← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 85

Sashe 18

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da na dafata tayi saurin juyowa. Badia kaddai nadama kike yi na kulle Baballe da akayi? Bari kiji Badia tun wuri ki sanar dani abinda ke ranki kada kisa inji kunya, in gama haƙilon tsaya miki daga ƙarshe ki ɗebi ƙasa ki tula mun" "Wallahi Malama nadamar auren Baballe kawai nake yi. Bana dana sanin shigowarki rayuwata domin ki taimaka mun. Malama babu ranar da zata fito ta faɗi Baballe bai kutuntumama iyayena ashariya ba. Abu mafi ciwo a gaban yarana mata sai ya tsinkeni da mari" Mari Badia da yaranki goma miji ya mareki ke kuma kina zaune baza ki haƙura da auren ki nemi rayuwar da tafi ta gidanshi ba? Wai ina zamu kai son miji ni Hindu, anya matan wannan ƙarnin da muke ciki ba cutar son rijalu bace ta kamasu ba kuwa?.... Muje inga ɗakin naki mu gaisa da yara, ga magriba tayi sai muyi sallah sai in tafi." Tare muka shiga yaran suna tsakar gida ƴar babbar tana bakin murhu tana tuƙa tuwo ga miyar a rufe a gefe a ƙaramar tukunya. "Mama sannu da dawowa ina wuni? " Suka gaggaisheni na amsa da fara'ata ina ƙarema gidan kallo, da yaran gidan hmmm. Babbane sosai gidan yana da filin tsakar gida sosai, ga ɗakin Badia can gefe ga kuma tamfatsetsen ginin Amarya. Jana tayi muka soma zuwa ɓarayin Amaryar duk da a rufe cikin yake an yi jere. Yasha fenti har tsakar gidanta yayi mata. "Kinga harda tsakar gida ya yanka mata, ga bayan gida a ɗaki gana baƙi a tsakar gidanta. Ni da yara goma da banɗaki ɗaya muke amfani, wani sa'in wata na ciki wata ta matsu haka dai muke rarrafawa, muke gurgura rayuwar." Allah ya kyauta amman wannan ginin Baballe ya kashe kuɗi Badia, nace dama yana da kuɗine? " "To yana noma, noman shinkafa, da dawa, kuma abun ya karɓeshi yana ajjiye hatsi sosai kawai dai nice ba zaima ba har gidan gona gareshi ya zuba kaji sama da dubu akace shima a bakin ƴan uwanshi nake ji. Wallahi Allah bansan da wannan gidan gona ba. Dan ni ranar da naji a zaune na kwana ban bacci ba" Kina me?" "Inata tubkewa da warwarewa, gami da mamakin Baballe" Murmushi nayi kawai. Hannunta na jawo muka fito, muna tafe tana labarta mun har muka shiga ɗakinta. Manyan ɗakunane ciki da falo fulastar ɗakin duk ta farfashe ko leda babu a ɗakin fenti ma dan masifa harya sude ba'a iya gane wanne kalar ne, ga jinin kuɗin cizo ko ta ko ina tamkar ɗakin Shanno ta Kaila zance, ko ta Jega. Uwar ɗakin babu komai sai katifa da jakunkunan kaya masu yawa, rai goma sha ɗaya ba wasa ba. Tsummokarai tako ta ina saman ƙofarta shaƙe fal da kaya. A haka na ɗauro alwala ta shinfiɗamun zani nayi sallah, ko sallaya bata dashi, aka zubo mun tuwo na daure dai nayi loma uku. Badia a irin ɗakin da kishiya zata shigo ta sameki kenan abinda Baballe yake nufi kenan?. Kuma sabida wauta irin taki batun miliyan ɗayanki kince kin yafe, me yasa ba zaki ƙwarara kanki ayi mai gabaki ɗaya a wuce wajen bane. Ko akwai abinda kike tsorone?" "To ya za'ayi sai haƙuri kinga dai rayuwa. Abinda yasa na ce na yafe mishi shine. Akan wannan kuɗin Baballe zai mun sakin wulaƙanci, yarana goma ace ina riƙe dasu babu Aure, a irin al'ummar da muke ciki zai zame mun babban ƙalubale. Yaran kansu sai aure ya gagaresu za'ace yaran macene. Gani da siriki ina tsoron abinda zai taɓa rayuwar aurenta." Hmm nagane, kuma nagani Badia, zanyi ƙoƙari in sha Allah ayi miki filasta da fenti gobe masu aiki zasu zo, masu fulasta kenan su soma aikinsu. In ya baki kuɗin kayanki sai a sai masu sauƙi ragowar a rage ayi jari babu komai " Kuka ta fashe dashi kawai na shiga tausa. Daf isha na bar gidan Badia takwas da rabi na sha kwanar gida mijinyawa na tsaye ya saka hannu a ajjihu da alama tunani yake yi tunda haka ya saba, aikin banza. Get ya buɗemun na shiga. Kafin ya gama rufewa na shige gida a guje cikina ya murɗa yara na mun sannu hannu kawai na ɗaga musu na wuce a guje. Ina zama a sita sai gudawa, ba sai amai ba kuma. Wallahi kamar wasa nayi amai har bana iya tashi, mijinyawane ya shigo ina kwance cikin amai ya shigo ganin ƙofa a buɗe yasan babu lafiya. Kada ka taɓani bana son taimakon ka, ka fice mun" Nayi saurin katseshi daga shirin ɗagani da yake yi. "Haba Tutar so yama zan barki haka a cikin amai?" Daddagewa nayi na miƙe duk da saida ya riƙeni da yaga jiri na ɗibata. Fisgewa nake son yi na kasa. Da ƙarfi na fisge hannuna na tureshi, ina haki, idanuna sai rufewa naji suna yi. Kaje zanyiwanka ka fitarmun nace ma, wallahi in ba haka ba zan iya raunataka a banza. "Mai taurin kai kawai, ya ma za'ayi in barki haka" Zaunawa nayi a saman sita. Shi kuma ya goge aman tas kafin ya fita ya barni. Rarrafawa nayi na shiga wajen wankan na watsa ruwa a jikina sai naji dama_ dama saida na huta sosai na fito ɗaure da tawul ina tafiya a hankali. Har wannan lokacin ina jin cikina na haɗa shirgi, ga tashin zuchiya. Abinci na tadda mijinyawa na jeramun a kan teburi harda ruwan wanke hannu. Ƙuramun idanu yayi kamar ya cinyeni dan sha'awa har ajjiyar zuchiya yake saukewa a kakkatse maza a barsu kawai. Shi da yake da matan bariki meye na ajjiyar zuchiya dan yaga bagidajiyar mace. Kaina na kawar ba tare da nace uffan ba nayi saurin zura doguwar rigata, kana na zare tawul ɗin ta ƙasa. "Zo ki zauna ki samu ki saka wani abun a cikin ki. Ga magani na kawo miki kisha" Bance komai, kallon dana watsa mai yasa wallahi ba shiri ya saka kai ya fita kawai, harda haɗawa da sauri, tsaki naja na yane kaina da mayafi na ta da kabbarar sallah. Ina idarwa yaran suka bubbuga naje na buɗe musu sukai mun sannu da jikin. Azgar wa yayi girkinnan? " "Nine Ammi duk da bansan ko shi kike so ayi ba. Nayi ta kiran wayarki babu amsa." Yayi ba kullum mutum ke samun abinda yake so ba. Zanci abinci in kwanta sai mun haɗu kuma gobe. Ina da magana da kai zuwa gobe" Nayi sallama dasu na rufe ɗakina. Ina cin abincin amman hankalina, tunanina yana ga ɗakin Badia da irin abincinsu wanda babu tsabta a ciki gashi naci yana neman halakani. Naci ne kawai sabida in ƙarfafata, amman wallahi nasan za'ayi haka. Ni ko abincine a ido bai mun ba, in dai naci saiya dawo gaskiya. Zuchiyata tace. To namiji na neman halakata ya cinyeta da ciwon hawan jini, ta faɗi ta mutu ƴaƴanta sune da asara. Wata zuchiyar tace. To su yaran a tantagaryar ƙasa kenan suke kwana babu ko tabarma ko yaya, katifa ɗaya ce a ɗakin ai? " Iska na fuszar daga bakina kawai. Na lumshe idanuna ina jin zafi da raɗaɗin halin da mata suke tsintar kawukansu, a gidajen aurensu. Rayuwar mata abar a tausaya ce. Da mafarke_mafarken Badia na tashi dashi na wuni a wajen aiki dashi, na labartama Luba ma tace zata bini ofishin ƴan sandan taga Baballe muna hanyane wata itama ta kirani tana son ganina a yau ɗinnan tana cikin matsala. Adireshina na tura mata itama ɗalibar cikin zaurena na kan manhajar WhatsApp ce, kuma tana taimakawa wajen bama mata shawari na hankali. Banso bata adireshin nawa ba, amman bazan iya zuwa inda take ba, kuma wajen aikina bazai yiwu in ce zan maidashi wajen jin koken mata ba, akwai dai yiyuwar in samu ofishi nawa na musamman. "Hindu inaga ki buɗe ƙungiya kiyi rijista kawai kamar shawarar da a baya mijinyawa ya taɓa baki, sai ki kama ofishi kawai ki dinga jin koken mata. Amman gayyatarsu gida ba mafita bane, yadda rayuwarnan ta kasance" Kallonta nayi tare da yin guntun murmushi nace. Shi kuma aikin nawa zaki karɓa mun Luba? A yanzun ma yaya na cika ishasshen bacci ba samu nake yi ba. Ga yarana ranar hutu kaɗai suke samun lokacina. Amman gaba zan kafa ƙungiyar da matan arewa zasu yi alhafari da samuwarta. Jibi Fauziyya d Sulaiman irin ƙoƙarinta da tallafama gajiyayyu da take yi. Matar jarumace sosai. Zan samu buɗe ofishi Luba, amman sai nabi matakan duk daya dace, gudun take doka" Luba tace. "Ga Umma Sulaiman ƴan awaki Anty Baby tana ƙoƙari har gida suke ginama marayu da marasa ƙarfi, ko su gina rijiyoyin burtsatsai. Harkar taimako akwai daɗi kuma itama kinga tana wani shiri mai suna sirrin mata a Aminci rediyo tare da mataimakiyarta Hajiya Badia. Amman ita kinga aikinta sau ɗayane a sati kawai. Ba kamar mu masu aikin kullum ba. Aikin ɗakko rahoto ba ma aikin ragwaye bane, ga haɗarin dake cikinshi. Jiya ina kallon aljazira wallahi gobarace akayi a wata ma'aikata, masu ɗaukar rahoto daga wajaje daban_daban ƙasa ta rufto musu a kansu, wallahi sun rasa rayuwarsu, ta dalilin ɗakko rahoto" Har muka isa gidan Badia muna hira. Ma'aikatan dana turo har sun gama fulastar ciki da falon tun safe. Tace ma a maƙota zasu kwana zuwa gobe ya bushe sai a yi mata fenti. Sai godiya take yi tana shi mun albarka. Ko da muka isa ofishin ƴan sanda mun tadda Baballe an fito dashi wani abokinshi yazo zai biya kuɗin sai gamu abun yazo a daidai. Duk da abokin yayi ƙoƙarin tanƙwara Badia akan ta rage yawan kuɗin ta duba darajar ƴaƴa kunsan maza wajen son kansu babu damane, to Allah kuwa me yasa shi Baballe bai duba darajar Ƴaƴa ya martabata ba uwar ƴaƴanshi goma fa, yara goma ai sunfi ƙarfin wasa. Ni na zame mata baki sabida na fahimci tana tsoron Baballe, sai harararta yake yi yana ƙuta. Haka dai da suka gama surutansu wannan abokin nashi ya ciro kuɗi a leda cib kuɗinta ya miƙama kofur ya ƙirge kuɗi tas. "Hajiya kuɗi sun cika cib" To Alhamdulillahi mun gode Kofur Allah ya saka da alkhairi. Yanzu kam za'a iya ba da belinshi mun gama da wannan amman bamu san ko zamu sake dawowa akan sabon kes ba,
Chapter 18 · 0% Book details