← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 85

Sashe 76

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Yana tashi daga aiki ya juya akalar motarshi izuwa gidan Mijinyawa Babba, da tunanin acan zai ƙarashe ƴan kwanakin da suka rage mishi, kafin ya bar garinma baki ɗaya.
Ya jima yana matsa hon,
Mijinyawa Babba ne ya leƙo ta ƙaramar ƙofa. Ganin mijinyawane hakan yasa ya koma ciki.
Kafin can mai gadi ya fito ta ƙaramar ƙofa.
"Baban Azgar ashe kai É—inne? "
"Nine Yahuza buÉ—e mun in shiga daga ciki."
Jim yayi kafin yace.
"Wallahi bansan me zance maka ba ma. Yanzu haka motar ɗiban kayan ɓarayin Mamansu Azgar tana tsakar gidan kwashe kayan akeyi. Dama na ɓarayin ita Asama'u Nanno tasa an kwashe ba tun yanzu ba.
Sannan É—an uwanka ya bani umarnin karma in barka ka sake shiga.
Dan Allah kayi haƙuri, nasan abun babu daɗi. Ni kaina abun yayi mun nauyi sosai, amman ya zanyi."
Murmushi Mijinyawa yayi ma Yahuza.
"Ai babu komai Yahuza. Ita rayuwa haka take.
Babu matsala bari inje"
"Ka tsaya yace dani ince maka zai fito. Au kama ganshi ya nufo mu"
Ya nuna mishi Mijinyawa Babba da yake nufosu.
Shiru yayi kawai, yana sake ƙarema ɗan uwan tagwaitakar nashi kallo, har ya iso gareshi, ya dafa tagar motar tare da zura kai ciki.
"Ashe baka ji gargaɗina ba Magawata? Lallai ka ɗauka wasane, ai muddin Hindu matarka ce, ni da kai ya ƙare abadan.
Uwatale har yanzu jinin daya taru a idanunta bai baje ba. Nanno yanzu bata iya takawa sai da sanda, Yaya Jamila kuwa jikinta har yanzu yaƙi daɗi. Sabida kaine ɗan daɗi Hindu, kace aljanunta ne suka yi, ba ita ba.
Kawu ya goyi bayanka, ai shikenan ni dai na sallama. Nanno dai tace ta yafe maka, ba kuma zata yi maka baki ba.
Amman muddin da ace bakina zai bika, wallahi saina lalataka da bakina, na tsinema albarka daga kai har zuriyarka."
"Kace haka bama sabida kana baƙin ciki da samuna, ni da matata ba?
Ban taɓa tunanin in kowa zai juya mun baya har dakai ba Nawata.
Tur da Uwatale wacce ta zama wasila ta faruwar wannan tashin hankalin.
Batun tsinemun da kake yi da zuriyata kuma, kash gashi ba kai bane ubana ba. Ni da kai duk haifarmu akayi.
Kuma na gane girman hassadarka, kai da matar akanmu.
Wato a ƙarƙashinka kaso muci gaba da rayuwarmu ko?
Sai kaga Allah yayi mana liɗifi shine cutar hassadarka ta motsa, a baya ma bata motsa bane sabida a ƙarƙashin inuwar arzikinka muke.
Ashe wannan ne dalilin da yasa duk sanda zan ma batun siyan fili, sai kace kai baka yadda ba, kai in faÉ—ama in Uwatale ce tayi mana wani abun. Kai in ba zumunci zan yanke dakai ba in zauna tare dakai.
Ashe duk ƙaryane, sha'awa kake yi ka ganmu muna ƙarƙashin alfarmarka. Kaji kunya ka yaudareni, kaci amanata. Amman Allah zai sakamun in sha Allah"
Sun yi rikici da musayar kalamai masu zafi, da ɗaci sosai. Daga ƙarshe motar kayan Hindu ta fito a gidan.
Kai tsaye Mijinyawa yace motar tabi bayanshi.
Wajen Æ´an kayi nayi masu shago ya kai kayan kawai.
Nan kuwa suka yi siyan wulaƙanci sababbin kaya masu darajar gaske amman milliyan biyu kacal suka siya gabaki ɗaya.
Bai ja da yawa ba, sabida ranshi a jagule suke, kayanma baya ko ƙaunar ya buɗe idanunshi ya gansu, sabida tunanin abubuwa da yawa.
A akawunshi suka sanya mishi kuÉ—in, ya sallami masu mota, kai tsaye Hotel ya wuce, ya kama É—aki ya shiga ya kwanta.
Shiru yayi, dan a lokacin baya son hayaniyar komai da kowa. Jijiyar gefen kunnenshi aiki kawai take yi, ta kumbura ta cika, haka tai ta yi.
Kunnuwanshi wani irin ƙara kawai suke yi mai, yayinda zuchiyarshi ke wani irin harbawa wanda ya wuce ƙa'ida.
Idanunshi a lumshe suke rub.
Gaga_gaga_gaga_gaga.
Chapter 76 · 0% Book details