Sashe 62
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Mrs BUKHARITSURON TSIRIN..
TSANDAURI...
LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI.
LAMBA TA KOMA SHA BAKWAI (17)
✨ SABON TURAREN WUTA. ALFARMA DA ƘAMSHIN CIKIN GIDAN DARAJA.
OUD AL MALAKI ✨
Kuna neman ƙamshin da zai canza yanayin gidanku, ya dawo kamar fadar sarauta? Ga sabon haɗin Turaren Wuta na musamman da kowace mace mai aji ya kamata ta mallaka don burge maigida da baƙi.
Inganci Na Musamman
Yana da inganci sosai, zai fitar da ƙamshi mai daɗi da taushi, a yayin ƙonawa.
Ƙamshi Mai Kafuwa Hayaki kaɗan a kan garwashi zai mamaye kowane kusurwa na gida, yana zama a cikin labulaye da kafet na tsawon kwanaki.Mazubi Na Alfarma, Ya zo a cikin kyakkyawan mazubi mai adon lu'u-lu'u da kristal wanda zai ƙawata gidanki Hajiya
(Farashin wannan turare shine 25k ne)
Mijinyawa:.
Yana fitowa daga É—akin Hindu, falo ya nufa kawai ya zauna ya kasa zama, yana tsaye a waje É—aya yayi shiru kanshi na sarawa tamkar zai tarwatse.
Can ya goya hannayenshi a bayanshi ya shiga safa da marwa, yama rasa tunanin me zaiyi lissafi ya ƙwace mishi baki ɗaya. Hindu ta riga da ta kaishi ƙarshen_ƙarshe ya rufe babinta kwata_kwata ko da hakan na nufin mutuwarshi ne. Shima bawai bai iya taurin kan bane ba, aa abubuwan da suka faffaru na sadaukarwa iri_iri da tayi mishi wanda ne, wanda a tsarin rubutun layi baizo kansu ba shi yake dubawa kawai, yake ɗaga ƙafa, kuma ya doge yake son kare Aurensu. A baya ita ta kare musu Auren, sun so su faɗi su rushe, Hindu ta cicciɓosu tace. A'a ba zamu faɗi ba da izinin Allah, zamu rayu abadan.
Ajjiyar zuchiya ya sauke, ya girmama taurin kan Hindu, da baƙar zuchiyarta wacce ta shafe dukkannin alkhairanshi, akan laifi ɗaya ko kuskure ɗaya. Duk da yasan laifinshi yana da girman zunubin da dole Hindu taƙi yadda dashi a karo na biyu. Yasan ba ita yayi ma laifi ba, kuma ya roƙi Allah gafara, yasan Ubangiji mai rahamane mai jin ƙaine, ya yafe mishi. Yana neman yafiyar cutar da zuchiyarta da yayine, da yaddar data bashi ya karya. Da amanar abokinshi da yaci, ya lalata Asama'u da yayi, yayi mata fata_fata da rayuwarta.
Masu iya magana suna cewa tsalle ɗaya akeyi a shiga rijiya, amman sai ayi dubu ba'a fito ba. Haƙiƙa zina bala'i ce zina ƙazantace, zina saɓama Allah ne.
Tunda ya aikata abinda ya aikata, bai sake samun nutsuwar zuchiya data gangar jiki ba, aikin nashi ma ba maida hankali yake yi ba, ga rigimar Hindu da shirunta da yake gasa duniyarshi.
Zuchiyarshi ce ta bijiro mishi da wata tambaya data gigita tunaninshi.
Yanzu Mijinyawa inka tafi ciwon Hindu ya tashi wa zai iya kularma da'ita, bayan kasan da irin sharaɗin da iyayenta suka amince da aurenku, Hindu dai inka rabu da'ita ba gidansu zata koma ba zamanta zata yi a gidanta, ka zaɓarma uwar ƴaƴanka zaman kanta kenan koko yaya? "
Zuchiyarshi ce tai mishi wannan tintuntinin, sabida girman soyayyar Hindu.
Yasan shi wawane akan soyayya, kuma shi da Hindu sunyi wata iriyar shaƙuwar da, rabuwa da'ita a ƙanƙanin lokaci ba abu mai sauƙi bane. Kuma yasan ta fishi jarumta, amman tabbas yasan itama tana gasuwa iyakar gasuwa. Babu shiri ya sulale ya zauna a saman kujera, yasa hannayenshi biyu bisa kanshi ya tallafesu a fili ya furta
"Hindu me yasa zuchiyarki take da tauri tamkar tsandauri, da mance alkhairi akan kuskure guÉ—a É—aya rak da kika kama mijinki dashi? Gashi a dalilin taurin kanki kina son ruguza mana iyalinmu, ki ruguzamun nutsuwa da walwalar yarana ya Allah"
Wata zuchiyar tashi ta tare shi da cewa.
"Amman Hindu tana da gaskiyarta, domin anyi mata cin amana ƙololuwar gaban mamakin da ya wuce ace ta yafe a iyakar fatar baki kawai.
Ka saketa kawai sai kafi mutumci a idanunta, muddin kaci gaba da riƙe igiyoyin aurenta ma kaida shawo kanta a irin zuchiyarta har abada, kenan rayuwarku zata wanzune cike da ƙunci da ciwon ruhi mai raɗaɗi. Amman in kuka rabu shikenan zaka auri wacce zata ga mutumcinka, itama ta auri wani mijin da zata mutumtashi kamar dai yadda take yi maka a da wannan shawarace. Amman samun mace irin Hindu ba abu mai sauƙi bane, kafi kowa sanin wacece Hindu, ya son da take ma yake. Kuskure anyi. Kuma kai ka rushe gidan gaskiya. Ka saketa kawai, ka saketa"
Haƙiƙa yasan duk abinda zuchiyarshi ta faɗa mai gaskiyane, domin zuchiyarshi itace shi tafi kowa gane karatun damuwa da ƙuncin da suke karantawa tare, kuma yana ganin shawarar daya tsayar kenan na sauwaƙema Hindu ya kwashe yaranshi ya nisanta da ita,ko Allah zaisa watarana albarkacin yara ta huce, in shan ruwan Auren bai ƙare ba sai a dawo, in ya ƙare shikenan sai ya gina sabuwar rayuwa, itama ya bata damar gina sabuwar rayuwa. Gara a rabu cikin mutumci, bama zai yadda a shiga kotu dashi ba. A rayuwarsu bai taɓa zato ko tunanin akwai wani dalilin da ka iya zuwa ya raba wannan auren ba, ashe akwai ranar da zata zo Hindu ta rufe idanunta ta runtse taji ta tsaneshi akan laifi guda ɗaya, ba laifuka birjik ba. Yadai sani abadan babu wata mace da zata iya ture matsayin Hindu a zuchiyarshi, kamar yadda aka rasa macen da zata iya hawa matsayin iyabo tsuntsun soyayya a zuchiyar Gwadabe. Yana ma Hindu fin son da Hamma ya nuna ma Iyabo. Hindu ta mishi fin son da Iyabo tayi ma Hammanta.
Idanunshi da suka soye yake jinsu inya ƙibta tamkar zasu yage, ya lumshe a hankali wani raɗaɗi ya tsirga mishi har cikin zuchiyarshi. Shiru ya kwanta a saman doguwar kujerar yana sauraren zuchiyarshi, dake aikin watsa jini zuwa gangar jikinshi da sauri sauri.
Ya jima gaya a cikin wani irin yanayi daɗewar da shi kanshi baisan iyaka ba. Alwala kawai ya ɗauro sabida bacci ya ƙaurace mishi sam, sai wajajen huɗun asubane da sanyin asuba ya soma ratsa duniya ya sulale akan sallayarshi kanshi da zuchiyarshi suna shirin yin bindiga.
Azgar ne ya leƙo falon ya tadda mahaifin nasu a kwance a ƙasa ya takure kamar marar lafiya, take tausayinshi ya dirar mishi ya ƙarasa kusa dashi daf ya tsugunna. Taɓa jikinshi da yayi yaji zafi kau, gashi babu ishasshen lokaci sun kusan makara ma zuwa sallah.
"Abba lokacin Sallah yayi ka tashi, Abba kayi haƙuri zan baka wata shawara ka ɗan bama Ammi lokaci zata huce. Amman Abba ka koma can gidan Baba Babba kaci gaba da zama. Zan yi iyakar iyawata inga kun daidaita da Ammi, kuma nasan yadda zanyi kaji Abbanmu? "
A raunace idanu tab da ƙwalla yayi maganar, yasan Ammi ce ta caza mishi kanshi tunda shi dai yasan a ɗakinta ya barshi.
"To Azgar bari in yi alwala kaga bansan sanda bacci ya kwasheni ba, sallah nayi akan inna idar sai in shiga ciki. Batun sasanci ka bar wannan zancan kada kace ma Amminku komai. Kar ka tunzurata Azgar, rabu da'ita zan tafi bama zata sake ganina ba in dai na bar cikin gidannan. Ya kuma isa haka, ya isa haka Azgar."
A hankali ya miƙe ya fita, Azgar ya fito dokin ƙofa yayi tsaye har mijinyawa ya fito suka wuce masallaci.
Sai kawai yaji alƙiyamarshi ta tsaya jin furucin Abbansu.
Hindu:.