai tsaye sai gwammaja adireshin da wannan baiwar Allah da miji ya bata kashi ɗinnan. Ina isowa unguwar na tambayi yara sunan inkiyar gidan data bani suka nuna mini ina kusa da gidanma. Gidan harda get babba kusan ma yafi ko wanne gida kamar dama_ dama a unguwar. Ba mugun kyau gareshi ba, a ɓuɓɓule ma yake get ɗin shima ko fenti babu kamar yadda gidanma babu fentin sai dai gidan babbane a tsukukun shine yafi kyau. Tura ƙofar gidan nayi na shiga mata yama_yama a tsakar gida anata hada hadar safiya ga yara kamar tsaki. Wata matar ƙabila na tambaya wajen Hajara nazo. "Ummm tana ɗakin Maman Junaidu, ga ɗakin can mai jan labule, amman dai tafiya kika zo kiyi da'ita dai ko? In ba haka ba mugun mijinnan nata sai ya halakata, sannan hankalinshi zai kwanta" Murmushi nayi nace. E tafiya nazo yi da'ita" Harna wuce ta dawo dani da cewar. "Baiwar Allah daga can garin nasu kika tawo, a waya ta kiraki ne? Lallai wannan karon abun yaci tura tunda har Hajara ta iya neman agaji, matar da ko ihu bata fiye yi ba in mijin ya sha giyarshi yana jibgarta yana amai" Idanu na zare bansan sanda na furta. Giya fa kika ce, au giya ma yake sha ya jibgeta kenan?" Saurin rufe bakinta tayi alamun tsabar gulma dake cintane yasa tayi suɓul da baka. Sai kawai na girgiza kaina na nufi ɗakin data nuna mun bayan na dakata mun gaggaisa da bataliyar matan gidan. Sai kallona suke yi kamar zasu cinyeni. A dokin ƙofar da aka nuna mun nayi sallama wata murya ta bani izinin shiga na shiga a hankali. Hajara na kwance a doguwar kujera fuskarta ta aune, ga wani jini daya taru mata a kusa da fuskarta, bakinta a fashe da saman idanunta. Mai ɗakin kuma tana zaune a ƙasan kafet tana yanka tuwon ɗumame ga risho a gabanta, shayi sai tafasa yake yi yana fidda ƙamshin citta. "Sannu baiwar Allah ga waje zauna. Hajara matsa mata" Kasancewar kujerar ita kaɗaice a ɗakin. Yi kwanciyarki ƙasa ma ya isheni nagode" A ƙasan kafet na zauna muka gaisa da wannan mata, kana Hajara ta gaisheni na amsa ina kallon yadda mijinta ya sauya mata halittarta. Ke kuwa Hajara me kika yi da mijinki ya jibgeki haka, da alamu ba yauma ya saba dukanki ba, sabar mishi kika yi yaita jibgarki kamar ubanki da sunan aure. Wai me yasa mace da kanta take ɓarar da damarta, kimarta darajarta? Har kullum ina faɗe ina mayawa wata fuskar tafi gaban mari. Wanne irin laifi mace zataima mijinta in da soyayya, da darajarta, yai mata irin wannan dukan sa'an, kuma yayi tunanin zasu ci gaba da aure harma suci gaba da mu'alamar aure? Baiwar Allah kiji mun wannan abun, wai ashe lalacewar da muka yi da son nuna ma maza sai dasu dole zamu rayu, duk irin cutarwarsu a garemu ashe har ya kai irin wannan matakin? Jibi fuskar Hajara fa wanne kamilin magidanci, nitsattse,wanda yasan darajar jinsin mata, mai daraja iyayenshi, da matar aurenshi, mai addini, da sanin ya kamata ne zai yi wannan ɗanyen aikin" Ajjiyar zuchiya ta sauke Hajara kuma sai kuka mai nishi take yi. Wannan mata tana sassaka tuwo a cikin miya tace. "Baiwar Allah wallahi Mijinta tantirin mugune, azaba kaɗai yake gana mata, duka kuwa ta mayar da kanta tamkar jaka, dan tana karɓarshi taƙi ta sanar a gidansu balle a duba irin matakin da za'a ɗauka, ni nayi mamaki ma da take sanar mun tayi magana dake zaki taimaka mata. Yanzu duk dukannan da yayi mata kuma yace ta bar mishi gidanshi a daren, sabida babu kishinta a ranshi balle tunanin abinda kaje kazo game da fitar ta a cikin duhun dare, in akayi la'akari da ita ba ƴar gari bace, shima zuwo ne uwar ɗaki kaɗai gareshi, kuma ba nan kusa take ba. Da mugun zazzaɓi ta kwana saida Baban Junaidu ya siyo mata magani ta haɗiya ta gargasa jikinta tukunna ta iya bacci" Jikinta na taɓa yananan yayi zafi sosai. Hajara tashi muje in kai ki asibiti a duba lafiyarki, ina da aiki daga can wajen aiki zan wuce, bansan wa zai zauna dake a asibitin ba" Matarnan tace. "Baban Junaidu ya yarje mun akan duk inda zaki je da Hajara in biku, bari in sallami yara da abun karyawa sai mu tafi". Jiranta nayi ta kammala sallamar yara, taba Hajara taci amman ta kasa ci jikinta ma rawa yake yi shayin kaɗai nasa ta daure ta sha badan tana so ba. Fitowa muka yi riƙe da'ita Maman Junaidu na kiciniyar rufe ƙofarta, muka ji an ɗumo wata ashariya mai ƴaƴa da jikoki an ɗumama Hajara. Da sauri na juyo, ita kuma tayi saurin komawa bayana ta maƙale. Kallo na ƙare mishi daga shi sai gajeren wando da singileti, kanshi kuwa wani irin gashi mai dada ya tara wallahi har wuyanshi yadda kuka san bommali, wannan mawaƙin da yayi sharafi. Haƙiƙa iyayen Hajara sun yi kuskure mafi muni da suka ɗauki ɗiyarsu suka bata wannan miji, da irin wannan sufa tashi ta rashin daraja. Wai iyaye muna tunowa ƴaƴanmu nada hakki akanmu kuwa, ko mun mance kiwo ilahi ya bamu na yaranmu, akwai kuma ranar da zamu tsaya gaba gareshi ya tambayemu akan ababen kiwonnan daya bamu? Ko da yake kada in yi saurin yanke hukunci, ta yiyu Hajara ce ta liƙe ta kafe sai shi, iyayenta suka ja ta ja suka sake mata kamar dai yadda ya faru dani. Ta yiyu sun gaji da'ita burinsu su kaita ɗakin aure, ta yiyu kuma abun hannunshi suka bi da sauransu_da sauransu. "Ke dan abu ta kazan.... Daga ina a dangin Hajara bansan wacece ke ba da har kike yinƙurin fitarmun da mata" "Haba Figo wannan irin zagi haka ya'isa mana asibiti zamu kaita ba wani abun ba, baka ganin yadda idanunta ya tara jinine? " Cewar Maman Junaidu ni dai ina tsaye mamaki zai halakani, Allah mai iko ashe lalacewarmu har ta kai a ɗauki mace a ba Figo? "Babu to inda zaku je in dai ni nake aurenta. Zaki zo ki wuce ki girka mana abinda zamu ci ne ko saina tattakaki ne? " Matan gidan duk suka dena abinda suke yi suka rufu a kanmu suna kallon ikon mai saukar da ruwa da iska. Yinƙurowa yayi Hajara tayi saurin riƙeni tana kuka. Kai lafiyanka ƙalau kuwa a hakanne
Chapter 44 · 0% Book details