← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 85

Sashe 66

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saudat:. Bari dai in ci gaba kar in sauka akan maudu'in da nake kai, kamar yadda Mrs Bukhari take yi labari cikin wani labarin, wani sa'in inta shige cikin wani labarin sai ya danne labarin farko wanda kuma shi ya haifi wannan. To a haka muka ƙulla alaƙar soyayya ni da Nazifi sosai mai ƙarfi. Naga bahaushen bature, ma'abocin son turanci da rayuwar wayewa ta masifa. Kuma shi a lokacin iyayenshi suna son ƙulla Aurenshi da ɗiyar ƙanin mahaifinshine, shi kuma baya so yace bata waye sosai ba, bata cikin kalar tsarin rayuwarshi har hotonta ya nuna mun, naji kishi sosai sabida ta fini kyau sai dai in nuna mata wayewa, da manya manyan turancin dana dinga nacin iyawa tun muna sakandare ai kun san wannan gurin nawa. Mun shirya zamu yi aure zai barni a Najeriya in ƙarashe karatuna, kafin yazo ya ɗaukeni mu koma Amurka in jona mastas ɗina acan, ya kuma nema mun aiki. Ai kuwa dake Abbanmu ma yasan familyn Nazifin bincike bai zame mana wahala ba, kuma bamu ji mummunan tarihi akan Nazifi ko zuriyarsu ba, bai koma Amurka ba saida aka ɗaura Aurenmu, amman kash a ranar ya bar ƙasar ko ɗaurin auren bai samu halarta ba. yana Abuja sabida ta can jirginsu zai tashi. Amarya ita kaɗai a katafaren gida sai abokanshi ne suka zo suka sayi baki, suka sallami ƙawayen Amarya ni kuma daga ni sai Magena kuliyana tare muka tare yana gefena. Ni dai nayi shiru a kan sabon gadona inata nazari akan Nazifi, da irin burin da yaci na wannan ranar ashe bazai kasance tare dani ba. Murmushi nayi kawai na miƙe naje na yi wanka na sauya kaya na kwanta a bayan Usama magena ɗan Amana fari sol dashi ɗan ƙasar waje. Bacci ranar nayi harda makara, ba sabamba anyi gidan kai" Mariya Habibu tace. "Hmmm ɗakin kai akwai daɗi yafi ko wacce duniya daɗi, amman fa in an dace. In ba'a dace ba kuma yafi ko wacce duniya tashin hankali da matsala, mace inta rasa farin cikin gidan aure rayuwarta taɓuwa take yi." Kai kawai Saudat ta girgiza ta kurɓi zoɓo kana taci gaba. "Hmmm a waya ni da Nazifi tamkar zamu haɗiye juna haka muke soyayya, kullum zani makaranta in dawo, ban nemi komai na rasa ba ban taɓa kukan komai ba. Har Allah cikin yaddarshi, da amincewarshi, na kammala digirina tas a fannin lauya sai ya rage shirye_ shiryen tafiya Amurka kawai aketa yi mun, daga dangin Nazifi kuma ni kaɗai zan tafi babu ɗan rakiya daga ɓangarenshi ko nawa" Tsaya kada ki mana rinto baki faɗa mana sau nawa ango yazo aka darje Amarci ba? " Na tambaya ina tuntsurewa da dariya. Luba tace. "Hindu rigani kika yi gaskiya, kinsanni da shegen son labari, gani da wutar ciki" Ita kuma sai tayi dariya tace. "Bai zo ba ko da sau ɗaya ne. Haƙuri dai kullum yake bani akan yanayine na aiki" Ƙur nayi mata ina nazari can nace. Kuma ke a lokacin baki yi zargin komai ba, a matsayinki ta lauya ba. Namiji mai lafiya ya auri mace ya ajjiyeta bai waiwayota ba. Ke a lokacin da kuka yi auren zuwa kammala karatun naki shekara nawa ne a tsakani? " "Duwaf kenan shekara uku da wata shidda cib da aurenmu, jirginmu ya sauka a Amurka. Ki fahimta a lokacin ban samu damar saƙa komai ba. Dalili kuwa shine Nazifi na ƙoƙarin bani lokacinshi ga kalaman soyayya da yake yi mun. Kana yana yawan nuna mun ma shi da ƙyar yake bacci dauriyace kawai yake yi. Sau biyu yana ja mun rai cewar zai zo daga baya zancan sai ya shiririce. Hmmm ina kai ku dai, Umma ta turo mun Yayata Kulu muka kwana tana harhaɗamun kayana kuɗaɗe na cire na sai ƙananun kaya masu tsadar gaske da kyau, ni a lokacin ma atampa uku na ɗauka, lesiri biyu, kayan burge miji Anty Kulu ta loda mun kawai in faɗa muku. Ƙaramin akwati cike da magungunan mata, na gida dana tada komaɗa kala kala. Washegari ta rakani har Abuja da yamma sakaliya jirginmu ya ɗaga zuwa Amurka Ya sauka a washington DC. Duk da sai da jirginmu yayi mana juye a burtaniya, muka huta muka ci abinci kafin muka sake hawa jirgin Washington DC ɗin. A taƙaice sai da muka kwana har muka kai rana kafin muka sauka. lamarin daya sauya mun tunani da rayuwa kenan. Amarya ta galabaita ta dahu sosai. Babban abinda ya tashi hankalina shine ganin Nazifi a cikin halin rashin ɗoki da zumuɗin ganina a matsayina ta Amarya fil a leda, ya dai riƙo wata uwar fulawa a hannunshi gari guda, yana tsaye ƙiƙam har na iso gareshi kafin ya buɗe mun hannu na shiga jikinshi muka sauke ajjiyar zuchiya. Ina kallon wata bahaushiya wacce muka hawo jirgi ɗaya daga Burtaniya ita nata gogarman fulawarma zubarwa yayi ya tafi a guje sukai kaciɓis a hanya, amman banda Nazifi. Mijin wata bana wata bane. Ko da muka shiga tasi zuwa gida shiru motar ta ɗauka kowanne cikinmu da tunanin da yake yi. Wallahi tun kafinma in ƙarasa gida naji nadamar baro iyayena da dangina ta kamani ƙaƙas, sabida na fahimci tabbas da matsala. A haka muka je gida ya saukeni har girki dai yayi mun amman fa babu wannan fara'ar da ita ta soma jana ga nazifi sai ɗaure fuska. Tambayar duniya yace babu komai aikine fal kanshi, shi yasa in yi haƙuri. Sai da na kwana ɗaya Nazifi ya ɗan sake. Babu karsashi a jikina. Ta ɓangaren mu'amala kuwa tun a daren na tsorata da salon Nazifi, ace saurayin da bai taɓa aure ba, bai taɓa sanin mace bane zai kasance a haka? Daren naci wuya sosai bai ragamun ba ina irin abunnan na saina fanshe wahalata da kuɗina, irin abinda Nazifi yayi mun kenan akaita Amarci ƙaƙas Ango ba fara'a babu nuna yabawa, a rana ta biyar da daddare ya shigo mun da ƙorafinshi da wasu sharudɗanshi duk akan mu'amalar aure fa. Shi yafi son mace mai sake jiki wayayya ta haƙiƙa, amman ni sai in dinga ƙin sakin jikina dashi sannan bana yi mishi kaza wa kaza wa kaza. Shiru nayi ina nazari har dai ya gama kafin nace dashi. "Ita mace da kunya aka santa sosai. Sannan inka duba ni ban sababa amman a hankali zan zo in saba, zaka samu abinda kake so tunda kaine malamin nawa" Sai ya haɗe ranshi wai kunsan wacce kalma ya jefeni da'ita maras daraja wanda yasa har yanzu ina kallonshi da wannan baƙin? Dukkanmu girgiza mata kai muka yi muna son ji. Murmusawa tayi ta girgiza kai tace damu. Cewa yayi . "Haba Saudatu kada ki raina mun hankali mana, kina nufin akwai wata mace da zata haɗa digiri ba tare da tasan kala_ kalan maza ba ne? Ke dai kawai wulaƙancine kawai ke damunki in zaki sake ki sake muci duniyarmu da tsinke kawai. Abubuwan da mu ka yi a baya mu ajjiye a gefe, muyi mai lada shine maganar gaskiya. Amman ya zan rayu a wannan ƙasar in koma gida da tunanin na samu wayayyar mace, daga ƙarshe kuma ki dinga nuna mun kamar baki waye ba haba ke kuwa. Kiga abinda kikai mun jiya harda amai kenan ƙyamata kike yi, ko me a gabanki nayi wanka kuma ko a fuska ai kinsan ni ba ƙazami bane, da wayewata ina likita mai daraja lamba ta ɗaya" A lokacin in da za'a tsaga jikina ba za'a samu jini ba daskarewa nayi kawai ina kallon Nazifi, ina gaban mamaki. Wato ashe da yawa yawan jahilan maza, irin kallon da suke ma macen da tayi jami'a kenan ko dai Nazifi bai same ni a mace cikakkiya bane? Kallonshi nayi na kira sunanshi nace. "Baka same ni a matsayin mace bane Nazifi, ko kuwa lissafinkane ya baka duk matar jami'a mazinaciyace, ko kuwa sabida kasan ka lalata mata bila adadinne yasa kake tunanin irinku su suka cika Jami'ar, harma kake hasashen babu wata macen Jami'a da zata tsira da mutumcinta?" A kausashe nake magana idanuna tab da ruwan ƙwalla. Hmmm cikin wata kwaɓar yace dani "Haba Saudat ke dai ayi sha'ani kawai, amman matan Jami'a ai ragowar laccarorine da abokan karatunsu. Nifa a jami'a mata ke bi suna roƙon in kwanta dasu, sai dai ba ko wacce take mun ba. Da wannan dalili na kafa hujja nake ji tamkar budurcinki bai cika na asalin budurwar da bata san komai ba. Kawai dai in zaki saki jiki ki dinga farantamun, kawai ki saki, ni wayayyene ina son harkar wayewa." Hawayen da suka cika guraben idanuna tuni suka shiga zuba a kumatuna, kaina da zuchiyata sukai mun dundurundun dasu yawu a bakina ya ƙafe. Naziru kuwa ko a kwalar rigarshi hankalinshi kwance yaita sarrafani yana ɗora hannayena a duk inda yake son in taɓa shi. Amman ina baƙin ciki gami da nadamar aurenshi sun hanani sukuni, a ƙarshe ma tureshi nayi a kaina na juya baya. Ranshi a wannan daren ya ɓaci sosai dan bai kwana a gidan ba ni kaɗai na kwana ina kuka, babu sallah babu salatin ma'aiki arrasul S A W, haka gari ya waye dani kaina kamar zai tarwatse tsabaragen ciwo. Ga gari ni bansan kowa ba, daga tawowa dawa zaka soma raba matsalar gidan aurenka? Nayi tunanin yin haƙuri in danne domun muyi zama na aminci da Naziru, sai dai abadan girmanshi ya gama zubewa bashi da wani kwarjini ko kima a idanuna sam. Dake nice mace kuma inason sanin daɗin aure, saina tattare komai na mayar dashi ba komai ba, na kuma saki jikina na dinga yi mishi abinda yake so, wallahi shafuka_shafuka na koyan mu'amalar aure iri_iri babu wanda bana shiga, in karanta in kuma kalli bidiyo duk dan in zama gwana kuma ƙwararriya a shinfiɗa, sabida na fahimci babu abinda yake faranta ran Naziru sama da mu'amalar aure. Duk da dai zuchiyata cike take da wasi_wasi da taraddadi amman ban tabbatar da gaskiyar abinda nake zargi ba sai wata ranar Juma'a da safe dana tashi da amai. Kuma ga zazzaɓin dare daya tusoni gaba a lokacin watana huɗu da zuwa. Muna zuwa asibiti gwajin farko akace ƙaramin ciki gareni sati biyar, yana cikin na shida. Matsalata a gidan naziru na farko kenan gagarumar matsala kuwa. Ni ina murnar
Chapter 66 · 0% Book details