← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 85

Sashe 39

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mace tayi sana'a ko aiki. Al muhim shine a duk inda take ta tsare darajar kanta a matsayinta na musulma, mace, matar aure, uwa, ƙanwa, ya, kaka. Shine kawai madamar mace zata tsare mutumcinta shikenan, tasan iyakokinta, ta tsare mutumcinta na musulma, ta kame daga hulɗa da mazan wajen aiki, ko mazan kasuwa, ta kama girma da darajarta ta ɗiya mace. Har kullum ina buga misalina da Layla, in kuma mace ƴar gwagwarmayar iya tallata kayane a barma FMK kayanta. Wai mata kunsan daɗin kuɗin kai kuwa? Da kin sani da kin kama sana'a kinyi adda'ar Allah ya dafa miki, da kin sani da kin yi aiki kin roƙi ilahi ya riƙa miki. Je ki bibiyi tarihin FMK, Layla Ali Othman zaki ɗauki darasi, ita Layla misalin bugawane ga zawaran da suke ganin ƙarshen rayuwane yazo musu shi yasa. Ku bibiyi tarihin Layla zawarawa sai ku sauke numfashi, a yanzu tana da Aurenta fa ato ( ranki shi daɗe ina miƙo gaisuwata💪🏼) Nayi rubutu mai jan hankali sosai kafin na sauka na ajjiye wayar tawa, nayo wanka na kwanta. Haka dai abubuwan suka ci gaba da tafiya rubutun da nayi jiya sai ya samu wani irin farin jinin da babu inda bai shiga ba, sai yaɗashi mata suke yi domin mata ƴan uwanmu su amfana da abinda na rubuta. Na fito da shirin fita aiki na tadda yaran na jirana duk sun shirya, sai lokacin na tambayi Mijinyawa, sabida banji motsinshi ba, ina fatan inji sunce ya tattara kayanshi, ya ɗauke gadonshi ya tafi. A lokacin Azgar ke faɗamun ya tafi Jama'are jikin Nanno ya tsananta sosai, shine aka kirashi suka wuce tare da su Yaya Zakiya, da suka kwaso jiki zuwa sunan Uwatale. Allah ya bata lafiya nace kawai na kwashesu na saukesu a makaranta nace dasu su wuce can gidanmu in an tashesu nima can zan wuto inna taso aiki. Hakan kuwa akayi daga wajen aiki kai tsaye na wuce gidanmu Luba kuma na barta zata shiga kasuwa zata siyo takalmi da jaka na sunan kishiyarta. Ina ƙoƙarin fitowa a mota wayata ta shiga ruri da baƙuwar lamba. Kamar ma bazan ɗauka ba dan lokacin anata kiraye_kirayen sallar la'asar maza sai wucewa zuwa masallaci suke. Sai da wayar ta kusan tsinkewa kafin na ɗaga. "Alhamdulillahi Malama Hindu Lantana ce ina ɗaya daga cikin memba ta zaurenki dan Allah in babu damuwa so nake ki sakamun lokaci in zo ko ofis ne in sameki, inaso zamu yi magana dake. Kishiyace za'ayimun kuma bazawara mai buɗewar idanu shine nake son a saka ni a hanyar mutumta kai" Ajjiyar zuchiya na sauke kana nace. Haba Lantana in dan wannan ne ai bama sai kinzo ba. Akwai rubuce rubuce da nayi a zauren da shafukana musamman na uwayen gidane, ai waɗannan kaɗai ya ishi duk wata macen da take son sanin hanyayin kare mutumcinta ko? " "Eh hakane duk na karantasu kuma na haddace, tare da ɗaura ɗambar yi, ina dai son ganin naki ne tafe da wata matsalar duk akan aurenne dai, dan Allah Malama ganin naki zai mun amfani, kuma zai sanyayani" To naji gobe ƙarfe uku ki kirani lokacin na taso aiki sai kizo gida ki sameni zan tura miki adireshin gidana" Godiya ta shiga jero mun gami da yima iyayena adda'a. Naji daɗin adda'arta ga su Innarmu sosai. Ina kashewa wayar mahaifin Jamila mai rasuwa ya kirani. "Ƴannan da fatan ban katse miki aikinki ba ko?" AA Baba ba damuwa, ya ƙarin haƙurinmu, da fatan kuma an dace samun hoton nashi Baba?" Baba yace. "To a gaskiya bamu samu ba wallahi. Ƴata inaso ki taimaka mana dan Allah. Mutuminnan mugune sosai. Bai yadda ya bar mana wani alama ba sam." Idanuna na lumshe nace. To Baba kwatanta mun yanayinshi, duk da nasan ba abu bane da zai yiwu ba. Amman ya yanayinshi yake?" "Yananan mai ɗan ruwane siriri haka, tsayin nashi ma ba can sosai bane." Idanuna na buɗe da sauri, wani abune yazo kaina. Am Baba yana da zane a fuskarshi haka, farine ko baƙine to?" Baba yace. "Yana da haske ƴata. Kuma kamar dai yana da kalangu a gefe da gefen kuncinshi, dake ba ƙura mishi idanu nake yi ba. Kinsan masu kuɗi da kwarjini" Kai na girgiza baƙin ciki na neman halakani da jin abinda yace. To shikenan Baba zanci gaba da bunciken, duk yadda ake ciki zan sake tuntuɓarka" Da haka na sauke wayar. Nayi shiru ina dogon nazari, na buɗe wayata na duba abu, na kulle idanuna nayi nazari kamar na ƴan mintina, kafin na buɗe idanun nawa. Sakkowa nayi, na rufe motata na shiga gida da sallama. Duk matan gidan kamar suna can cikin gida a nan nake jin hayaniyarsu ko me akayi kuma sai Allah, ni da nasan ma haka zan zo in tarar da gidan da gidana na wuce ya fiye mun. Ko in bi Lubana kasuwa. Ina shiga lungunmu na gane a lungun Baba dogara ake wani abun, gasu Innah Mairamu can muryarta tafi ta kowa tashi. Gidan yawa babban masifa kai Allah ya rabamu da gidan gandu, babu daɗin zama, babu sirri, ƙyas ake jirace da kowa. Falonmu na shiga na tadda wata shariar aketa fafatawa an cika an cika. "Yauwa ga Hinduwan ta ƙaraso. Ke Hindu zo ki zauna ayi wannan maganar ta ƙare kawai, nagaji da yadda aketa mayar da wannan maganar babba, da wani sharrin dai ake neman mu, duk yadda akayi." Cewar Innarmu da suke zaune a gaban Baba Sojanmu, ga Salamatu, ga Yaya Saratu, ga Habiban su Salamatu, ga Yaya Zakiya, ga Khadijan Innah Mairamu, ga Sailuban Baba alƙali. Su Innah Abida duk suna zaune. Waje na samu na zauna ni da Salamatu muna fuskantar juna. Harara ta sakar mun harda tsaki marar sauti, ni kuma nayi murmushi tare da girgiza kaina irin na cusa haushi. Ashe Baba Sojanmu akan gidanshi akayi komai yana kallonmu yana nazartarmu. Can yace. "Ke Salamatu me Hindu ta rubuta miki da aketa abu ɗaya yau kwana biyu magana taƙi ƙarewa, ga gida ya soma ɗinkewa da baƙin nesa. Wannan wacce maganace da girmanta yakai a kwana biyu ana yinta, duk lungunan gidannan ya ɗauka zance guda ɗayane Hinduwa tayi kaza, Hinduwa bata kyauta ba. Me Hinduwannan tace ne, inda babu ƙasa anan ake gaddamar kokawa" Innah Abida na kalla na dubi Salamatu dake ƙoƙarin soma magana. Ni dariya ta bani wallahi, sai kace wata ƙaramar yarinya. Ko da yake Innah Abida ma haka take yi. "Baba Sojanmu daga na turo hotunana da mijin da zan Aura shine Hindu take cewa gashi ɗan tsurut a gabana. Kuma dama tunda aka kawo akwatina suke ta nuna abubuwa, ga Innah ai tana ganin komai. Hatta Innah Ruwayya ma sai habaice_habaice take saki a falonnan. Daga magana a zaure, su Saratu suka goyi bayan ita Hindun. Rikicin da yaƙi ƙarewa dama a zaure ne ake ta sake tayar da zancan" Ta ƙarashe tana huci harda runtse idanu, dama muguwar mafaɗaciyace hancinta mai zufarnanne na mafaɗata. "Shikenan iyakar bayanin ko akwai wani?ki gama kab inajinki, wannan lamari ace harda dambe tsakaninki da Zubaina, gotai_gotai dake. Ke kuma Zubaina zaki ci gidankune. "Ta nawa ɓangaren akwai wani. Tun jiya da ƙannena su Ladidi suka ƙaraso Ruwayya take harararsu, tana musu wani gani ganin da dama can ta saba muddin ƴan kwantagora zasu zo, saita nuna ƙyamarsu a fili. Abinda yayi ni, shi yayi ka. Su Ladidi ƙanenka ne kuma ƙannenane ta ko wanne ɓangare, danme su da gidan wansu ba zasu zo a wanye da matarka lafiya ba? " Kafin yace wani abun sai ga Goggo Shirwa ta ƙaraso yayar Baba Sojanmu ce daga ita sai Baba Alƙali. "Haka su Ladidi da Talatuwa suka ce, tunda suka shigo falonnan Ruwayya take kallonsu ɗaiɗaya, ni da sabida ita da yaranta da basa ganin mutane da gashi wallahi banso zuwa bikin ba. Sabida ita ko kwantagora tazo biki saita raina mana arziki, bare mun biyota har fadarta. To fadarta mana A gaskiya Soja Ruwayya matarka bata fiye son a zauna lafiya ba. Kuma a kan turbar data ɗaura yaranta kenan. Ba dai kaga su Saratu sun shigo cikinmu sun zauna a sake ana hira ba. Sai dai su shigo a gaisa kawai sunfi gane su haye gadon uwarsu suita shewa, kasan wannan jini na Maiduguri na yawo a jikinsu matan Maiduguri raini garesu sosai, ga girman kan tsiya." Goggo Shirwa haka dama take duk sanda tazo wani sha'ani na gidannan in sha Allahu sai sun tunzura Innarmu. Bance laifin nasu bane susu kaɗai ba. Innarmu ba mace bace mai haƙuri ba, kana ba mace bace wacce in akayi mata ba zata rama ba. Sa'a kaɗai mutum zai taka har ya yar da magana ta ƙyaleshi. Amman bata hargowa da ihu cikin sanyin murya da murmushi zata rama baƙar maganarta, wanda ke kusa ba lallai ma yaji muryarta ba. Amman nasan kab dangin Baba Sojanmu basa ƙaunarmu ta dalilin ƙin Innarmu da suke yi. Shi kuma yaro bazai taɓa shiga inda kullum kyararshi da aibata mahaifiyarshi akeyiba. Wannan shine musabbanin da ko sunzo sun sauka a ɗakin Innah Abida iyakarmu dasu gaisuwa. Innarmu ma da taga mun jima bamu fito ba zata kwaɗama yaro kira ya dawo ɗaki, ba wanda take jin tsoro. Kuma ita kanta Innah Abida sau nawa ta sha korarmu in mun shiga ɗakinta, lokacin muna yara. Wannan tun muna yara kenan fa ake abu ɗaya duk akan rijalu. Baba Sojanmu yace. "Amman Yaya Shirwa ni banji wata magana mai zafi da Hindu ta faɗa da har zai kawo rikicin da za'a kwana biyu anayi ba. Shin mijin ba ɗan tsurut ɗin bane? Nima fa da kaina nace da Abida shi kuma mijin Salamatu haka yake ƙanƙani, gata ai. Ke Ruwayya me kike dashi na cewa akan wannan maganar? " Goggo shirwa saita juya ta wuce ɗakin Innah Abida tana zage zagenta. "Hmmmm ƙauyanci yaƙi sakin Shirwa, gata dai gotai_gotai ji yadda take tafiya bagazan_bazagan. Innarmu tace. "Ban dai sani ba ko su yaran suna da abun faɗe tunda rikicin nasu ne bana iyayeba. Amman banga wani abun faɗe da zance ba" Baba Sojanmu yace. "Ke Hinduwa me kika rubutoma ƴar uwarki? " Wayata na ciro na dubo rubutun da nayi na karantoma kowa, na kuma nuna ma Baba Sojanmu ya gani, ya
Chapter 39 · 0% Book details