Sashe 32
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
rayuwarshi ba, ta Amarya kawai yake ya mance yana da uwar ƴaƴa ni Lubabatu dana Aureshi baida ko biyar yake yi. A yanzu da nake yi muku maganarnan rayuwa nake yi sunan ina da miji ko rabon kwana ba'ayi dani. Ni dama bai dameni ba, amman a ƙalla a kwana a ɗakin naka ko da a falo namiji zai kwana gobe ya fice, a ƙalla ya siya ma ɗan mutumci. Amaryar ta haihu ta haifi ƴan biyu dukka maza. Hankalinshi ya sake karkata ya koma kanta. Wallahi da Sunusi ake zaman barka ƙaƙas, yana cikin mata ai ni naga abinda yafi zare tsayi" Dariya nayi har ina ƙwarewa, suma su Saudatu Mustapha dariyar suke yi. (inaso ku nutsu sosai, kuyi karatun nazari, ku fito mu tattauna sosai. Wannan haɗuwar bawai hira da cin abinci bane kawai ba. Hirar bawai hira bace wacce zata wuce a hira kawai ba. Mu buɗe zukatanmu mu yi karatun da kyau) Sumayya tace. "Ikon Allah Luba lallai ko wacce aka ganta cikin sutura ba'asan abinda ta fuskanta ba kafin a ganta cikin suturar ba. Kowa ka taɓa yana da abun faɗe. To ta nawa ɓangaren labarin. Ni da Auwalu a tsangayar Aminu Kano muka haɗu shi yana fafutukar haɗa mastas, ni kuma ina ta damben kammala digirin farko, ina karatun likitanci. Gashi gida an matsamun in fidda mijin aure. Sun gaji da zaman karatu da nake yi a gidan ɗalibai hostel dan gaskiya Babanmu ya fiso ka zauna a gidan ɗalibai ka nutsu kayi karatu, duk ƙarshen sati sai ka koma gida. Dangi sun damu Mamana da surutu akan so suke su maidani ƴar boko inzo ince ni nafi ƙarfin maza su basu yadda ba. Sabida nayi jinkirin soma jama'a gaskiya, ban shiga da wuri ba. To dama ina soma karatu, sai aka matsama Mama lamba, ita kuma sai ta ɗauramun firejar duka a kaina, inna dawo hutun ƙarshen mako. Ina cikin wannan firejar muka haɗu da Auwalu, hmmm lokacin an turani asibitin koyarwa na malam aminu Kano domin in yi aiki dasu, to shima ashe a cikin irin wannan firejar tawa yake a gida, dan ba yaro bane gaskiya, iyayenshi suna Bauchi karatune ya kawoshi Kano yana zaune gidan Kawunshi ƙanin mahaifiyarshi, kuma da aikinshi a hannunshi karatun yake son ƙarawa sabida samun ƙarin girma dai da sha'awar karatun ma. Irin wannan matsin lambar da iyaye ke ma yaransu yake sawa mace ta zaɓi mijin da ba daidai da rayuwarta bane ma'ana tayi zaɓin tumin dare. Kazalika namijin na iya zaɓar macen da ba tai daidai dashi ba kuma ya sani, amman sabida gudun kar wa'adin da aka ɗibar mishi ya cika a gida sai ya zaɓi wacce duk tazo mishi, domin kar ace za'a bashi ko wacce irice a dangi. Abinda ya faru dani kenan a zaman hira biyu kacal na fahimci Auwalu ba irin ra'ayinmu ɗaya ba, kuma na gane wani irin bauɗaɗɗen mutum ne mai saurin fishi, da tsattsauran ra'ayi, rashin fara'a, da rashin nuna damuwarshi a kaina. Amman tabbas a baki in muka haɗu yana furta mun yana sona. baya gajiyawa, amman fa a iyakar fatar bakinshi ne a aikace babu wannan son kwata kwata. A hakan na gabatar dashi a gidanmu na kaishi har gida ya gana da iyayena, aka tsayar da maganar Aurenmu akan dana kammala karatun sai ayi bikinmu. Kuskurena na farko kenan dana tabbatar na aikata. Hmmm tafe_tafe na kammala karatuna asibitin malam Aminu Kano suka riƙeni a matsayin gama garin likita wacce a yaren nasara ake kiranmu da General practitioner (Gp) Sai mukai aure da Auwalu duk da halin rashin damuwa dani da yake nunawa, ni kuma dake aiki ya sha mun kaina sai bana damuwa sam. A hakan mukai Aure ya ɗaukeni mukai Bauchi yuu dole na bar aikina amman dai mahaifiyarshi ta nema mun aiki a babban asibitin Bauchi naci gaba da aikina da daɗi babu daɗi, inata turawa Auwalu kuma ya ɗan canja babu laifi yana ɗan iya kirana a waya haka sau ɗaya a rana, shi soyayyarshi bata motsawa sai yana son ya kwanta dani kaɗai, da zaran ya gama, aikina yake ƙarewa kallo ban isheshi ba, wallahi. Sai kiga ya sauya tamkar ba shi bane wannan na kan gadon ba. Ina goyon yarona na farko ya samu aiki a Kano babba da yafi nashi na Bauchin, muka ɗungumo muka dawo naci gaba da aiki da Malam Aminu Kano a matsayina na gama garin likita. Lokacin dana samu cikin yarinyata Fati a lokacin komai ya cukurkuɗemun ni da Auwalu, babu zaman lafiya ko kaɗan kullum cikin fishi da ƙunci yake, mu zauna mu fahimci junanmu, ya hanani wannan damar ga aikina baya bamu ishasshen lokacin daya dace, a lokacin harya soma ƙorafi akan aikin ya isheshi shi kam in ajjiye. To kunga ai anzo wajen ko? " Kai na jijjiga nace An zo wajen tabbas ki bar aiki a matsayin wacce tayi rantsuwa zata kare rayukan al'umma, Auwalu yazo da abinda zai kawo haɓakar rashin zaman lafiya a aurenku. Ina mamakin mazan da zasu auri mace tana aiki, ko tana Jami'a, yazo ya ce a dena aiki, ko ta gama karatu yace, ba zaki yi aiki ba. To wai tun farko bai ga ƴar sakandare itace ta dace dashi bane wai? Sumayya tayi murmushi tace. "Sak kuwa abinda yake so kenan dan daga haka ya tsiri gaba dani Hindu. Sai ayi wata baice mun komai ba. Duk ranar da yake buƙatata zai neme ni, ni kuma ban taɓa hanashi kaina ba. Ke sai yai wata biyu, fin haka ma, in kinga yayi magana dani to zai amfana da albarkar da Ubangiji ya halittoni dashi, kinga fa kenan a fakaice, ya maidani injin ɗin walwala da fulejonshi kenan fa, daga haka sai in yi ƙyanƙyasa, iyakar kwantiragin daya auroni in yi kenan fa. Wannan rikicin sai da ya ɗaukemu shekara biyu. A lokacin duk na rame na lalace Hindu, duk wanda ya kalleni saiya tambayeni ciwon me nake yi. Ana haka ya samu aiki a Abuja aikin daya canja mu daga tsaka_ tsaki zuwa mataki na sama_sama, aikin daya ɗaga darajar Auwalu wanda ya samu ta dalilin mijin ƙawata kuma ni naima ƙawar tawa magana kamar wasa aka ɗauki Auwalu, lokacin yarana uku na kuma yanke na gama harna ɗaura robar tsarin iyali. Bazan iyaba, itama ta ukun Allah yayi zata taka doron duniyane wallahi. A lokacin dana sama mishi aikin yana tsaka da gaba dani. Rayuwa tayi kyau, taci gaba da tafiya damu. Nima ina aikina a wani asibiti mai zaman kanshi ana biyana da kyau. Zaman namu dai kadaran kadahan, ga tarin dukiya amman ni da Auwalu har lokacin bamu fahimci junanmu ba, bansan me yake ciki ba, baisan me nake ciki ba ,muna rayuwa a gida ɗaya a matsayin miji da mata. Bayan shekaru sai ya sake tsuro da wannan fishi na rashin dalili a tunaninshi zai gasani. Sai naƙi gasuwa sabida na riga da na ƙuna a lokacin ko gezau bana ji, zuchiyata ta bushe ta kangare. Madadin ma damuwar abun ta dameni saina koma karatu naje na haɗa mastas ɗina a Jami'ar Abuja, ga aikina ga yarana da suke ɗebemun kewata. Ranar laraba na dawo da safe kasancewar aikin dare nayi Auwalu da yara sun gama shiri zasu tafi ya ajjiyesu a makaranta. Sai cewa yayi. "Sumayya inaso zamu yi magana dake, inata son muyi maganar amman duk sanda zaki dawo a gajiye kike dawowa, ga lokaci yanata ja. Gara muyi maganar tunda lokacin da zan dawo ke kuma lokacin kike shirin zaki koma ƙaddararren aikin da yafi miki kula da yaranki da mai gidanki" A gaban fa yara. Sai Ahmad ya saka ƙannenshi gaba suka fita, a lokacin sun girma shekara biyar yanzu da yin hakan, Ahmad yana Jami'a yanzu haka. Ai naji abinda yace, kuma ni nasan ban rageshi ba, ina yaga lokacin nawa ma. Zama nayi kamar yadda ya umarceni, banyi raddi akan abinda yace game da aiki ba. "Aure nake so in yi dama shine nake ta son in faɗa miki. Sabida tunda mukai aure haƙuri nake yi dake ta wajen mu'amalar aure gaskiya, in kin lura shi yasa sai in yi sati, wata ɗaya, wata biyu, har uku, ban nemeki ba. Ba dan bana so bane ko bani da lafiya bane. A'a sai dan rashin gamsuwa da bana yi ne kawai, baki da ɗanɗano sam, kuma ni bama na dai ganewa dai. Sannan baki da lokaci kullum a gajiye kike, ga yawan amsa waya da yawan bama marasa lafiya lokacinki. Sai dai bawai bana sonki bane in zaki gyara ta yadda zan dinga gamsuwa shikenan. Sannan in ki ajjiye aikinki sai in fasa auren. Ki zauna kiyi nazari na kwana uku zai kama ranar sati da muke gida sai mu zauna mu tattauna" Zazzaro idanu waje muka yi dukkanmu ita kuma Sumayya idanunta suka cika tab da ruwan hawayen baƙin cikin fama miki mai raɗaɗin zafi dake ƙasan zuchiya. Sabida jarumta murmusawa kawai take. Wato abinda na lura kamar yadda aka tsara zuchiyar namiji da faɗin da zata iya ɗaukar soyayyar mace huɗu, kuma ko wacce a muhallinta. Haka Allah ya tsara zuchiyar mace da faɗin shanye damuwoyi da matsala harma da jimiri. Sai dai wannan haƙurin da yawan shiru da mata suke yi su bar magana a ciki, shi ke faɗa musu ya wanzar musu hawan jini, ciwon zuchiya, da buguwar zuchiya mai shanye ɓarin jiki, ku harda ma rasa rayuwar baki ɗaya. In ba mace mai taurin zuchiya aka samu ba. Yanzu dai ku jibi furucin Auwalu tamkar yaci kashi dan Allah, ko da yake mata zasu ce, ai maza sunfi haka na Sumayya kaɗanne. Harma su buga misalinsu da matan da akai musu fiye da hakan. To ni tambayata anan shine, tunda anayi, dole ayi shiru, ko kuma dole yadda wance tayi, wance ma dole haka zata yi? Ni kam aban amsata ni Hindu a kwament sekshon. Nisawa nayi kawai Luba ce ta samu zarafin cewa wani abu da murya mai ɗauke da amon tausayi, gami da ɗaura kai a matsayin da mai labari ya ke kai. "Yaya kika ji a lokacin dan Allah Sumayya. Ace Namiji ya kalli tsabaragen idon matarshi bayan shekaru da aure yace bai taɓa jin daɗinta ba, shi yasa ma bai fiye nemanta ba?