← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 85

Sashe 11

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gidana yace zai tayar mun da hankali. Sabida haka ku tashi ku fice mun a gidana, ko dole ne, ko kuma zuchiyace babu?" Ranar anyi ɗauki babu daɗi wallahi dani da Jamila da Uwatale. Dan Uwatale ta tashi tsaye kamar zata dakeni. Ni kuma a lokacin jikina har rawa yake yi. Bansan sanda na zabga mata mari ba. Na kuma sharara mata mari. Inaso in sake marinta sai ga hannuna a kan ƙirjin Nawata na mara. Idanuna ya gama rufewa jira nake wani ya tunkaroni in dira a wuyanshi. Duk sun ja baya suna salati, nanno ta ƙanƙame ƙanwarta Goggo ƙam. Mijinyawa da Azgar ne suka nufo ni da zummar riƙeni. Hannayena nasa na hankaɗe Mijinyawa yaje ya zauna da ƙarfi a kujera, dashi da kujerar suka kifa. Na ɗauke Azgar da mari, na rufeshi da duka tako ta ina kawai, ya ma kasa karewa. Ita Sabira wajen Ubanta ta nufa harda kukanta. Da ƙyar ƙurar ta lafa nai musu wankin babban bargo, idanunsu duk suka raina fata. Suna takure a waje ɗaya tsoro na neman halakasu. Fuu na sa kaina na fice a ɗakin. A ɗakin Sabira na zauna ina jijjiga. Ina hango su Sabira suna kai musu kayan kari, marasa zuchiya kawai. Naga yayo cefane da yawa harda buhun shinkafa, da katon na taliya, katon na makaroni, da wake, doya, man gyaɗa, manja, maggi, ƙwai, kayan shayi. Azgar ne ya zubo mun soyayyar doya da shayi. Ɗauke doyarnan. Akwai kayan shayi a ɗakina wuce kaje ka haɗo mun dashi" Zai yi magana na nuna shi da yatsana jikina na wani irin rawa. Da sauri ya miƙe zumbur. A ɗakin Sabira na karya su kuma nace suje falo bana ma son ganinsu suma ɗin. Ina shan shayi mijinyawa ya turo ƙofar ya shigo ya zauna a bakin gadon, ni kuma ina daga ciki. Tunda ya buɗe ƙofar nayi mishi kallo ɗaya ban sake ɗagowa ba bare mu haɗa idanu. "Hindu kiyi haƙuri da abinda su Nanno suka yi miki, nasan in da sabo mun saba kiyi haƙuri kinji?" Naji, nayi kuma" Na faɗa a taƙaice, sai yayi shiru can yace. "Na saki Asama'u sabida na gane nayi kuskure mai girma Hindu. Na rantse miki da girman Allah ban kwanta da Asama'u ba tunda na aureta, san... " Da Allah mijinyawa bana son jin komai. Kada ka sake kiran sunan tsinanniyar yarinyarnan a gabana kar ka sake nace, ka kusanceta baka taɓa kusantarta a rayuwarka ba, ni fa inka lura bashi ne a gabana ba. Sakinta da kayi zaluncine kuma. Ai dama maza kanku kaɗai kuka sani, duk abinda zaku yi kanku kuke sawa a gaba. In Abdulƙadiri ne ya lalata maka rayuwar ƴa suka gama tumɓele a titi, zangon baƙi_ zangon baƙi, ya aureta ya saketa zaka ji daɗi ko? To ka sani ka zalunci ƴar mutane ni daka ganni bana bayan zalunci, Hindu bata kasance mai son kanta ba. Ka fice mun a raina babu abinda zaisa ka sake shiga mijinyawa. Bazan iya zaman aure da mutumin da bana jin ko ɗigon sonshi ba, takaddata kawai nake buƙata. Ka sauwaƙemun saki mara kome in je in yi auren farin ciki ga mijin da bazai ci amanata ba. Ko da zai ma ci ba irin wannan nakan ba. Sannan kayanka daka jera ka kwashemun ka bi danginka ku fice mun a gida tun kafin in muku korar kare. Ina ɗaga muku ƙafa sabida yaranane kawai. Amman wallahi ka kiyayeni in ba haka ba zan maka abinda abadan yaranka ba zasu iya sake kallonka ba." "Hinduuu... ni kike cema zaki auri wani? " Ya ambaci sunana da zafi da kaushin murya har tana ɗan rawa_rawan kishin nace zan yi auren farin ciki. Miƙewa tsaye. Miƙewa nayi inajin wani irin ƙarfi na zuwa mun, take na soma tunkararshi yana matsawa da baya da baya. Iyakar abinda na sani kenan na dawo hayyacinane na tarar da mijinyawa a bango, hannayena du biyun suna wuyanshi na shaƙeshi yana kakarin mutuwa, idanunshi sun firfito sosai suna ta hawaye. Da sauri na sake mai wuya na ja da baya. Ai sai ya kama haki, gami da tari yana dafe da wuyanshi. Zama nayi ina harararshi Da sauri ya fice. Na bishi da harara. Kaina sai yamutsewa yake yi. In ka gaji da kanka zaka zuchiya ka rubuta mun takaddata wallahi, aikin banza da wofi yaushe zan iya sake yadda dakai a rayuwata. Hmmmm. Jikinka na rawar iskanci dan na ambaci zan auri wani, ni da ka Auri yarinyar dana gama rainonta ka lalatata kafin ka Aureta, ka kaita har gadonmu na sunnah ashe haɗiyar zuchiya ni ya kamata ace nayi kenan. Maza da yawa basu da kunya wallahi hiye. Ban sake komawa falon ba wuni sukai cur inajinsu a Kicin sunata dafe_dafe da soye_soyen gadarar cefanan ƙaninsune yayi, ni kuwa ko a jikina in sun so su kwashe abincin dukka ma in zasu tafi. Shi su kai ma asara wallahi ina abinda ya dameni. Da su Uwatale suka shigo ɗakin Sabira yin sallah sai nayi komawata ɗakina, tare da daka tsaki, suna jina. Na shiga group ɗin gida anata shirye_shiryen bikin Salamatu har zuwa lokacin ba'a san wanda zata aura menene muƙaminshi ba, gashi mu ɗabi'ar gidanmu shine in mace zata yi aure a san muƙamin mijin nata to su Salamatu sai suka ɓoye face dai iyaye maza da su dole zasu sani. Abinda muka sani shine a katsina zata zauna. Su Nanno basu suka bar gidan ba sai bayan azahar. Ina kicin lokacin "Zanje in rakasu gida sai dare zan dawo kinji? " Murmushi nayi sabida a gabansune nace. Adawo lafiya Allah ya tsare" "Zamu je har da yaran sa dawo da uban nasu in zai dawo? " Gaku gasu Jamila wannan ma in aka faɗama ubansu ya wadatar ai. Inma dasu zaku koma laba'asa" Sallama nayi ma su Nanno nayi shigewata sai da suka tafi na fito na shiga gyaran waje. Ruwa har a kujera da ƙasan kafet sai da suka zubar mun. Ga tulin wanke_wanke da suka barmun akayi kaca _kaca da Kicin da saman gas kukan ma dan mugunta irin ta wasu dangin mijin. Kajin da ya siyo guda biyar sun soye biyu sun cinye, uku suka rage na buɗe firiza na jefa na kunna dan babu komai a cikinshi. Kayan abinci kuwa naga halamun an ɗebi kusan kwatan buhun, na cikin kwalin duk an ɗiɗɗiba, nama gani a hannun Uwatale a cikin bakko. Adana komai nayi a inda ya dace na tsabtace gidana, na ɗaura tafashen kaza kana na je nayi sallar la'asar. Ina soya kaza, ina shan shayi dana haɗa dan yinwa nake ji sosai. Kafin Magrib na gama aikina tsab da nayi sallah kuma na zauna kenan naji ana buga get babu shiri na nufi bakin get na tambaya su waye. Ashe su Baba Sojanmu ne da su Innah Abida suka zo ganin waje. Sai cewa Innah Abida tayi. "Gidan ɗan mitsitsi dashi abun sha'awa. Akace guntun gatarinka ai yafi sari ka bani, amman dai yayi kyau. Ya fiye muku gidan wan mijinki mijin Uwatale ko" Kallonta kawai nayi Innarmu ce tace da'ita. "Ai kuwa wannan gidan baiyi irin wannan ƙanƙantar da za'a kirashi da guntun gatari ba. Ke dai magana kika faɗa kawai. Gashi komai ya zauna a muhallinshi" "Ba haka nake nufi ba Ruwayya" Baba Sojanmu dai yana ta kallonsu suna mayar da zance, Innah Turai tace. "Gida kam yayi masha Allah. Kuma wallahi yayi namijin ƙoƙari a wannan zamanin da filaye ma faɗar ɗaya suke yi balle ka sai gida a tsaye" Ni dai abinci na fita na kawo musu, Innarmu tace zata kama ruwa kafin taci abincin. Ɗakina na shiga da'ita ashe ba ruwan zata kama ba. "Hindu maganace take ta cin zuchiyata shi yasa na kasa haƙuri sai kin zo gida muyi zancan. Wannan yarinyar ta faɗamun ashe ke kika sai gidannan ba mijinyawa bane ya siya ba. Ina fatan wannan makwaɗaitan iyayen nashi sun san zancan dan gudun watarana? Kinga Goggonku Yahanasu, ta taɓa siyan gida suka rayu a ciki ita da mijinta na farko, babu wanda ta sanarma gidan nata ne har Allah yayi mishi rasuwa kuma ɗiya macece a tsakaninsu, kinga danginshi na da gadonshi. To sai a wannan lokacin take sanarwa ai gida nata ne. Rikicin da akayi har kotu kuma duk da haka su sukai nasara a kanta aka samu wani baƙin azzalumin lauya haka aka raba gadonnan da ƴan uwanshi, da haushi ya ƙume Goggonku gadon yarinyar tata da tuminin takabar ta duk ta haɗa ta bar musu, kinsan mu Kanuri muna da zuchiya sosai. To shine nake gudun kada a kuma" Sun san ba gidanshi bane a yau da suka zo, bayan azahar suka tafi suma da sunyi tunanin shi ya siya har Nanno ta soma faɗanta" "To shikenan daga nan kada maganar ta fita ko ina a rurrufa a zuwan shi ya siya ɗin. Kinsan gidan namu ya sake lalacewa da gutsiri tsoma sosai anyi rikice_rikice da gore_gore sosai lokacin kina landan har yanzu ƙurar bata gama lafawa ba ma. Sannan sunanki ne akan takaddar gidan ko? " Innarmu sunanane, ki kwantar da hankalinki. "Muje kar su ji shiru Abida ta biyo mu" Tare muka fita muka dawo falon. Suka ci abinci sukai mun sallama suka tafi. Dukka abincin suka cinye dake dama iyakar mu nayi abincin sai shayi na haɗa na dafa taliyar ƴan yara naci nayi ƙat. Da misalin taran dare ina zaune ina kallon tashar Arewa 24 na jiyo ana buɗe get dake akwai kin get a hannun Azgar. Jim kaɗan sai gasu sun shigo da kayan shofin leda leda nan falon suka baje yahuza suya da Habib yogot nima aka miƙo mun tawa ledar. Hannu nasa na karɓa ba tare da godiya ko nuna jin daɗi ba. "Ba yanzu zaki ci bane Giwa?" Na riga na ci abinci a ƙoshe nake" Bismillah nayi na tashi zan fita. "Tutar so kin mance da ledar taki baki ɗauka ba?" Ya faɗa da murya mai sanyi. Ban kalleshi ba nace. Sabira ki saka mun a firji in kin gama" Na yi shigewata ciki. Washegari ranar aiki ce sassafe kowa ya shiga shirin fita. Na barshi ya sake kwanane sabida su Nanno suna gari basu tafi ba. Bana so suka komawarshi da komatsan kayanshi. Amman
Chapter 11 · 0% Book details