← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 85

Sashe 29

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

hoton Auren nasu na kuma yi, Anata magana a zaure sai tara magana akeyi masu kambabata nayi,masu saka alkhairi nayi nima dai danna hoton nayi nace. Masha Allah ga ango a gaban amarya abunshi." Na tura tare da ajjiye wayar muka ci gaba da hirarmu daga baya ma Kicin muka koma muka ɗaura girki muna yi ina bata labarin mutuwar jamila da kuma bin diddigin mijin da nake so nayi. "Allah sarki na tausaya mata iyayenta sunyi wasa da rayuwarta sosai. Amman Hindu ni kam ki bar kes ɗinnan kawai" Dariya kawai nayi mata ina yanka latas da zamu ci shinkafa da miya. "Nasan ai tunda kika ce zaki yi babu mai hanaki wannan naci da taurin kai naki ba dama" Harararta kawai nayi. Bayan mun gama girkinmu muka sake bajewa a falo sai wajejen bayan la'asar Saudatu Mustapha ta kira wayata take shaidamun mu haɗu a Calido top roof ƙofar mata. Wani gidan cin abinci ne mai kyau gami da tashe. Mijinyawa na yawan kaimu wajen asabar da lahadi kowa yaci abinda ranshi ke so. Muna kan shiryawa kenan bayan munyi la'asar muka jiyo shigowar mijinyawa da Azgar. Atampa super mai ruwan ganye na saka ɗinkin riga da zani, na ɗakko mayafina baƙi, takalmi da jakata ma baƙi, suna daga cikin wanda na siyo a landan na zizara sarƙata ta gwal da ɗankunne da ƙaramin zobenta dama akwai zoben gwal a yatsana wanda yake da'iman dan tunda na siya ban taba cireshi a hannun nawa ba. Humra na shafa mai sanyi wacce ba zata dinga tasowaba ita nake shafawa duk sanda zan fita masu ƙarfin a gida nake shafasu, bata da ƙarfi Anty Badiat tana yinta ne musamman domin mata masu fita aiki, da kuma masu cutar asma. Sam babu ƙarfi sai mace ta matsoki sosai ne zata iya ɗan jinta ato kafin a kafurtani, na san me nake yi. Tabarauna na ƙara gani na saka. Muje Luba biyar saura ƴan jarida basa wasa da lokaci. Da ɗan jarida da lauya, da likita bansan wanda yafi girmama lokaci a cikinsu ba" Dariya tayi tare da ajjiye man bakin data gama shafawa tana gyara zaman mayafinta. Tare muka fito da'ita muka tadda masu gidan a falo mijinyawa yayo siyayya kowa da ledarshi. "Hajiya Luba kece a gidan namu? " Ya faɗa harda tasowa haƙiƙa mijinyawa na girmama hatta ƙawayena. Idanunshi jawur, har sun soma kwantsa. Gaisawa suka yi sosai ya dubeni yace. "Ga rubutu da magunguna na karɓo miki, Azgar zai kai miki ciki" Saida na kawar da kaina nace. Nagode Luba muje ko? Azgar zo ka rufe get" Na juya na fita na bar mijinyawa a tsaye da Luba. Sun jima sosai. Ni dai na faɗa mota na zauna na jirata har suka gama ta shiga mota muka fice sai ƙofar mata. Haurawa muka yi sama ko zamu ga su Saudatu Mustapha, amman bamu gansu ba. Maza da mata, ƴan mata da samari, magidanta masu ra'ayin fito da iyalinsu suci abinci duk gasunan ko wanne da abinda yake yi. Luba bari in kira inji suna ta inane? " Wayata na kara a kunne kuka ɗaya biyu tayi Saudatu Mustapha ta ɗaga tare da cewa. "Gani a bayanku ina hangoku ku dawo baya kaɗan" Juyawa muka yi tare da Luba muka hangota can nesa tana ɗago mana hannu. Baya can muka je sai na fahimci wajen shi na musamman ne babu yawantar mutane kujerun wajenma na musamman ne. A wani tebiri na gaba can muka hango Sumayya ta zama ƙatuwa sosai ta zama babbar mace tamkar ba ita bace wannan doguwa fara siririyar a makaranta ba. Da dariya muka ƙarasa wajen Sumayya ta taso da sauri ta rungumeni tsam muna dariya ta sakeni, ta rungume Luba sai farin ciki muke da junanmu, yaushe rabon da mu haɗu ai an jima gaya kuwa har gara Luba duk sunje bikinta shekara ashirin baya fa kenan. Sumayya kece kika zama babbar mace haka? Gaskiya oga ya tsaya miki Hajiyata" Na faɗa bayan na zauna." Sumayya tace dani. "Hmmm jikin dai na ƙibane amman Hindu Duwaf halin da nake ciki yaci ace na dawo ƙashi wallahi, amman dake kurman jiki gareni kin ganni dumimi dani" Saudatu tace. "Hmmm ai sha'anin rayuwar yanzu sai godiyar Allah. Matsalar dai bazai wuce ta kishiya, dangin miji, ko shi kanshi mijin ba" Murmushi nayi nace Ai a cikin wannan matsaltsalun da kika karanto da wuya kiga mace tace miki bata da ɗaya daga cikinsu. Wacce kuwa bata cikin wannan layin to da sauranta a duniyarnan Saudatu." Murmushi Saudatu tayi da gani mai ciwone idanunta take suka kawo ruwa suka taru sai ajjiyar zuchiya take saukewa. Dukkanmu sai muka shiga girgiza kayuka ko wacce da abinda ya famu a zuchiyarta. Ko wacce tana da tabo ko in kirashi miki a zuchiyarta. Wallahi rayuwar mata ɗamfare take da tarin ƙalubale. Jama'a mu kwana anan, sai in Allah ya kaimu gobe. (Dan Allah a dinga karatun nazari, ba karatun nishaɗi kaɗai ba) Mrs BukhariTSURON TSIRIN... TSANDAURI
Chapter 29 · 0% Book details