Sashe 69
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
To kun dai sani a makaranta Dr Mariya ma ake kirana, ina amsawa da karsashi cikin alfahari. A wannan lokacin a raina na saka ni likita nake son in aura tsabar soyayyata da aikin jinya. Ga yawan saka fararen kaya duk sabida gurina, ashe wannan guri bamai cika bane sam." Saurin katseta nayi na muskuta tare da cewa. A'a lokaci bai ƙure ba har yanzu Mariya Habibu. Ai ba'a tsufa da ilimi kuma in sha Allah in dai kina so, to burinki zai cika. Ke dai kici gaba muna saurarenki" Dariya tayi mun tare da cewa. "Hindu Duwaf iyayen son karatu na ƙwaƙwuduba kenan. Haka dai kike gani amman ƙwaƙwalwata a yashe take ita da fankon ashana babu maraba, ke naga rayuwa, rayuwa ta ganni fa. To a haka dai anata buga_buga ga iyaye ƙarfinsu ya ƙare har ta kai ta kawo mahaifinmu ya dena fita kasuwa, Babban wanmu ne ya maye gurbinshi a kasuwar. Haka aketa gurgurawa an gama karatu babu kuɗin ci gaba da karatu na gaba, kuma fa akwai yara da yawa da suke gama sakandare babu kudin wucewa Jami'a duk iliminsu haka za'aita zaune har ƙwaƙwalwar ta toshe, son karatun ya fice a ran mutum, shikenan duk iliminshi an salwantar mishi dashi. Talauci kenan bashi da daɗi sam, Allah dai yasa mu dace Ameen. Wata ranar asabar ina zaune wata ƙawata jarumace a masana'antar fina-finan hausa, tazo tace in karata wajen shirin film da kamar bazani ba dai sai na miƙe muka fita, saboda zaman gidan wallahi ya gama isata. A hanya muna cikin bus nake sanar mata nima ai da da hali da na shiga wannan masana'anta ta fina_finai, in ɗan dinga samun kuɗin da zan rufa ma kaina asiri, ai kuwa tace. "Shikenan Mariya in sha Allahu zanyi ma furodusanmu magana za'a ɗaukeki yadda kike masha Allah ɗinnan." Dake na fita kyau gaskiya, haka ko akayi rabon za'ayi, wallahi muna shiga wajen ga jarumai waɗanda na sani, dama waɗanda bansansu ba, ƴan bayan kemara kenan sai furodusan yace. "Ga ainihin wacce zata dace da Talatu nan gaskiya, kuma dama sabuwar fuska akeson amfani dashi. Ke a gida za'a barki kiyi film? " Gabana ya tattake ya tsinke, nama kasa magana sai kallona akeyi a wajen. Ba shiri ƙawata tayi carab tace. "Dama abinda ya kawota kenan shiga film, kuma babu matsala muna tare maƙotanmu ne." Wallahi dake ƙaddara bin me ita take yi tamkar inuwa, a ranar ita batai aiki ba dama sabon film ne nina ja shirin ita tazo a matsayin ƙawata, akayi film ɗinnan nice har a gaban Ali Nuhu ananne na gane sarki sarkine. Mutumne shi mai dattaku, natija, jan na ƙasa a jiki da ƙarfafa sababbin ƴan koyo, gashi da kwarjini sosai ya riƙe mutumcinshi irin riƙewar da baka isa ka kawo mishi wargi ba. Na koya daga Ali Nuhu sosai. To daga wannan film ƙaddarata ta soma aiki, Duk inda na ratsa laƙanina na cikin shirin ake ambata. A lokacin ɗaukakar daɗi wallahi. Har gida ake zuwa ganina, tsofaffin ƙawayena duk suka dawo, da samarina waɗanda muka rabu suma duk sai suka dawo hmmm. Ke Hindu a lokacin kina daf da yin Aure in ban mance ba mun haɗu daku a kasuwa, na rufe fuskata sai nice na kulaku kun tuna ke da Luba? Dariya Luba tayi tace. "Mu ko muka tuna jama'a aka taru a kanmu, wani mai shago fa da muka tsaya gaban shagonshi muka gaisa, bayan kin tafi wallahi da muka shiga saida yayi mana kyauta gwaggwaɓa, sabida dai mun sanki kuma ya tambayemu muka faɗa mishi tare mukai karatu fa" Dariya duk muka saka kafin taci gaba da cewa. "Haka na ɗaukaka naita fina_finai kuttun farin jinin al'umma ya fashemun. Kuskuren da mu muke yi ƴan wasan hausa, rashin tsari da hangen nesan me kaje kazo. Sabida a lokacin da mace take ganiyarta tana samun kuɗi tana da alfarma iri_iri madadin tayi amfani da alfarmarta ta yadda ta dace sai kiga bata yi ba. To garama na yanzu suna buɗe shago, sai dai abun takaicin kusan duk abu ɗaya suke saidawa shagon abaya, maganin mata, turaren wuta mafiya yawansu. Basa komawa makaranta suyi karatu mata_matan suyi amfani da alfarmar da suke da'ita su samu aiki, suyi ma al'umma hidima. Sai dai kiga basu wannan ƙasar, basu waccan ƙasar, mota, waya mai tsada, gidan haya mai tsada, siyan kayayyaki marasa alfanu tunda zaki ga wata bata da gida, bata da gwala gwalai amman duk sabuwar waya ko mota burinta ace a Kannywood ita ta soma hawa. Mu zamaninmu a lokacin da sauƙi, ba kuɗin da yawa amman akwai albarka, kuma ga girmama juna. Kannywood yanzu ai ta zama raka_raka amman akwai arziki cikinta. Amman Mariya Habibu masu wayo cikinsu irinsu Rahama sadau, Fati washa, maryam both, nafisa Abdullahi. A matan kenan kinga ai sunyi karatu a wasu ƙasashen ma ko?" Dafani tayi tace. Yauwa to ai basu da yawane, kinga shi yasa Rahama take burgeni sosai, yarinyar tana da masifar wayo kiga yadda ta ɗaga famili ɗinta, kuma Allah ya taimaketa ta samu uwa mai fahimta. Kinga ai tana riƙe da muƙamin da ilimine ya bata. Amman sauran fa? Wasu da ilimin nasu suka shigo, amman sai su ajjiye ilimin a gefe su saka film a gaba. Sai ciwo ya zubar dasu azo ana kafe hoto ana maula ai ba daidai bane. To haka nima ɗaukakata tazo na saima iyayena gida, Yayana na buɗe mishi shago a kasuwa, na cika mishi kaya muna raba riba, gani da ƴar motata kuma duk inda zan shiga ina da alfarma, wannan shine kaɗai daɗin ɗaukaka Alhamdullillahi har yanzu ina da wannan alfarmar duk da dai ƴan zamani basu wani sanmu ba abun ya jima. To a dawo ɓangaren mijin aure, sabida tsabar ruwan idanu da ƙyar na zaɓi wani Alhaji tare da iyalanshi suna Lagos. Mun yi soyayya kamar babu gobe, gaskiya ina son shi sosai, wallahi Aure sai ya gagara mahaifiyarshi, danginshi, suka ƙi fur abu mafi ciwo harda karuwa Mahaifiyarshi saida ta kirani. Ni kuma nace in shine Autan maza na haƙura dashi wallahi. Haka muka rabu. Na faɗa soyayya huɗu sai anzo batun aure da gabatarwa iyaye, sai su ƙi. Daga wannan lokacin na tsinke da lamarin harkar film, abun ya fita a kaina gashi ita harkar kamar shan taba ne dainawa yana wahala gaskiya. Shi yasa nake so a dinga ma matan film uzuri in anga basui aure ba, ko sun kasa zaman auren. Wallahi ba tulin maneman ba, mijin Auren. Ba Auren ba abinda ke cikin auren. Mufa munfi shanye baƙin cikin gidan Aure fiye da gama garin matan da basu da ɗaukaka domin me? Mu idanu na kanmu da mun fito sai ace dama bama zaman Aure sam, Ko kiji ana ai dama wance ce zata zauna a gidan Aure? Wance matar gwamna tafi ne, ko matar shugaban kasa tafi, ko matan sarakuna tafi ne da su sukai zaune a gidan Auren nasu? Wallahi rashin fahimta ce da yanke hukunci akan rayuwar mutum ta baɗini, tunda ai ba fitowa zaka yi duniya kace dole sai ka gamsar da jama'a ba. To a taƙaice wancan Alhajin nawa wanda mahaifiyarshi ta hana auren shine ya dawo, bayan mahaifiyarshi ta rasu. Ni kuma a lokacin Mamanmu an gama zigata akan in yi Aure ai ƴan film basa aure, kuma ta yadda wallahi ko gaisuwata bata amsawa ga Abbanmu Allah yayi mishi rasuwa. Ai yana zuwa nace to ya turo tunda mun riga mun fahimci juna, ai kuwa cikin sati guda aka saka biki, amman na zaɓi yin bikin da ba sai an yi sharholiya ko bikin da za'a kama hall ba, sai akayi biki a gida ƴan film sun mun rana su suka cika gidan bikannan waje ma haka maza duk mune ƴan film, su suka kaini ɗakin aurena, suka durƙusar dani a gaban kishiyata sukai mana nasiha mai kyau. Buɗar. Bakin kanwar kishiyata sai ca tayi. "Asabe dama ƴan film suna da tarbiyyar da zasu zaunar damu wai nasiha suke yi mana ƴan film fa?" Buɗar bakin margayya bazan ambaci sunanta ba, sananniyar mata mai mutumci tace. "Suna da wannan tarbiyya sabida suma ƴaƴane kamar kowa, ba bishiya aka girgiza suka zubo ba. Mariya ke dai kiji duk abinda muka ce miki ku taso muje mu kaita ɗakinta" Sabida kara da irin haɗin kai na Kannywood a wannan lokacin wallahi dangina ƴan kallo suka zama kawai, sun ƙwace biki tas sai dai san barka. An yi biki an watse ashe ƙaddarata anan zata soma ya Allah. Ta ɓangaren miji a lokacin gishiri na kan kaza, shi bani da matsala dashi sam sai da kishiya. Wautar da nayi shine saina ɗauki matsalar Asabe ba'a bakin komai ba, duk abinda tayi in shanye, duk sharrin da tayi in bata haƙuri, mafi girman kuskuren da hatta yanzu inajin zafi inna tuno kenan. Tafiya tana ta tafiya a haka anata gurgurawa da daɗi babu daɗi dai. Ta ɓangaren dangin miji basa sakani a lissafi basa mun kallon mutum zance, ne ko me oho. Sai dai ina zaune Asabe tayi mun sallama ta tafi bikin dangin miji dake danginshi da yawansu suna Legas musamman ta Agege, da idiraba, da obalande dai haka. Ita Asabe tana jin daɗi dangin miji da'ita suke yi, kunga ai ba zata faɗamun ba. Shi miji yana tunanin an faɗamun girman kai na ɗaurama kaina shi yasa nake ƙyamatar shiga danginshi, sabida ni ƴar film ce dai. Wannan labarin banfa sanshi da wuri ba har sai da bikin ƴar ƙanwar mahaifiyarshi ya tas, to ita a Taraba suke a cikin jalingo, wannan dai na tsinci zancan bikin a bakin wata maƙwabciyata wacce jininmu yazo ɗaya da'ita, mutuniyar Argungun ce masu kifi. To da naji banyi ƙasa a guiwa ba sai da kwana ya zagayo kaina saina tambayeshi, domin inji daga gareshi. Ashe ni daga ranar matsalata zata soma da miji. Nayi muku tsallake Asabe wata iriyar macece maras lissafi, muguwa wacce ta iya takura mutum. Akwai wani film nawa da wata waƙa ni nahau waƙar bazan faɗi sunan mawaƙiyar ba dan kar ku canko wacece ni. To wannan waƙar kullum itace abun wasan Asabe da fina finai na. Ina zaune zan dinga jiyota da maƙota suna tsinewa, da aibata ƴan film ƙage da sharri babu irin