← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 85

Sashe 50

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI

LAMBA TA SHA UKU (13)

Aimun afuwa na samu kuskuren lambane, nayi lamba ta takwas har sau biyu, jiya lamba ta sha biyu ya kamata in rubuta saina rubuta lamba ta sha É—aya Afwan dan Allah

Ajjiyar zuchiya Luba ta sauke tare da cewa.
"Haƙiƙa nasan inda Hindu take mijinyawa, amman kayi haƙuri zuwa gobe zaka ganta ta dawo gida wani ɗan abune ya taso kayi haƙuri, amman tana ƙasarnan cikin garinnan namu mai albarka na Kano"
Ɓoyayyar ajjiyar zuchiya ya sauke yaji sanyi mamaye da zuchiyarshi jin Hindu na ƙasar cikin garin. Amman haƙiƙa ya zame mishi dole yasan inda take me kuma ya faru.
"Dangane da taimakon ka da kake son nayi dan taya ka shawo kan Hindu, a gaskiya ni shawarata anan shine ka ɗan nesanta da'ita, ka bata waje ta sha iska sai inga kamar zata yadda tayi haƙuri ta yafe maka, kuci gaba da zumunci. Mijinyawa bari kaji kaganni ko nice Sunusi yayi mun irin abinda kaima Hindu, ta reni ɗiya ka aureta a ƙarke, to na gama auren dashi abadan. Abune mai wuya Hindu a irin sanin da nai mata ta yadda ta zauna dakai a gaskiya. Amman ka jarraba bata iska. Wannan dai shine".
"Luba ki yi ma Allah, domin darajar Allah ki sanar dani ina Hindu take a wanne halin take? Na roƙeki dan Allah. Sannan in bata waje zai sa ta sakko, Luba a shirye nake, dama nayi tunanin hakan ko dan in sama mata farin ciki ko dan sabida su Nanno, ke kinsan abubuwa da yawa ai.
Amman Luba ni É—in komai zai iya faruwa dani.
Ki gane Hindu tayi mun irin sadaukarwar da ko Nanno a girmana dai ba zata iya mun ba, ballantana ƴan uwana. Akwai dalilan da yasa lallai na damu da rarrashinta, nake son ta haƙura Luba. Allah shine shaidata inna haƙura na biye ma Hindu muka rabu, Luba nayi mata zalunci mafi munin zalunci. Kinsan abubuwan data sadaukar domina kuwa?
Ko da yake ku kun É—auka tamkar maza basu san ai musu karamci ba ko Luba.
A tunanin mata da yawa namiji ba É—an goyo bane ba ko Luba.
A tunanin da yawan mata mu azzalumaine waÉ—anda kawunanmu kaÉ—ai muka sani ko?
Wallahil azeem ba haka bane, ba haka muke ba jostis fo rijalu Luba. Duk ɗan halak yasan halacci, duk ɗan halak ɗin da matarshi ta sadaukar dominshi Luba ya sani. Kuyi kwalliya dominmu mun sani, kuyi girki mai daɗi dominmu mun sani, ku yi cikon cefane mun sani, kuyi kitso ko ƙunshi mun sani, duk abinda mace zata yi dominmu idanunmu yana kai. Kuma tana tarin ɗunbun ladanta ita a wajen Allah.
Wallahi firejar aikin yau da gobe ke sa wasu mazan da yawa kauda kansu, badan basu gani ba, ba dan basu yaba a zuchiya sunji daÉ—i ba. Firejar tana da yawa. Wani daya shigo gida dukkkanin wata gajiya sakko mishi takeyi Luba. Wani ma magana wannan baya so ai mishi sai ya huta, kanshi ya É—auki caji, kune kaÉ—ai kuke iya saukemu fa.
To a cikin mata na faɗa na kuma Hindu ta dabance. Ko wanne namiji tai mai sadaukarwar da tayi mun, bazai iya rabuwa da'ita sasakai ba wallahi. Ta wuce ƙashin yadawa."
"To Mijinyawa duk kasan da haka me yasa ka auri Asama'u? Ka gane ba ƙarin aurenka bane ya zama matsala a garemu ba. Wacce ka aura itace matsala. Haba mijinyawa ai ana barin halas dan kunya. Ko da yake wannan karatun malamai sunce kuskurene, kuma a wajenku kuskurene. Bazance Hindu ɗari bisa ɗari take ba ajizace. Amman ƙoƙarinta ba duk kai ba. Bazance zata zame maka uku a ɗaya ba ta yadda zaka kauce ganin wasu matan ba, ko aurosu ba, itama bata jayayya da ikon Allah. Macece mai tawakkali, da miƙa lamuranta ga rabbil izzati. Amman in zaka auro mace sai ka auro macuwat wacce zata dace da Hindu, azo a buga a kwashe, wacce ta biya allonta sai ta wanke. Sabida lokuta da dama yaran matan duk bulace, a waje dai soyayya ƙaƙas, yarinya data soma haihuwa fa magana ta ƙare."
Murmushi yayi ya dubeta.
"Luba ki bar aikin ƙaddara. Kuna wasa da ƙudurar Ubangiji, da kuma rubutaccen al'amarin Ubangiji. Ke dai nayi kuskure kuma ɗan ba ƙara"
"To shikenan rubutaccen al'amari ba? Hindu tana ofishin Æ´an sanda a kulle. Sanadiyyar taimakon wata baiwar Allah da tayi. shine mijin ya haÉ—a harda matar tashi ya kullesu.
Wayarta na hannuna motarta kuma tana wajen aikin mu. Kayi haƙuri itace ta buƙaci bata son a sani ciki harda kai. Kaga abinci na tusa a gaba amman wallahi sam na kasa ci tunaninta kawai nake yi"
Kai ya dafe yayi shiru na lokaci mai É—an dama.
"Nagode Luba zanje in sameta mu yi magana, dana sani da wuri ai ba zata kai haka a kulle ba."
Yana kaiwa nan ya fice da sauri lo bi ta kan Sanusi bai yi ba ya shige mota, sai ofishin ƴan sanda na wajen. Da sallama ya shiga ya sanar dasu wacce yazo gani,ƴan dokar suka shaida mishi dare yayi sai dai gobe ya dawo. Ya buƙaci belinta ma shima suka ce gobe ya dawo bazai gagara ba duka. Yana ji yana gani, ya baro ofishin ƴan sandan da zummar asubar fari ma a wajen zata yi mishi a bashi belin matarshi, inma kotu za'a shiga koma menene shi zai ɗauki sintirin yi da kanshi. Abinci ya siya musu na mutum biyar harda nama da ruwa. Nanma saida yaita roƙo suka amince zasu miƙa ma su Hindu abisa sharaɗin sai yaci a gabansu sun gani kamar yadda ƙa'idar take, haka dole ya ci loma ɗaɗɗaya ya kama loma biyar, kafin suka amince suka kaima su Hindu wannan abinci.
Yana hanyarshi ta komawa gidane Mijinyawa Babba ya kurawo wayarshi idanu kawai ya lumshe tare da É—aga wayar.
"Ina kuka shige da kai da matar taka Mijinyawa? Gani a gidan naka na kawo ma su Nanno Abinci, yanzu iriyar rayuwar da kuka zaɓama kan ku kenan aikin jarida haukane dama bamu sani ba? Kuna ina yanzu nace? "
"Ina hanya na kusa isowa."
"Ita kuma Hindun fa shafaffiya da mai?"
"A_a Mijinyawa kar muyi haka da kai. Kai ka sani bazan taɓa aibata maka matarka a kunnenka ba, ko da kuwa mai ta aikata maka kuwa. Bai kamata ka biye ta su Yaya Jamila kaima ka shiga gaba a sahun masu kushe mun mata ba. Yana da kyau ku san bafa haifata kuka yi ba. Ya kana neman zaƙewa da yawa, sabida munafukar matarka tayi maka huɗuba ko"
"Yayi daidai"
Cewar Mijinyawa babba. Mijinyawa yace
"Ƙwarai kuwa yayi daidai, yadda kake jin Uwatale a ƙoƙon ranka, ina jin fiye da haka a kan Hindu. Wai me Hindu ta tsare muku ne da kuka tsaneta? Kuma abu mafi zafi ace harda abokin tagwaitakata. Ko da yake matarka kake biyema shi yasa duk kabi ka sauya mun. Amman ni da kai mu zuba in dai akan Hindu ne. Inna ƙyale su Yaya Jamila, da Yaya Zakiya wallahi bazan ƙyaleka kana sakona kaci kashi akan matata ba. Turar kowa ta kaini bango, nagaji abu kamar cin ƙwan makauniya"
Sai jiyo kukan Nanno yayi gami da salatinta tana ambaton
"Ɗan uwan naka wanka kake caccaɓama magana, akan wannan baƙa gajeruwar matar taka, wacce yara biyu kaɗai kuka haifa baku haifi duniya ba? ".
Wayar ya kashe yana ji tamkar ya ciro zuchiyarshi ya yayyafa mata ruwa tsabaragen zafin da take yi mishi, abu ya gwale mishi goma da ashirin cikin taimakon Ubangiji ya samu ya shigo gida dan gabanshi wannan dishi_dishi yake gani tsabar fireja.
A tsakar gida yaci karo da mijinyawa Babba da Gambo. Ƙarasowa yake son yayi su gaisa da mijinyawa, amman shi yinƙurin ficewarshi yake yi, yayi mishi banza kamar bai ganshi ba.
Bai daddaraba yaje gabansu tare da miƙa mai hannu bakinshi ɗauke da sallama.
Ya dai amsa mishi sallamar hannun dai bai miƙa mishi ba, haka suka wuce suka barshi saroro a wajen.
Cikin gidanma babu daÉ—i nanno tafi awa guda tana zazzaga mishi ruwan faÉ—a, Yaya jamila tana sake ingiza lamarin abinka da É—a da uwa sai ta sassauta da taga yadda duk ya birkice idanunshi suka sauya launi.
"Kiyi haƙuri Nanno laifin nawa ne shaf na mance Hindu ta faɗamun zasu yi wata ƴar tafiya daga wajen aiki, har saida na kirata a waya tukunna na tuno"
"To shi fitar da kayi ka jima aina zaci nemota kaje yi. Matarka ta bar gidan dai sabida zuwanmu ƙiri da muzu Hindu ke nuna bata son mu raɓeka, tabi dukiyarka duk ta handame tayi kane_kane har umara Hindu taje da kuɗaɗenka kai baka je ba, ni baka kaini ba bare ace na neman ladane ko, amman ita shafaffiya da mai har mota ka sauya mata ayi magana kace ita tasiya da kuɗinta alhalin uwatale ta faɗamun ma'aikatan gidajen rediyo albashinsu bai kai ma nasu Uwatalenba su ma'aikatan jinya ba. Ita uwatale banga ta sai mota ba, banga taje umara ba ko suturar da take sawa bata kai ta matarka ba ai. Dan ko ranar da muka zo, wannan yarinyar tace mun zinare ne a kunnen matarka, atampar jikinta mai tsadar gaske ce.
Wallahi Mijinyawa kaima kanka karatun tanutsu ka kiyayi duniya, ka kiyayi matarka. Uwatale tayi gaskiya"
Kasa cewa yayi uffan. Dama yasan Yaya Jamila da Uwatale su suke sake cusama Nanno ƙiyayyar Hindu, ta hanyar farfaɗa mata ƙarairayi da gaskiya bai ɗaya.
Haƙuri yaso bata amman ta hanashi, hanyar waje ta nuna mishi bai musu ba ya fita kanshi na sara mishi tamkar zai tarwatse.
A daddafe ya duba su Azgar ya tabbatar sun ci abinci kafin su kwanta dai ko. Kana ya shaida musu Ummansu tayi tafiyane amman ba zata wuci gobe zuwa jibi ba zata dawo. Ya umarci yaron da yayi ƙoƙari gobe in su Nanno sun tafi, ya haɗa mishi duk kayayyakinshi a akwati, ya ɓalle gadonshi ya jingine mishi.
Abinci Azgar ya taso ya bashi a tire shayine mai zafi da jallof ta taliya mai bushasshen kifi. Godiya yayi ma yaron ya shige ɗakin Hindu, tare da rufo ƙofar😆
Chapter 50 · 0% Book details