← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 85

Sashe 37

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

kun dawo yadda kuke da. Ni na samu haka Duwaf? Nifa Sanusi baima san abinda yayi mun laifi bane bare har yayi tunanin yin karatun ta nutsu. Sabon iskancin daya buɗe na faɗa miki wallahi dashi ake zaman bakwai duk matannan da suke zuwa da maƙota, masu shigowa Sanusi yana tsakiyar mata da yara a ƙwaƙwube a hannunshi, yadda kika san sune yaranshi na fari fa" Hmmm kawai na iya ce mata a wannan karon. Zuchiya kowa da irin wadda Allah ya dasa mishi sunanta dai kawai iri guda. Ni kuma ina ganin girman laifin Sanusi bai kai kwatan na mijinyawa ba, amman dake Luba bata san irin wainar da Mijinyawa da Asama'u sukaita toyawa kafin su yi auren bane shi yasa take mai uziri. Kuma take ganin wai ya sauke kanshine ya biyoni, kuma wai sabida ni ya rabu da Asama'u. Wallahi bai rabu da'ita sabida ni Hindu ba, ai bani na haɗasu ba. Auren ba laifi bane duk abinda sharia ta kawoshi ta yadda dashi baya zama laifi. Amman ashe bani da daraja da kimar da mijinyawa zai iya kawar da kanshi akan Asama'u, ya auro yarinya daidai dashi wacce zata zo mu rayu cikin farin ciki ta haifa musu yaran da suke so? Hmmmm taya wai zamu sasanta da mijinyawa ne. Masu cewa in yafe mishi, to na yafe mishi na sake na yafe mishi, na sake na yafe mishi, amman zaman aurene babu mahalukin daya isa yasa in zauna dashi. A haka muka gama aikinmu muka taso ƙarfe ukun yamma. Kai tsaye gidan makokin Jamila muka je ni da Luba ta hanyar kwatancen da mahaifiyarta tayi mana. Ƴan tambayoyi nayi mata ta bani amsa sabida akwai binciken da nake son yi in Allah ya dafa mun sai mijin Jamila yazo hannu da izinin Allah. Zan ta bibiya, ga lambar waya ma na samu, duk da bata shiga, babu mamaki ma ya cillar da layin wayar. Daga nan muka wuce asibiti wajen Maman khadija itama jikin nata da sauƙi, sati mai zuwa zamu soma zaman kotu da izinin Allah. Ƙarfe shida daidai muka shiga gida ni da Luba, Mijinyawa baya nan motarshi bata ƙofar gidan ma hakan yasa muka barbaje a falo tare da Sabira, Azgar dai bayanan ya shiga gari dubiyar abokinshi da suka yi hatsari. Saida Luba tayi magriba taci tuwo kana ta tafi gida. Ina zaune ina cin tuwo ina duba saƙwannin mata tare da nazarin matsalolinsu idanuna na lumshe kaina na wani irin turirin zafi, haƙiƙa mata a wannan zamanin muna cikin damuwa da matsaloli da dama. Sannan da daman matan da suke shiga irin matsala mai girma ko samun matsalolin cin zarafi da tozarci. Basa sana'a, basa aiki, basu iya juya taro ya koma sisiba, da mazajen suka dogara kawai. Ga ba safot na iyaye da dangi. Mata a wannan zamanin fa ya zame mana dole mu yi aiki, ko sana'a a cikin gida, domin kare mutumci da darajar kanmu. A halin da ake ciki ko iyaye sunfi ji da yaransu masu ƙumbar susa, ƙiri _ƙiri a ɗakinku zaki zama saniyar ware in bakya sana'a ko aiki, wani abunma sai ya faru amman ke ba'a fada miki ba sabida babu abinda zaki iyayi. Zauren gidane yake ta ɗaukar hankalina irin yadda aketa saƙwanni sai zuwa lokacin na tuno da wayar da muka yi da Innarmu. Ai babu shiri na shiga zauren na gane ma idanuna me nace daya tayar da tarzoma haka. Wai ashe da nace ga ango nan a gaban amarya abunshi. Shine abun baƙin ciki. Khadijan Innah Mairamu itace ta soma kwamen akai akan. "Me kike nufi da wannan kalmar Duwaf ya hausar ga ango a gaban Amarya abunshi?" Ai tana faɗa sai aka soma taɓa maganata, ana mayar mun da raddi akan me yasa zance haka. Yaya Saratu ce tace. "Ni banga wani abu a kalmar da Hindu tace ba. Shin ba a gabanta yake ba daman? " Khadijan Innah mairamu sai cewa tayi. "Kamar baƙin ciki take yi da hakan, dama ku kun saba ƴan ɗakinku sunfi so ace komai sune akan gaba." Sai Salamatu tayi saƙo mai murya na kusan minti ashirin. "Dole kice haka Saratu tunda dama ku ƴan ɗakinku bakwa laifi. Sai ku faɗama mutum baƙar magana ku nuna akan daidai kuke. Tun ranar da aka kawo akwatunana kuke nuna baƙin ciki da hakan, sabida a tarihin gidanmu babu wata mace data taɓa samun irin kayan dana samu. Hindu tasan nafi ƙarfinta da ɗan ƙauyan mijinta wawa. Sannan da take cewa ga ango a gaban amarya abunshi ita da take gajera kamar a kifeta da kwando ita ba ƴar tsurut take a gaban mijinta ba, abunma babu tsari. Me ta fini dashi, gajerar mace, sannan me Mijinta yafi nawa dashi faɗin ƙirji da jikin samudawa ko? . Ku dama taƙamarku Innarku itace mace wacce tayi boko a iyayenmu, sai kuka ɗauki wani irin girman kai kuka ɗaura ma kanku. Shi kuma Baba Sojanmu yana jin tsoronta, yafi ji da'ita ƴar boko hakan ya baku dama kuke ta tsula tsiyarku" Ta dai inda dai ta shiga ba tanan take fita ba. Tai ta zazzagar ƴan ɗakinmu. Ai kuwa ta sha baƙaƙen maganganu a wajen Yaya Zubaina, zafafan saƙon murya saida ta jero uku masu zafi duk saida na saurara. Ta ciccire mata aiki, ta zagesu tatatas. Ɗakina na koma,naci gaba da sauraren abubuwa. Ƴan ɗakin Innah Mairamu suke ƙara tura abun, su da ƴan lungun Baba Lukumanu. Ƴan lungun Baba Alƙali kuma suna karemu. An yi abubuwa sosai har takai da zage_zagen juna a tsakanin Yaya Saratu da Salamatu tunda ita Salamatu kai tsaye da Innarmu take yi, duk haushinta a kanta yake tana mugun taya Innah Abida kishi da Innarmu. Innarmu kuma taci dubu sai ceto zaren wallahi ba kalan yadin bane. Ni da abun ma ya gundureni, saina fita a zauren na koma Facebook na yi rubuce_rubuce akan mata su tashi tsaye wajen sana'a ko aiki, inda hali a haɗa duka biyun. Na buga musu misalai masu yawa akan matan da suke tsaye da ƙafafunsu ba'a iya kafaɗar miji suka jingina ba, suma kafaɗune ababen jinginar wasu. Na kuma buga musu misali da macen da bata aiki, bata sana'a, da ƙafafun miji take tsaye komai sai ta jira anyi mata bata da ikon siyan komai ko canja komai sai abinda ta gani. Gashi yanzu a zamaninnan ba dukkan mazan ke sauke ratayayyen hakkin kulawa da mata da yara ba. Sai dai ɗabbaka sunnar ƙarin aure kaɗai da yawa suka iya. Iyaye basa son a dawo musu da ƙorafi, to me ya kamata mata suyi? A nemi ilimi arabi, da boko, ayi aiki, ayi sana'a. Na nuna musu muhimmancin sana'ar mace da darajar da take yi a cikin dangin miji, nata dangin, dama shi kanshi mijin. Na kuma buga musu misali da Nana Khadija da irin gudummawar da ta baima addinin musulinci da dukiyarta da lokacinta. Addinin musulunci bai barmu sasakai ba. Babu a inda akace kar mace tayi aiki ko sana'a matsawar zata kare kima da mutumcin kanta. Bari mu ja nunfashi anan sai kuma gobe in Allah ya kai. Mrs Bukhari
Chapter 37 · 0% Book details