← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 85

Sashe 43

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonshi nayi tare da cewa. A'a ka bar asibitin in nasha magani na samu bacci shikenan. Yanzu in asibitin zamu je a ruwannan zamu tafi, mu ba abun hawa ba? Jibeka a jiƙe kaima ka dawo ruwa ya dokeka" Hannayena ya kama yana kallona. "Ina fatan ba ruwa bane ya dakeki ba ko, kinsan fa jikinki baya jurar dukan ruwan sama? Zan ƙoƙarta in sai abun hawa akwai wata mota da abokin aikina yaimun tayinta dubu saba'in sai dai gyara gareta da matsaloli sosai, kuma bani da kuɗinma ke kinsan komai, tsohuwace sosai tasi ma da akeyi da'ita daga baya aka ajjiye ta dai. To guntun gatarinka akace yafi sari ka bani. Amman bari in sauya kaya sai in samu Mijinyawa Babba ya aramun motarshi in kai ki asibiti, hakan zaifi" Tashi yake yinƙurin yi ina nishi na riƙe hannunshi. Ka bani magani in sha da shayi mai zafi ma ya'isa. Ko fa munje asibitin bamu da kuɗi yadda wata ya raba ɗinnan kuɗin motar hannuna ma ya ƙare gobe sai dai in tafi a ƙafa. Kaga batun zuwa asibiti ai bai taso ba. Nafi zargin gajiyace" Shiru yayi baice uffan ba yana dai ta nazari, can dai ya sauya kaya yayi alwala ya fito. Fanado ya ɓalla ya bani nasha, ya haɗo mun shayi baƙi ya kawo mun. "Bari dai muje masallaci mu dawo zamu san yadda zamu yi, ke dai babu damuwa. Kinsan bazan barki baki da lafiya a gida ba, rashin kuɗi ba hujja bane, nifa namijine Tutar so ki jirani ke dai, zan san ya zanyi dole muje asibiti" Fuskata ya shafa ya fita na bishi da idanu kawai, tare da lumshe idanuna ina jina tamkar zan tashi sama tsabar yadda nake jin daɗin irin sa'ar da nayi da miji nagartacce. A lokacin ina ganin nafi duk matan duniya dace, da samun nagartacce, tsayayyen mijin da muka fahimci junanmu gaya. Mijin da ya zame mun abokin birne sirrina. Mijin da ya yarda dani, na yarda dashi. A daddafe na ɗauro alwala da ruwan ɗumi, na gabatar da sallah kana na jawo ledar daya shigo da'ita na buɗa, shinkafa ce kwano ɗaya da wake gongoni huɗu. Kai na girgiza kawai na sha'afa babu hatsi a gidanma gobe dole zan san abunyi kafin a biyamu albashi gaskiya. Daddagewa nayi na miƙe da ledarnan a hannuna na fito. Da sauri Asama'u ta tareni tare da karɓar ledar a hannuna. Ki dafa shinkafar rabin kwano, aci har safe, wake bazai nuna a darennan ba ayi shinkafar aci da manja da yaji, in yaso gobe nayi mana mai waken da kaina" Lokacin basu tasa sosai ba, amman suna aikace_aikacen gida da har su Yaya Saratu suna mamaki. Musamman Azgar dake son yaga an sakar mishi yayi girki, har tuwo zai talga ya tuƙa. Idanu na lumshe sabida irin zazzaɓin da nake ji. Azgar ne ya shigo da sallama ina zaune a falo, matan suna Kicin sai musu suke yi, da hayaniya dai irin da yara daidai sa'anninsu. Shi kuwa Azgar duk saiya ruɗe ganin yanayin da nake ciki, yaita yi mun sannu ina amsawa a hankali. Can saiga mijinyawa ya shigo a gaggauce. "Tutar so taso muje asibiti maza, Azgar ku kula da gidan ba zamu daɗe ba" Haka na miƙe muka fito, dama da mayafi a jikina. Muna fitowa ya riƙe mun hannayena, yana riƙe dani ga lema a hannunshi har zuwa wajen motar mijinyawa. Har lokacin ana ruwan sama, amman ba mau ƙarfi ba. Ya sakani gaban motar ya zagaya a gurguje ya shiga sai asibiti. Akaimun dai gwaje_gwajen daya dace rashin hutune kawai ke damuna, aka rubutamun magani muka tawo. "Ki daure ki ringa hutawa Tutar so. Jibi jikinki fa yadda ya rikice, bakya samun wadataccen bacci, sabida zaurenki da fashin Facebook ɗinki. Washegari kuma ki shirya ki tafi aiki ki dawo kuma ki shiga aikin gida. Anya bazan hana wannan wayar da kan matan ba kuwa? Aikine shima mai zaman kanshi yana da buƙatar lokaci ga risach da kike yawan yi, na ƙananun kosis da kike yi ta yanar gizo, ki dinga hutawa, kinga ya soma shafar lafiyarki. Kullum a cikin ciwon kai kike." Idanuna na lumshe tare da buɗewa nace dashi. Ai ana samun lada sosai, irin addu'o'in da suke yi mana muna ganin hasken su mijinyawana" Murmushi yayi tare da saka tafukan hannayena cikin nashi. "Wannan gaskiya ne, shi yasa nima wani sa'in nake shiga cikin bidiyonki ayi dani ai. Sabida inason duk abinda kike so, shi yasa nake baki gudunmawata, amman a dinga hutawa. Me kike sha'awar ci tun kafin mu shiga gida in siya miki? " Tukunna Kafin mu kai wannan jallin, ina aka samu kuɗin, kaddai a wajen Mijinyawa babba ka karɓo? " "Kai haba dai wayata dai na siyar sabida dai lafiyarki madam ɗina, nasan ba zaki ji daɗi ba in na tambayo mijinyawa babba kuɗi ba. In dai ya bani zan karɓa, in ya hanani bazan ji haushi ba. Tunda yayi mana sutura, da tuni muna gidan haya muna gwagwagwa." Murmushi kawai nayi mishi. Miyar sutu nake so kayi mun inci da shinkafa, asa ɗanyen kifi ko bushasshe in kuɗin zai isa. In muka je gida Azgar sai ya siyo kayan miyan a maƙota" "An gama ranki shi daɗe da girman kujerarki" Dariyar ƙarfin hali kawai nayi. A hanya muka tsaya ya sai mun kifi guda biyu ƙananu. Muna isa gida Azgar na shigowa shi da su Gambo daga masallaci suke. Aikenshi nayi maƙota siyo kayan miya, mu kuma muka shiga cikin gidan ɗaki na wuce na kwanta ina jiran abinci Sai wajajen tara sai ga mijinyawa da tiren abinci shinkafa da miya da shayi sak irin na yau ɗinnan ya dire mun a gabana. Bai gushe ba ya dinga bani a baki ins ci, har saida ya samu tabbacin na ƙoshi tukunna. "Toh ga maganin ɓalli ki sha, ko zaki iya wanka?" Kai na girgiza mishi. Akwai sanyi, bazan iya wanka ba" Maganin ya ɓallamun, na zuba a baki na kora da shayi. Kayan baccina ya ciromun, ya fita wajen yara, ya ɗan zauna dasu ina jiyo hirarsu. Sai bayan ya sallamesu sun tafi sun kwanta, kafin ya shigo da sallamarshi. Saida yayi wanka ya hayo gadon, muka shige jikin juna, yana shafamun bayana har bacci ya kwasheni. "Tutar so! " Kiran sunana da mijinyawa yayine ya dawo dani cikin hayyacina, ya kashemun tunanin da nake yi. Na kalleshi yana zaune akan kujera. "Dan Allah kiyi haƙuri da dukkan abubuwan da suka faru ɗazu a falo, ki daɗa haƙuri da kalaman su Yaya Jamila har Allah kawo ƙarshen komai. Wallahi Tutar so kunyar Ubangijina nake yi, kan abinda shaiɗan yai riƙo da hannayena na aikata. Kema kin zamemun tamkar suruka. Naga hotunan zunubina da kika turomun, ina ƙara daɗa baki haƙuri. Ina kewa da mafarkin rayuwarmu mai daɗi da muke gudanarwa a baya, a kullum cikin tunani da mafarkan Giwata ta da nake, bata yanzu ba, wacce nake jin kunyarta tamkar zan nitse. Nina ruguza komai da hannuna. Amman nayi miki alƙawarin matsawar kika bani dama ta biyu zan gyara duk abunda na lalata. Albishir mafi daɗi da farin ciki shine, nayi miki alƙawarin ke kaɗaice sarauniya a fadata, baki da abokiyar tarayya, babu gurbin wata macen a zuchiyata. Wannan gangariyan alƙawarine ba irin gama garin alƙawarurrukan da ƴan uwana maza suka saba yi ma matayensu bane, a lokacin da suke ganiyar soyayya ba, ba kuma romon baka bane, ba kuma toshiyar baki bane Hindu cancantarki ce, da sadaukarwarki." Fasali ya ja yana yamutse fuskarshi halamun yana jin wani irin zafi a ƙasan zuchiyarshi na taso mishi. Sai dai kash nawa zafi da ciwon ya wuci gaban misali, tunda zuchiyata ta kama da wuta har yanzu ci take yi, daidai da sakan ban taɓa mance komai ba, komai da komai yananan ƙyam a ƙwaƙwalwata, a kullum saina yi bita da nazarin dukkan abubuwan da suka faru. Maganganun yaudaran da mijinyawa yake yi mun sai nake ji tamkar ya raina ni ne, ya raina kuma tunanina Hakan yasa nayi murmushi kawai nace. Naji duk abinda kace mijinyawa, zaka iya fita" Miƙewa nayi ɗauke da tiran abincin na fice na kai Kicin, Ɗakin Sabira na leƙa tana zaune tana karanta littafin labari na turanci. Ke kaɗai kike zaune, kina karatu ƴan matana? Na tambayeta ina murmusawa. "Karatu nake yi, Ammi tun jiya nake son gama wannan littafin, amman saura kaɗan, yau zan gama in sha Allah, ya jikin ki Ammi? " Da zaran goma tayi kiyi adda'a ki yi bacci. Akwai Makaranta gobe. Azgar shi yana falon ne?" "A'a yana ɗaki tare da Yaya Musa. Shiru nayi ina nazari Azgar kenan yaron kirki. Leƙawa ɗakin nashi nayi na taddashi yana waya yana gadon Mijinyawa a kwance. Musa kuma yana kan gadon Azgar ɗin yayi bacci baki a buɗe sai munshari yake ja kawai. Kai na girgiza kawai. Ina jinjina ƙarfin maita irinta su Yaya jamila. Ysnzu menene dalili, da amfanin barin Musa ya kwana, tunda tare suka zo, ai ya kamata da zasu tafi sun wuce dashine. "Ammi kina son wani abunne"? Ya tambayeni harda toshe wajen jin sautin murya a wayar. Kai na girgiza mishi kawai na karkashe wutar korido data Kicin na koma ciki da sallama a bakina. Mijinyawa na zaune inda na barshi, har naje nayo wanka nayi zaman daɓaron shafa mai, na gama inajin idanunshi na yawo a jikina harna sanya rigar baccina, na shafe jikina da sassanyar humra mai sanyi da taushin ƙamshi ta wajen MRS BUKHARI nayi hayewata gado. "Nayi kewar shaƙar wannan humrar ta dare mai sanyaya ruhi da kwantar da gajiya gami da sakko da shauƙi" Hmmmm Mijinyawa kenan. Ashe baka fita ba, nayi tunanin ka fita ai. Ka kashemun wutar in ka fice, in kuma anan zaka zauna, ni sai in bar maka gidanma baki ɗaya" "Aa wane mutum inji mutuwa. Kaina bisa wuyana zan fita." Miƙewa yayi da sauri ya fice" Juyawa nayi na soma adda'a ina shafawa bacci ya sureni ban sake sanin komai ba sai da wayata ta tasheni da alama, na ƙarfe biyun dare. Dake jikin nawa babu ta inda baya ciwo. Mayar da idanuna nayi na kulle kawai. Ƙarfe huɗu daidai kamar yadda alamar cikin wayata ya kuma kaɗawa na tashi idanuna a rurrufe, na nufi banɗaki
Chapter 43 · 0% Book details