Sashe 60
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
hawa natane, ba nawa bane. Kuma har Nanno na faɗama yaddane dai basu yi ba. Ko na mutu yau wannan gidan ba nawa bane'" "Dis is siriyos, u a de ona ob is wandaful, biyutiful haus, fantasti,. To kun ma ji, laifin ya ƙaru akan wanda suka aikata a baya." Tsawa Kawu ya kuma dokama Zakiya akan ta ba da haƙuri. Baki na rawa, a bisa dole duk suka bimu da haƙuri Baba Sojanmu ya ruɗa musu cikinsu. Mijinyawa Babba ma ya ba da haƙuri bisa dole, wallahi kallo basu isheni ba. Yau Innarmu sarautar take ji, sarakaine a kanta yau, taƙi cewa uffan. Kawu yai ta haɗa Baba Sojanmu da Allah akan abar maganar ta mutu a haka. Mijinyawa ma yaita bin baki, haƙuri kawai suke ta bayarwa dai. "Kagane ni zanso aje Ofishin ƴan sanda a saka hannun da wajewa, duk abinda zaije ya dawo ya biyo baya sune silarshi. Ni ina ganin hakan zaifi abi doka a zauna lafiya." "A_a Soja maganarnan a batta hakanan, a rufeta Allah ne ya haɗamu a waje guda da muna so da bama so baga mu a zaune ana tattauna matsala ba. Ka daure a duba, nama alƙawarin babu abinda zai kuma faruwa, ba zasu sake zuwa ba ma" "Well naji, amman ka sani, tabbas suka sake zuwa mata gida, ko ciwon kai tayi fa to tabbas sune, shari'a daga nan har kotun Allah ya'isa zamu je gaskiya, ka amince? " "Na amince, ba zasu sake zuwa ba. Wallahi nayi maka alƙawarin duk wacce ta sake tako gidannan, ranta sai yayi mummunan ɓaci. Kuma mun shaida mun gamsu gida nata ne, muna mata fatan alkhairi. Ku taso mu tafi ma kawai" Nan ya tusa ƙeyarsu suka fice, Mijinyawa yabi su kawu. "Allah ya kyauta ai kiyi zamanki Hindu asibitinnan bama sai kinje ba gaskiya. Wannan dangin mijin naki suna nemanki da sharri, danma mijinki ba irin mai goyon bayan danginshi bane, ko yasan sune ba a daidai ba. Shin kin dena shan magungunan naki ne ko yaya wannan abun har yanzu basu sakeki ba? " Innarmu tace. "Kasansu da naci ai ko sunce sun tafi laɓewa kawai suke yi, baga dangina sunata fama ba. An tsufa ma amman har yanzu anata abu guda. Ke dai Hindu ki dinga kiyaye duk abinda zai dinga ɓata miki ranki, tunda ku lalurarku bata son ɓacin rai. Sannan wannan nacin da taurin kan naki ya kamata ki rageshi. Duk wanda kike son taimakama in mazajensu ko danginsu suka nuna basaso, sai ki haƙura tunda ba dole bane. Ina amfanin da yaranki da aurenki ace an kulleki a ofishin ƴan sanda, ya kike ganin wannan maganar ta shiga cikin gida yadda za'aita jujjuyata ana kacancanata, masu neman ganin faɗuwarka hankalinsu ya kwanta." Akarami yace. Uwatale kuwa ni naso ace bata motsine a fita da'ita ranga ranga. Duk da gaskiya nasan ta daku. "Sannan tunda shi mai matar yace kar ki fitar mishi da mata, ai sai ki haƙura, wasu ma kina zaune zasu zo neman ɗaukin ki, ke ba hukuma ba ke ba gidauniya ba, ke ba takaddar shaida ba sai taurin kai da rigima da an sake an barki kin shiga aikin sojannan, tabbb za'a sha daga dake wallahi" Cewar Akarami. Dariya duka muka saka Baba Sojanmu yace. "To Hindu ki samu takaddar shaida mana ki fitar da suna, da komai in kika bi komai a tsarin daya dace zaki fi samun taimako harma daga wajen hukuma, kuma kema za'a san da zamanki in wani taimakon za'a ba yar, kema ta ƙarƙashinki za'a samu ki rabama jama'a. Kuma ya kamata ace kina da lauya ai. In kika shirya kimun magana nasan manya duk wani gudunmawa sai in baki, amman ki tabbatar kafin kizo kin tawo mun da albishir na samun gurbin karatun PHD ɗinki tukunna, kema Luba ki nemi gurbin karatu kiyi digirinki na biyu kuna wasa da karatu yadda rayuwarnan ta lalace, mazan ma da yawa suka lalace, ku tsaya da ƙafafuwanku fa. Halin rayuwar gaba ake jiye muku, ko mutuwa miji yayi ya barku da yara sai kuga baku tagayyara ba, ko rabuwace tazo shima mace ba zata lalaceba, kuma tafi kima da daraja a idanun duniya, Kema Saratu kar ki bari in kuma magana ga Innarku ma makarantar nake so ta koma itama. Luba kar ki sake in zo gidanki akan batun komawarki makaranta, ranki bazai yi kyau ba" Dariya duk muka kwashe dashi, Baba sojanmu yana dariya ya miƙe tsaye ba dai a haɗu bai yi batun karatu ba, dole sai yayi zancan a koma makaranta, nasan ina gama Phd kuma zai soma zancan batun zama Dikta ta ilimi, in sha Allah a mata a gidanmu nice Dakta ta farko bazan yi sake irin wanda nayi a baya ba. Har gaban mota muka rakasu Luba ta buɗe musu get suka fice zuwa Asibiti gaisuwar masu jiki. Su Azgar suna can. Wash Luba jikina ciwo sosai wallahi." "Hmmm Hindu, Ai dole jikinki yayi ciwo, damma ƙarfin hali gareki sosai. Hmm zamu koma makaranta dai tare wannan karon, inna soma babu tsayawa saina ƙure kullum Baba Sojanmu in muka haɗu sai ya kwaɗa mana gudumar son karatu, a wannan zamanin karatun yana da matuƙar amfani sosai. Dangane da samun takaddar shaida akan aikinki na agaji ina bayan su Baba Sojanmu gaskiya hakan yana da kyau. Wai ya batun kes ɗin Jamila marigayiyane? " Sosai Luba nima dama lokaci nake jirane shi yasa kika ji ban tada zancan ba, amman dama zanyi takadda dolena tunda inason wannan aikin da nake yi, gaba kaɗan ma aikin jaridar bar muku zanyi fa in nitse a aikin agaji, inason kuma in samu ilimi sosai. Wai Luba ba zaki koma gida ba mai jegon wai dawa kika barta ba zaki je ki dinga ɗaurawa kina sauke tukunyar ƴan barka da kunun kanwar miƙama maƙota ba" Dariya muka saka Luba har tana hawaye tace. "Da'ace bani da abun yi haka dole zaka yi wannan aikin ko kaƙi ko kaso, bama aikin bane wahala tunda ladan gidan aure kake nema babu mai yaba maka duk yadda kayi sai an zageka, dangin kishiya da dangin miji wallahi bansan waɗanda ba'a iya musu ciki ba" Ai duk inda kika taɓa wutane Luba kina ganin abinda a gabanki yau ya faru, na jiyanma akan idanunki ya faru fa ke da ba dan su Baba Sojanmu ba, bamu san yanzu wanne zancan akeyi ba da yanzu unguwarnan ta tashi, naso ki barni in sake jibgar Uwatale nifa a wajena bata daku ba. Batun kes ɗin Jamila ai ya sauya salo, zan baki labari" Wayata ce ta shiga ruri na jawo na duba Hajara ke kirana, da sauri na ɗauka tana kuka tamkar ranta zai fita a gangar jikinta, tayi magana ta kasa ta kashe wayar ta kasa. Shiru nayi ina nazari da tunanin shin mu mata wai a haka rayuwarmu zata ƙarene cikin ƙunci da takaicin mazane? Ajjiyar zuchiya na sauke kana nace. Hajara ki ƙarfafi kanki da kanki, ki zama jaruma ki nemi ƙafar tsaiwa da kanki, zan taimaka miki da jari sannan duk bala'i ki shiga islamiyya zaki gane haƙƙoƙin miji akan matarshi da naki haƙƙoƙin a kanshi, da yadda ake haƙuri mara cutarwa da yadda ake neman ƴanci kinga addininmu na Musulunci addinine mai sauƙin da babu irinshi. Hajara muddin kina irin wannan kukan akan wanda baisan darajarki ba, to kina cikin wuya, takaici, baƙin cikin da ni dake bamu san yaushe zaki fita ba, ƙila ma iyakar tsahon rayuwarki. Sai kin dakar da zuchiyarki, sai kin saba shanye duk abinda zai faru dake duk bala'i kada ki sake kuka to daga lokacin ne zaki iya tsayama kanki. Me Figo yayi miki kuma ina Mama take? " Ajjiyar zuchiya take ta saukewa da ƙyar tace mun. "Mama muna dawowa ta kama hanya ta tafi. Anty wallahi farfasamun jikina yayi yanzu haka ko iya tashi bazan yi ba" Yawu na haɗiye kuma wai irin mazajennanne akeso ai musu biyayyar yi nayi bari na bari alhalin su kansu basu san me ake nufi da kalmar aure ba basu san ya ake zaman auren ba? Tur da ire iren mazaje irinsu Figo tur da mazinatan maza masu buɗe tsaraicinsu ga matan bariki tur da mazinatan maza masu zinar wayar ire iren su Mijinyawa. Hajara kada ki sake bari Figo ya dokeki, ki haulace mishi duk abinda kika samu ki tabbatar kin buga mishi, ko kuma in kina da halin guduwa ki gudu, in kina da ƙarfi ko da cizo da yahushi ki ƙwaci kanki, in yaga kina ramawa zai bari ko yace kije ya sauwaƙe miki ki huta. Yanzu nasan Maman Junaidu ba zata sake taimaka miki ba tunda kinga daga taimako abinda hakan ya haifar miki, ki ƙarfafa jikinki ko da rarrafene kije ki watsa ruwan zafi in kina da magani ki sha na ciwon jiki ki kwanta, in babu ki aiki yara su siyo miki. Anguwarku unguwace mai tarin dandazon matasa me kike ganin zaki yi na sana'ar cikin gida? Ko da yake ki bari ki warware tukunna zan neme ki da kaina kinji ko? Ki ƙara haƙuri." Albarka tai ta shi mun tana ta godiya tamkar zata ari baki. Haka mukaita tattauna matsaltsalu masu yawa dai har wajajen azahar Luba ta shirya ta wuce gida, bayan ta gyara mun gida har girki tayi mun, hannu a kumbure fa a ɗaure. Wato samun ƙawar da zuchiyarta take a tsarkake irin Luba sai an tona, na dai jinjinama iyabo da Uwani ta balbalin a wajena Luba har ta fiye mun Tabalbalin wallahi. Wajajen dab la'asar ina zaune a falo da labtop a cinyata ina duba abu naji an yage get mota ta shigo nasan ma mijinyawane. Ina zaune kuwa suka shigo da yara. A hankali na amsa sallamarsu kusa dani sosai mijinyawa ya zauna. "Yaya jikin naki Tutar so" Kunji makircin maza ko? Wannan kaɗanne. Hmm da sauƙi ya masu jikin kuma? " Ajjiyar zuchiya ya sauke da yaji na amsa, harda tambayar masu jiki, kana yace. "Da sauƙi sosai. Luba ta wuce gidane? " Kai kawai na gyaɗa mishi. "Ammi akwai abincine yinwa muke ji? " Cewar Azgar. Akwai Innarku Luba ta dafa muku kuje ku ɗiba kuci" Har zasu fice mijinyawa yace shima a zubo dashi. Ina zaune har dai suka