Sashe 16
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
aurota basa ƙaunarta sam sunfi ƙaunar ƴar uwarsu Innah Abida kuma duk dangin Baba sojanmu a wajenta suke. Shi yasa ko sha'anine na ɓarayinta sunfi dandazo. To daɗin abun ba'afi Innata dangin ba suma zuwa suke su cika falon har da ɗakunan wasu lungunan ma. Naman kaza Salamatu ta shiga rarrabawa tana bi ana ɗauka sai wani dariya take yi dangin Baba Sojanmu na wani irin zugata ɗai_ɗai nake kallon kowa bana cewa uffan. Ni da ba dan ruwa ba ma tafiyata zanyi gashi har magriba ruwan bai tsagaita ba. Badia ce ta kirani ina sallah a ɗakin Innarmu su Yaya kuma sai ƙus_ƙus ɗin gulmar mijin da Salamatu zata aura da kayan da suka narko suke yi. Ina idarwa nabi kiran Badia. Da sallama ta ɗaga wayar na amsa mata muka gaisa. "Malama dama na kirane in shaida miki na amince a nema mun hakkina amman iyakar na kayan ɗakina wancan na yafe" Ajjiyar zuchiya na sauke wallahi jiya mafarki nayi akan kes ɗin Badia da Baballe. To shikenan Badia gobe in Allah ya kaimu zan zo in ɗaukeki har gida muje ofishin ƴan sanda mu shigar da ƙara a karɓa miki hakkin ki. Naji daɗi da kika ji kina son tsayuwa akan dugaduganki. Kinga ko babu komai zaki gyara muhallinki kuma zaki samu jarin juyawa. Kafinnan ki rubuta duk abinda ya kwashe, miki ki yi musu kuɗi sai ki turo mun total ɗin kuɗin ta saƙon kar ta kwana. Ai kin iya rubutu ko? " "Eh Hajiya na'iya rubutu zan rubuto miki in turo miki nagode_ nagode sosai. Wallahi jiya baki ga bacci mai daɗin da nayi ba" Murmushin cin nasara nayi tare da jin gurina yana hanyar cika akan wannan harkar na ƙwato ma mata ƴancinsu. Wannan labarin ya wanke mun zuchiyata fes na shiga cikin ƴan uwana muka ci gaba da gulma tare da shirin biki dan da alama akwai ƙarya da ƙure adaka a bikin. Take Yaya Zubaida tace mu fitar da lashin da a lokacin shine na sama, da kyale masu tsada na lokacin, sai mu yi ankon da ta fitar. A haka muka tsayar ni harma na hango ɗinkin da za'a buga mun, shi kanshi ɗinkin zai yi dubu ashirin gaskiya inma baifi ba kenan, ina da sarƙoƙina bani da matsala da wannan ina da sabon takalmi da jaka dana siyo manya masu tsada ta gaske guda biyu a landan, zan ci waje da ɗaya. Ruwa bai tsagaita ba a wannan rana sai goman dare. Su Yaya Zubaida duk sunce a gida zasu kwana kawai. Ni kuwa yara sai kirana suke yi hanlalinsu duk a tashe. Dole na miƙe na shirya dafa har nayi kwanciyata nima, amman Azgar harda kukanshi. A raina nace Azgar zaka yi kuka har sai ka dena hawaye. Dan ubanku in shi kaɗaine Autan maza sai dai ni dashi mu kalli juna. Wallahi_billahi na rufe babin Mijinyawa abadan. Zai sha mamakin Hindu. Ku dai ku biyoni, ni bana gaggawa daki_daki sannu a hankali nake ɗaukan mataki. Kuma yanzu saina gama tattara bayanai akan abokiyar aikin Mijinyawa kafin in tsallaka mataki na gaba. Duk abinda zanyi da cikakkiyar hujja nake yi. Mata ku bini a hankali dan Allah ku dena gaggawar yanke hukunci. Ina hanya Azgar ya kuma kirana na ɗaga nace. Azgar ina hanya bafa ɓata nayi ba gida naje ruwa ne ya hanani dawowa, amman kaga ina hanya ma." "Alhamdulillahi Tutar so wallahi nayi tunanin kin sake tafiyane kin barni a karo na biyu" Naji muryar mijinyawa a kunnena ai saina yi murmushi nace. Zan dai tafinne amman ɗakin mijina sabo ba. Ka zauna kaita yaudarar kanka dai, dan Hindu tafi ƙarfin a yaudareta wallahi. Ai kafi kowa sanin in nace bana yi da mutum in duk duniya zasu taru ba zasu saka in yishi ba. Tunda na iya bijirema iyayena na zaɓeka. Kai a tunaninka in nace na barka akwai mahalukin da ya isa ya sani in yika ne" Dogon tsaki naja tare da datse wayar kawai saina juya na koma gida kawai. "Dawowa kika yi kuma Hindu lafiya? ". Babu komai Innarmu kawai naga dare yayi gaskiya gara in kwana nima kawai" Doguwar rigar Innarmu ta bacci ta miƙomun na saka na shige tsakiyar su Yaya Saratu a kan katifar da aka sauke musu muka ci gaba da hirarmu wayoyina kuwa duk na kashesu. Inajin sanda mijinyawa ya kira Innarmu wajajen goma sha biyun dare, ta shaida mishi inanan sabida anyi ruwa bai tsaya kan kari ba zan kwana a gida tare da su Yaya Saratu. Mu kuwa hirar yaushe gamo muke yi wacce bamu samu zarafin yi ba. Sai wajen biyun dare fa muka haƙura mu kai bacci. Gida shima yana da irin daɗinshi, ƴan uwa kuma sarƙar wuya. Haka muka wayi gari sassafe na soma shirin aiki. Kayan Innarmu na saka na bar nawa anan naima kowa sallama na kama hanyar aiki takwas a wajen aiki tayi mun. Sha biyun rana akace nayi baƙo yana ɗakin jira. Ina zuwa naga mijinyawane da leda wai ya kawo mun abinci sai murmushi yake yi ko na menene oho, ni kuma na sake haɗe rai. Yayi juyin duniya nace abinci dai bana so kana bana son ana biyoni wajen aikina. Na juya na tafi na barshi daga shi har ledarshi. Ƙarfe biyar a ƙofar gidan Badia tayi mun, sabida sauri yasa ban shiga ba itace ta fito ta kuwa saka ɗaya daga cikin kayan dana bata harda mayafi wallahi ashe da kyanta, wahala ce kawai da ƙwallafa ɗa namiji a zuchiya ya sukurkutata. Kai tsaye muka nufi ofishin ƴan sanda na kusa muka shigar da ƙaran Baballe akan ya siyar ma da Badia kayan ɗakinta. Akayi rubutu akai duk abinda ya dace. "Yanzu a ina zamu samu Baballe ke Badia? " Ɗan sandan ya tambayeta. "Ko yanzu dana fito yana gida" "To shikenan bari aje a tawo dashi yazo sai a sasanta in ya yiwu, in kuma bai yiwu ba, sai mu turaku kotu kawai. Kofur Bala aje a ɗakko Baballe ta baka adireshi maza a tawo dashi tace yana gida" Muna zaune dake babu nisa sai ga ƴan sanda da Baballe sun shigo. "Abu ta kazan uba... Da gaske dama Badia ke kikai ƙarata to akan nayi miki abu ta kazan me? Zaki yi ta aurenki kuwa wallahi ƴar abu ta kazan uba " To sai me dan tayi ta auren nata? Baku da aiki sai barazana da saki, ko in kun saki mace mutuwa akace muku zata yi oho. Ko kuma kun ɗauka rayuwarta tsayawa take yi ne oho" Sheƙeƙe ya dubeni ya maya baki a buɗe na fahimci kallo na biyu na mamakine, shi yasa ya buɗe bakinshi. Kafin yace um an tasa ƙeyarshi zuwa bayan kanta, mu kuma muna daga wajen kanta. "Matarka Badia ta kawo ƙararka akan ka siyar mata da kayan ɗakinta kaf ba da izininta ba, kana baka iya ɗaukar nauyinta dana yaranta. Shin gaskiya ne anyi haka ko yaya? " "Abu ta kazan ubancan. Tabbb Badia wannan bayahudiyar mai hure ma mata kunne itace ta zugaki kike son tozartani a idan duniya, abunda baki taɓa yi ba? Matar da ake cewa kwangilar rushe matan aure taje ingila ta karɓo yanzu layin har yazo kanmu? " Kunji lafazin bakinshi? Hmm baku ji yadda yake magana da ƙarfi ba, bakinshi sai yauƙi yake yi. Da gani babu tarbiyya da addini tattare dashi jahiline tsantsa. "Dallah mai firen rufe ma mutane baki nan ba wajen wasa bane, hakane ko ba haka bane? " "Ba haka bane sharri suka ƙullo suyi mun kawai, yallaɓai wannan in kana Facebook zaka santa kullum fa bata da aiki sai zagin mazan arewa da nuna ma mata gazawar maza. Ina binta ai har kwamen na zagi nake yi mata a duk sanda ta saki sabon bidiyo. Ita da Lubna boƙararriya ina yawan la'antarsu." Banci ɗan sanda ya buga Baballe ya dawo hayyacinshi. "Kace baka siyar mata da kayan ɗaki ba ko? In muka je muka duba babu kayan ɗakin zaka sha wuya har gidan yari za'a kulleka" Da jin gidan yari sai Baballe ya sakko ya hau in ina. "Da gaske na siyar amman ara nayi ranka shi daɗe, ayi haƙuri sati mai zuwa aurena taya za'ace za'a kaini gidan gyaran hali? " Muryarshi lub tamkar bashi bane yake ɗura ashariya yana ɗumawa ba. Ofisa yace. "To zamu kulleta har sai ka biya kuɗin, madam nawa kika ce kayanki zai kai? " "Dubu ɗari biyu har da hamsin, ga jerin adadin yawan kayan daya siyar mun nan duk na rubuta a bayanaina" Baki Baballe ya buɗe idanunshi jawur yana kallona cikin tsana, ji yake kamar ya sakar mun iskar gas. "To zaka biyata kuɗinta mun baka kwana biyu in baka biya ba zamu turaku kotu, daga kotu sai gidan gyaran hali. Sajen a shiga dashi babu beli har sai ya biyata hakkinta. A tuɓeshi a adana mishi wayoyi da kuɗaɗenshi." Godiya naita ma ofica ina ƙarawa yace babu komai muje kawai gobe sai mu dawo da rana ko safe. Badia jikinta duk a mace yake har muka ƙaraso Mr Bukhari ce.