← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 85

Sashe 81

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

azahar da nayi wanka, gashi naji sai ƙaruwa yake yi. Yawun bakina in banda ɗaci babu abinda yake yi, ko abincin rana na kasa ci, yadda Sabira ta ajjiyeshi gashi nan ban ko buɗe ba. Azgar ne yake doko mun sallama daga dokin ƙofa can.. A hankali na tashi na nufi ƙofar nasa hannu na buɗe. "Ammi wai kizo inji Kawu Qasimu suna falo" Kai kawai na gyaɗa mishi na koma. Sai nake ji kamar muryar mace bansan ko kunnena bane. Saida na isa falon naga ashe Baraka ce. Ganinta yasa na saki fuskata tare da shiga da sallamata. Na nemi waje na zauna duk aka gaggaisa. "Hindu Tutar so. Gamu a karo na barkate mun sake zuwa, amman wannan shine karo na ƙarshe in sha Allah. Haƙurin dai muka yo tattaki mu sake bayarwa. Hindu mutumin da duk kika ji anata nacin bashi haƙuri, ko ya sani ko bai sani ba to an cuceshi ne" Qasimu kafin kace komai inaso kai da shi in muku tambaya ɗaya tak" Dum yayi yana kallona ya kasa magana. Mutuminku kuwa ko kanshi bai ɗaga ba tunma dana zauna. Sai cika yake yana babbatsewa. "To muna saurarenki" Ace kaine da Baraka ka ɗakko ɗa namiji ka bata ta raina, sai da yaronnan ya girma sai ka gane Baraka na kwanciya dashi, kuma har tana cewa yanzu ta san namiji, yanzune ta haɗu da jarimi... " "'A'uzubillahi minalshaiɗanunrajin. Hindu wannan wanne irin kwatancene kuma mai muni, mafi girma? " Au da girma tambayar, ko kwatancen, sannan me yasa? " "Hindu in sha Allah na zare hannayena akan lamarinki da Gawata. Ki mun adalci kar kiga kamar ko ina goyon bayan Gawatane akan kuskure ɗaya tak daya aikata miki ba. Ga Baraka nan ta zame mun shaida Hindu" Murmushin nasara nayi kawai na dawo da idanuna kan Baraka. "Hindu wallahi Qasimu kullum a bayanki yake ba bayan mijinyawa ba. Mu babban abinda muke hange shine yanzu duk wannan faɗi tashin da irin sadaukarwarku ga junanku, a haka labarim wannan soyayyar zata tsaya, to menene makomar yara da yace dasu zai tafi, kuma ba zai sake dawowa ba, makomar karatunsu fa? Hindu ki duba lamarinnan da kyau ku daure. Ki yafe ma Mijinyawa dan Allah ki yafe mishi" Baraka kenan. Ba ko wanne labarin soyayya yake samun ƙarshe mai daɗi ba. Da in zauna in shiga wuta ta dalilin na kasa sauke haƙƙoƙin auren da suka rataya a wuyana, da mu rabu kowa yayi rayuwa cikin aminci fa? Yara da kike magana akai sun girma Azgar ya samu matar Aure, ita kanta Sabira damace bamu bata ba da yanzu tana da tsayayye. A kansu kike magana me to ya rage na tarbiyyarsu da banyi ba. Karatunsu kuma mahaifinsu zaka tambaya? Qasimu ka ba abokinka umarni ya sauwaƙemun kafin ya tafi. In ba haka ba duk inda yake sai mun yi shari'a wallahi dashi. Baraka zo mu shiga daga ciki" Qasimu muryarshi a dashe na tashin hankali da rashin tsumi bare wata dabara yace. "Zai sauwaƙe miki kafin ya tafi Hindu, kiyi haƙuri wallahi an baƙanta miki, an miki ba daidai ba. Dole ai miki uziri. Ta yiwu wani rabon ke kiranki a wani gidan. Ta yiwu hakan yasa a gaba ku dawo da aurenku ku gudanar da rayuwa mai kyau, kuƙarashe abinda kuka soma. Ai shi tuni ya haƙura. Ko wannan zuwa nawa ne ba nashi ba. Kuma sai da yayi, yayi damu kar mu sake tunkararki da maganar, nine nace aa tunda munzo zamu yi maganar. Amman Hindu wannan yafiya wacce irice kika yi ne. In an yafe ai sai a yi haƙuri ace gaba da zama ko? " Ai ina wuta Magawata naku yasa Qasimu sai ya dira a wuyanshi da faɗa. "A yanzu bana buƙatar Hindu cikin rayuwata, kamar yadda bata buƙatata. Kada kiyi zaton ni na turosu, gaban kansu suka yi. Daga gobe kin gama sakamu cikin idanunki gaba da abadan. Zaki gane bake kaɗai kika iya taurin kai da zafin kai ba. Inna murɗe babu mai iya juyo dani" Ni wallahi dariya ma ya bani, na ɗan dara kaɗan. Kafin na kalli Qasimu nace. Bari in baku hadisi ingantacce. (a cikin Sahih al-Bukhari 4072) cewa lokacin da Wahshi ibn Harb ya zo wurin Manzon Allah (SAW) ya karbi Musulunci. Wahshi shine bawa mai neman ƴanci ido a rufe, wanda Hindu tayi amfani dashi wajen kashe sayyadina Hamza. Manzon Allah ya yafe masa (ba'a bashi hukunci, ko a zartar masa da wani mummunan nufi ba. Saboda Musulunci yana shafe abin da ya gabace shi) Amma Manzon Allah S A W ya ce da shi. "Shin zaka iya boye mini fuskarka? wato ka rika yin nesa dani" Dalili Ganin Wahshi yana ta da tsananin bakin ciki da kuma tunatar da Manzon Allah (SAW) kisan shahidi Hamza ibn Abdul-Muttalib (RA), wanda yake shi ne kawun Annabi kuma wanda yake ƙauna a zuciyarsa sosai. Halayyar Annabi (SAW) Wannan bai nuna cewa Manzon Allah (SAW) bai yafe masa ba ko ya ƙi amincewa da musuluncinsa ba, a'a, kawai tsantsar raunin dan Adam ne da kuma radadin da zuciya ke ji a duk lokacin da aka tuna wanda aka Fi so da aka rasa. Bayan Haka Daga baya Wahshi (RA) ya rayu yana kokarin fanshe kansa da aikata alheri a tafarkin Musulunci, har ma ya kashe Musailama Al-Kadhdhab (makaryacin da ya yi ikirarin Annabta bayan rasuwar Annabi) a yakin Yamama, inda yake cewa ya kashe mafificin mutane (Hamza) a lokacin jahiliyya, kuma ya kashe miyagun mutane (Musailama) a lokacin Musulunci. Wannan kaɗai ya isa ku gane cewar, yafiya daban, ci gaba da zama daban. Wannan hujjar ina fatan ta fito ai? " Bance komai ba na fito, Baraka na biye dani a baya har zuwa ɗakin Sabira, tana gaban akwati tana dannawa, ga jakunkuna biyu duk ta gama cikawa ta rufesu. Sabira kije ɗakina ki zauna. Amman kafinnan ki kawo ma Baraka abinci taci. "To Amminmu muma haka zamu dawo cewa kamar yadda kuke cewa Innarmu" Dariya kawai muka yi da Baraka, itama ta fita tana dariya. Kai Baraka ta girgiza tace. "Da dukkan alamu yarannan basu san dawar garin ba, naga fuskokinsu ɗauke da jin daɗi. Ko yaya zasu kasance zuwa gobe in lokacin tafiyar tasu tayi suka ga banda ke a tafiyar oho. Kai amman Asama'u tayi asara ji yadda baƙar zuchiya tasa Asama'u tarwatsa kan wannan ahali" Sallamar Sabira ce ta katseta dan bata sauka a inda take son sauka ba sam. Abinci ta ajjiye mata ta fita. Baraka kenan ai Mijinyawa shine babban shaiɗani, mu faɗa ma kanmu gaskiya. Laifin waccan yarinyar ƙaramine da ace a ranar data soma nemanshi ya sanar dani. Ko da bazai iya tunkararta ba. Haba ku riƙa aunawa a mizanin hankali, uzirin da muke baima maza yayi yawa. Zina duk zina ce, kuma hukuncin duk ɗayane. Shin Baraka ko mata ne kaɗai Ubangiji yace kada su kusanci zina, ko akwai inda akace macece kaɗai in tayi zina rayuwarta take lalacewa ne? Ko da yake sabida tsabar yadda ire_iren mijinyawa suke da yawa a wannan zamanin ma naga wasu matan sunce gara ka zauna sabida in ka fita baka san inda zaka je ba, kuma wai mazan haka suke duka. Amman nasan ba adalci bane wannan maganar da gyara. Maza ba duka haka suke ba, daga ciki harda mahaifina dan ba mazinaci bane, daga ciki harda yayuna, da ɗana Azgar. Da akwai bayin Allah maza nagartattu masu gudun famfalaƙi tsakaninsu da zina. Sannan Baraka in akace duk mazan haka suke wallahi ni Hindu na haƙura da Aure zan zauna in rayu, kuma zan kiyaye kaina. Ni bansan ma kinsan wannan aikin ɓarnar ba " Abincin ta zuba a bakinta ta tauna kafin ta haɗiye. "Hindu yanzu yarannan haka kina gani za'a rabaki dasu? " A'a ni dai naso Baraka. So yake yayi amfani da yaran ya tursasani zama dashi, ya ɗauka mutuwa zanyi in babu su, ko yana tunanin bazan iya rayuwa ba sai dasu, kin gane? Ai nasan kotu, kuma nasan uwa ita akeba raino duk da su Azgar sun yi girman da zaɓi za'a basu sai inda suke so. Na sallamashi dashi da yaranne su je. Rayuwata daga lokacin da suka tafi na dena ganinsu, zan soma wata sabuwa, ba tsayawa rayuwata zata yi akan mijinyawa ko yara ba. Ada can haka nake ni ni kaɗai na bansan mijinyawa ba, bansan yaran ba daɗa." Dafani tayi" "Hindu burgeni kike yi babu ɓoye_ɓoye da ace haka mata suka san ƴancinsu kuma suke nuna ma maza ba zasu iya rayuwa da mazinaci ba ko. Da rabi da kwatan maza sun tsoraci zina, duk da nasan basu ji tsoron mahaliccinsu ba. Lokacin da Qasimu ya sanar dani abinda ya shiga tsakanin mijinyawa da Asama'u, na tsorata. Na kuma yadda da masu cewa nono guba ne. Dariya nayi nace. Hmmm Baraka kenan, ina jinjinama matar da zata zauna da miji mazinaci, ni nawa ma zinar da ƴar da tsugunnawa mu haifeta ne kawai bamu yi ba, mu ta buɗe idanu ta gani a rayuwarta." kurum muka yi zuchiyoyi na zafi da murɗa girman lamarinnan. A haka ba madafa su Baraka suka kama hanya suka tafi. Da yamma sakaliya na kira yaran zuwa ciki dan tunda Mijinyawa ya fita tare dasu Qasimu bai dawo ba. Kallonsu kawai nake yi ina tunanin to ni mai zance musu ne? Kuma dolen dole akwai buƙatar in yi maganar dasu tunda dai gobe zasu wuce" Babanku ya faɗa muku wani abu game da tafiyarku gobe ne? " Azgar ne ya ɗago kanshi muka haɗa idanu, sai yayi mun murmushi mai taushi, irin na ƙauna mai tsanani tsakankanin uwa da ɗa. Sabira kuwa bata ɗago ba kanta na ƙasa. "A'a baice mana komai ba gaskiya ya dai ce mu haɗa kayanmu an mai tiranfar aiki zuwa garin katsina" Shikenan abinda yace daku? " Suka ce Eh shikenan." Shiru nayi naita karanto adda'a a zuchiyata kafin nace. To zaku bi mahaifinku ku je Katsina aikinshi ya koma can. Ni kuma zan zauna anan inci gaba da aikina, sannan zan jona PHD na in sha Allah" Sai nayi tsam ina nazartarsu da yadda zasu karɓi abun. Kallon kallo suke yi a tsakaninsu su su biyun nima su nake kallo kawai. Sai kuma suka dawo kallona nima su nake kallo
Chapter 81 · 0% Book details