← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 85

Sashe 7

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yadi, da singileti a jikinshi, ga ƙirjinnan ya haye kamar ɗan damben gargajiya. Wani muƙu_muƙun baƙin cikine ya kuma murɗeni. Kutsa kaina nayi cikin gidan shi kuma ya rufe get ɗin. Ke Sabira tashi ki shiga ciki mun iso gida" Na faɗa ina bubbuga Sabira. Murfin motar Mijinyawa ya buɗemun yana mun murmushi tare da amsar jakata. Na ko haɗe girar sama data ƙasa. "Tutar so sannu da shigowa maraba" Dubanshi nayi na girgiza kai kawai na fito nayi shigewata ciki. Sai kawai naga Qasimu a falo yana mun sannu da zuwa. Hmmm ohh shi aka ɗakko mun? Raini kenan shi wannan kamar ma baisan girman zunubin daya aikatamun ba ko? Qasimu ne zai sasanta wannan lamarin mai girman da yayi lalacewar da babu abinda za'ayi a gyarashi. Lallai na Mijinyawa wasane. "Hindu barka da dawowa sannu? " Babu wasa a fuskata kamar yadda aka saba. A hakan muka gaisa nayi wucewata naga jikinsu yayi wata iriyar muguwar mutuwa. Ina shiga ɗakina na danna sakata. Banɗaki na faɗa nayi wanka na fito. Azgar ne yazo yana buga mun ƙofata. Saida na saka kaya na buɗe mishi ya shigo. "Ammi Abba ne yace in miki magana suna falo. Ammi dan Allah kije kar ki ƙi zuwa kinji. Nasan abinda Abba yayi miki da ciwo amman ki saurareshi ko dan albarkacinmu" Kallonshi nayi muka yi murmushi a tare ina jin son su na huda ni. Azgar akwaishi da ƙoƙari da kulawa akan iyayenshi, nasan baya wuce ramar da yaga munyi ni da ubanne yasa duk jikinshi babu daɗi. Ba yara bane sun san dukkan abinda ke faruwa, ai suna gani ubansu ya auri Asama'u ni dasu dukka abun bai yi mana daɗi ba. Shine dalilin da yasa kaƙi bina, sabida ka buɗe ma Iyayenka gida su shigo ko?" Kai ya sauke ƙasa. Ai saina shaƙeshi na haɗashi da bango da ƙarfin da ni kaina nasan yafi ƙarfinshi, idanunshi suka firfito, ai sai kuka kawai ya sake. Sake shi nayi da sauri, ina harararshi ba ƙaramin haushi ya bani ba wallahi, ya zai mun haka. "Ki mun afuwa Ammi, kiyi haƙuri wallahi ya roƙeni ne in mai hakan. Amman bazan sake ba" To shikenan ganinan zuwa Azgar ya kan naka ya dena ciwon amman, ko dama shima kan baya ciwo? " "A'a Ammi ina ta shan magani amman gaskiya babu wani sauƙi, jijiyoyin kaina ciwo suke yi mun sosai" Kallonshi nayi naga idanunshi sun yi jawur dasu ga wata jijiya a gefen idanunshi daya tsaya. Duk da dai ya sha shaƙa. "Azgar akwai abinda yake damunka ne daya haddasama ciwon kannan, ko kuma karatune? Baka ƙarya baka taɓa yi mun ba, kada ka soma. Duk duniya baka da kamar ni meke damunka yarona? " Murmushi yayi ya sauke kanshi ƙasa yace. "Ammi bansan ta ina zan faɗa miki damuwata ba, amman ina cikin damuwa sosai" Murmushi nayi nace mishi. Ka zauna ga kujera ka jirani inje in dawo sai in zauna ka warwaremun matsalar kaji ko? " Na ƙarashe cike da nuna kulawata gareshi. Sai da na tabbatar ya zauna kana na fita na shiga falo da sallama na zauna a kujera. Gani Qasimu kun aika yaro kuna nema na, Allah yasa lafiya dai ko?" Na faɗa idanuna akan Qasimu shi kuma mai gayya ina jin idanunshi na yawo ajikina hakan yasa banyi gigin duban inda yake ba. Sassauta murya Qasimu yayi yace. "To Hindu ni nama rasa ta ina wallahi zan soma maganar ko kuma in kirata da roƙo." Numfashi ya zuƙo daga huhunshi ya fesar kafin yace. "Hindu duk wanda akace yayi haƙuri an gama cutar dashine. Mijinyawa ya faɗamun dukkan abinda ya faru a tsakaninku. Haƙiƙa abinda ya faru al'amarine mai girma wanda ya kai kiyi fishin da kika yi, domin ki huce babu laifi a ciki Hindu. Amman wallahi bana bayan Mijinyawa tun farkon fari, sabida dai bani da iko dashine shi yasa dole na zama ɗan kallo. Abunda ya shiga tsakaninshi da Asama'u wani abune na ƙaddarar da bawa bai isa tsallakewa ba. Dama shi shaiɗan burinshi babba shine shiga tsakankanin ma'aurata musamman masu fahimtar juna irinku. A iyakar ƙuruciya zuwa samartaka mijinyawa daidai da hannun mace bai taɓa riƙewa ba. Kuma kema shaidace tunda kun jima kuna gabza soyayya. Wannan abinda ya shiga tsakaninsu wani abune da zamu mishi kallo a matsayin ƙaddara da tsautsayi. Dan Allah kiyi haƙuri ki yafe mishi ya tabka kuskuren da bazai gyaru ba. Amman nadama muraratan a cikinta yake wallahi yayi nadama ya shiga damuwa sosai. Hindu bayan tafiyarki har zangon baƙi mijinyawa ya koma, sai ni naita tausarshi ma kafin ya dawo gida. Tunda abun ya faru har yanzu zuchiyarshi a cikin ƙunci take. Hindu kalamaina sun ƙare, yawuna ya ƙafe, harshe da haƙori ba zasu iya sarrafa miki yadda mijinyawa yake nadamar abinda duk ya faru ba. Sannan kinsan yana sonki irin son da ba ko wacce mace bace ta samu soyayya da sadaukarwa irin wanda ke kika samu ba. Ayi haƙuri ayi haƙuri. Ki tuna yara da irin zaman da kuka yi a baya. Ki auna da alkhairanshi Hindu sai a yafe mishi a fuskanci gaba. Duk wannan akan Asama'u dai akeyi to maganar Asama'u yazo ƙarshe ma ayi haƙuri. Shafinta an kulleshi abadan. Dan Allah kiyi haƙuri, abinda akayi miki da zafi" Yayi shiru yana sauraren ko akwai abinda zance. Ni kuma nayi shiru, duk maganganun da yake yi na sokiburutsu ni bama shigata suke yi ba bare har su taɓa zuchiyata in sakko ba. Sabida ba wajen bane, to Qasimu ne zai sa in sakko, ko a tunaninsu fishi nake yi ne? Wallahi da fishin nake yi in akace ya matso inda nake ma, ai bazai matsoba. Balle har ya tattagomun abokinshi sun wani sha ankon yadi kamar abokan ango, ga uban kwalli dama_dama caɓa_caɓa a idanunsu. Duk abubuwan da yace in kalla, shi mijinyawan me yasa shi bai kallesu a yayin aikata abinda ya aikata ba? Wato su maza suna da damar yin duk abinda suke so, sabida gadarar dole ne ma a yafe musu ko anƙi ko anso. Ko da yake malam bahaushe ma cewa yayi duk abinda namiji yayi adone. Mace dai itace a ƙasa duk ƙanƙantar abinda tayi sai ya taɓa rayuwarta shi kuma yaci bulus abinshi. Ado aka kira iskancin maza, a gabansu, a cikin kunnensu, tun suna yara an cusa musu wannan maganar mai cike da muni. Amman a hakan wai mijinyawa ya ba mata tausayi har suna taya Qasimu godona, wai in yi haƙuri mu ci gaba da zama. Ashe ba Hindun bace ma. Jin naƙi magana Qasimu ya sake cewa. "Sai batun sabon gida. Na taya ki murna sosai da Allah ya baki nasarar mallakar muhalli irin wannan. Amman muna roƙon ki yi haƙuri ki kuma daure ki koma ɗakin ki Hindu, a taimaka ko dan sabida gudun maganar Nanno dan nayi imani ba zata yadda ba. Yanzu haka ma gobe tana hanyar zuwa garinnan ne, kuma akan batun wannan gidanne maganar gaskiya. In yaso wannan ɗin sai ko haya ne a saka. Kiyi haƙuri duk dai akan zama da Asama'une to bata gidan a halin yanzu dan Allah Hindu kice wani abu, a duba yarannan sun girma bai dace ace har sun san abinda ke faruwa a tsakaninku ba" Mijinyawa ya ɗaura da cewa. "Giwar mijinyawa nayi miki alƙawarin zaki sameni fiye da yadda kika sameni a baya. In sha Allah bazan sake aikata abinda zai dameki ba. Giwar mijinyawa kiyi haƙuri nasan nayi kuskure mai girma. Wallahi kunyarki nake ji fiye da yadda kike tunani, kiyi mun aikin gafara ki tuno da irin soyayyarmu mijinyawa naki ne ke kaɗai har abada babu wata mace da zata... " Ƙur nayi mishi da idanuna, waɗanda sabida ɓacin rai har ƙanƙancewa suka yi, cike da tuhuma nake kallonshi, duk sai ya dibibice nasan abinda na tuno shi ya tuno irin kushe halittar nonona da ya dinga yi a wajen Asama'u da irin yabon zatinta daya dinga yi. Ya ce mun bagidajiya, itama tace mun bagidajiya. Alhalin sune gidadadawa ƴan ƙauye. Yace mun mai tumbi, yace mata suna suka tara, kenan ni Hindu ba mace bace rako Asama'u duniya nayi. Wai da duk wannan inci gaba da zama dashi? Asama'u fa in ba bacci tayi ba, bana ko runtsawa, gata da laulayi ciwo babu irin wanda batai ba. A kanta meye ni Hindu ba'a faɗamun ba. Haka zan rungumeta akan ƙirjina ina jin tsabar sonta kamar in maidata ciki in haifota. Amman yau itace ke kirana bagidajiya, sakamakon tsirara da mijinyawa yake yi a gabanta. Ya salam wai kunsan zafi da raɗaɗin irin wannan abun kuwa? Kunji amman wai shi nawa ne shi ni kaɗai. Hiye maza kenan wacce bata san yaudarar maza ba an sha da'ita. Murmushi kawai nayi da naga ya kasa iya furta wata kalmar yayi shiru yana ambaton. "Hasbunallahi wa ni'imal wakil. Billa nasan ba zaki yadda da duk abinda zai fito bakina ba. Giwar mijinyawa ki yafe mun" Har gaba da abada kuwa. Ai da ka ƙarashe yaudarar daka tasamma furtawa Magawata, da baka fasa ba. Shure_shure ai baya hana mutuwa ko?" Jin na ambaci Magawata sai suka kalleni Qasimu hannu a baki na ta'ajibi. Tasowa yayi yazo gabana kamar mai neman gafara ya tsugunna, wallahi a kan guiwowinshi yana rokona da duk kalaman rarrashi da roƙo. Nasan yana sona fiye da tunani amman narantse da Allah inji ɗigon tausayinshi banji ba. Ni sake tunzurani ma haƙurinsu ya bani, a ganina an raina ni ƙarshe da aka rasa wa za'a ɗakko sai Qasimu, Qasimu fa. Miƙewa nayi na dubi Qasimu nace. Nagode Qasimu mu kwana lafiya, dan Allah a gaishe mun da Baraka. Bari in ɗakko tsaraba a kai mata tunda dai kazo. Sannan nan gaba kada ka sake tunkarata da irin wannan surutan bana so, na ɗaga maka ƙafa sabida ƙawata Baraka ne kawai" Ajjiyar zuchiya ya sauke yace. "Baraka zata ji, zata ji Hindu" Haka yaita maimaitawa wallahi kamar mahaukaci fa. To ya faɗa yafi sau shidda. Na gigita Qasimu sosai ya gama faɗen duk abinda yake son faɗa amsa ce babu, bani da wannan lokacin a halin yanzu, ba wajen bane. Na fita a hankali nake takawa dan jiri ke neman kayar dani. Inaji Mijinyawa na cewa. "Qasimu ka taimaka kar in
Chapter 7 · 0% Book details