← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 85

Sashe 70

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

wanda basa yi mana. Ni a lokacin ne na gane girman ƙyama da al'umma tayi mana. Ko kuma ince ana sonmu a tv, anason ganinmu kuma, amman ba'ason a auromu sai mu zama bare tamkar ma ba musulmai ba. Kuma a hakan har zuwa kallona akeyi, ana murna in aka ganni, dole in musu fara'a in tarbesu, ga damuwa ni fal raina. Wallahi yaran Asabe har zagina suke yi a idona suna ce mun ƴar film mara tarbiyya, dake yaran ƴanmatane kuma mata, bana ko son fitowa mu haɗu babban abinda ke haɗamu Kicin. Kowa na da Kicin a ɓarayinshi sai babban Kitchen a tsakar gida babba sosai, cikinshi da ƙaton suto shaƙe da kayan masarufi. To anan ko wacce in ta shiga girki zata yi, kuma girki a haɗe. Asubar fari ran kwanana zan zare jikina in nufi Kicin, gashi ƙa'idar gidan abun tuya akeyi da safe, doya, dankalin hausa, dankalin turawa, sai ƙwai da ya zama dole. Kuma zaki yi cincin ko mutufib, ko fanke da yara sazu tafi dashi makaranta. Hmm to wannan ma kullum zai shigo yaita azalzalata, Asabe kuma ta dasa mita duk in birkice basa dubamun, cewar ni ba sabawa nayi da hidimar kowa ba, lokaci ɗaya hidimar yara bakwai gani,ga miji, ga kishiya, ba abu mai sauƙi bane. Tunda ko ita Asaben ai da sannu sannu aikin yaita hawa kanta ba lokaci guda bane. Amman sunƙi fahimta sam, duk da itace ke kambaba abun da'ita da babbar ɗiyarta. To mu dawo inda na tsaya cewar na tareshi da batun bikin Taraba. Dana tambayeshi. "Ashe za'ayi biki a Taraba shine ba'a faɗa mini ba, bare in soma shiri." Ai wallahi kamar na ɗana mishi wutane. "Menene amfanin sanar miki tunda ko an sanar miki ba zuwa zaki yi ba, ke da kike ƙyamar dangina? Asabe ce ta dace dani, kuma itace ta damu da dangina, da yarana ai. Wai ke da na Auroki na rufa miki asiri, yau ni kike tozartawa Mariya? To babu inda zaki je, suma dangina basa fatan ganin ƴar film a cikinsu ke baki san da yadda akayi auren naki bane. Na gama gajiya da ɗabi'unki, da yadda kike ma iyalina gani_gani, ga barin yara da yinwa da kike yi, kullum kekenan a cikin yin lattin girkin safe, da rana ma sunce har su dawo bakya gamawa, sai wajen huɗun yamma kike gama girki, na dare kuwa sai bayan isha wataran har gaba da isha kike kaiwa nima ina gani ai. Wannan shine tsiyar auren ƴar film. Baki iya uban komai ba sai rawa" Ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba wallahi. Ya barni in yi magana in wanke, kaina abu yaci tura, ya barni in bashi haƙuri ma, yaƙi yadda sai fuffuka yake yi. Ni kuma ƴar adam ce kamar kowa kuma babu ta inda ya zama ratayayyen hakki a kaina yima matarshi da yaranshi hidima. Sai naji na kawo wuya haƙurin da nake bayarwa na ja bakina nayi shiru kawai. Daga ranar yadda kuka san an mana farraƙu haka muka kasance tamkar musa da fir'auna. Asabe ta haɗa makirci, ta shiga ta fita, da asiri ta rabamu. Naje bikin Taraba saida nayi ɗan da kace banje ba, irin wulaƙanci, da tozarcin da akaimun a bainar nasi ba ɗan kaɗan bane. Gashi zuwana bikin yasa maƙwabta na nesa dana kusa sun hallara sabida ni, kunsan Allah yayi mu da farin jini. Wannan faɗama wannan, wannan faɗama wannan, akaita zuwa kallona sai wani ɗaki na shige na adana kaina saida nayi kuka kafin na samu salama. Haka muka dawo naci gaba da karɓar gashi, ga laulayi ya sameni inata gurgurawa a lokacin ko ɗakina miji ya dena shiga, ya ganni mu gaisa abun yaci tura, yaci abincina babu dama, duk ran girkina Asabe da yaranta kawai nake yi ma. Shi kuma Asabe zata fito tayi mishi girki na musamman. Tana yi tana cewa. "Gida nawa ne, na yi zantsuwar babu wata shegiyar da zata zo ta miƙe ƙafarta. Ramin kura sai ƴaƴanta. Inata laulayinnan har cikina ya tsufa a haka ban taɓa zuwa awo ba, ɗan maganin zaƙinnannan ban sha ba, in faɗa a gida nakasa sabida an riga an yima Mamanmu famfo akan bama zaman Aure, mun riga mun saba da kuɗi. Inaso in haskama duniya ba saboda kuɗi ko son film ke fito da ko wacce ƴar film ba, a. a wallahi ina da ja. Aure muke ke yi kamar kowa, da niyyar mutuwace zata rabamu, bawai auren jeki ki dawo ba. Ƙaddarar data haɗa Aure, ƙaddarar ke raba Auren, bawa kuma bashi da tsumi bashi da dabara, mu kaɗai muka san me muka fuskanta, me kuma muka shanye dan dai duk kada ace Aure ya mutu duniya ta ɗauka. Asabe ta azabtar dani, amman haka naita turawa, nace zan zauna a haka. To ina zaune da safe sai Mama tayi kirana akan Inna Mairiga ƙanwarta gata nan a tasha zata tawo ta zauna dani, tunda ciki haihuwa ko yau ko gobe. A lokacin da ta kirani kafin Innah mairiga ta taso zan hana, amman sai bayan da motarsu ta taso take sanar dani. Dana jiyo motsinshi zai fita sai naje na sameshi a gaban motarshi shi da Asabe nace. "Dama Mamace ta kirani tace dani Innah Mairiga ta taso, zata zo ta zauna dani." Sai nayi shiru dan a lokacin wani tsoronsu nake ji sosai dukkansu, ƙur yayi da idanu yana kallona can yace. "Sabida ban isaba harma saida ta tawo kafin zaki faɗamun, ke ɗin yarinyace da sai anzo an zauna dake ke da kika gama tsufa, kika rasa mai tayawa, ba zaki iyama kan ki komai ba? "Zan iya, wallahi nima Mama bata faɗa mini ba har sai da ta taso tukunna kayi.. " "Rufa mun baki dallah, akanme za'azo wani kula dake, kenan Asabe duk kulawar da take baki kin raina kenan ko?" Kaina ya ɗaure dan Asabe gaisuwata ma bata amsawa, bata ɗauke mun komai na ɗawainiyar girki da aikace_aikacen cikin gida ba, a haka nake gurguwara inyi komai. Naji kuma ana batun kulawar da take yi dani. "A.a Baban Murja ai ana zuwa a zauna in haihuwar fari ce. Tazo ta zauna in akayi suna ba sai ta tafiyarta ba, inma da'ita zata tafi wankan jego ba shikenan bama" Sai yace. "Ai shikenan tunda bayanta kike goyo, wato harma da wankan gida?" "Iyi sai taje ai tunda kaga tunda akai Auren bata je ganin gida ba" Ni da nake daskare a waje ɗaya mamakin kirsar Asabe nake yi. Wato kishiya bata kaɗan bar ganin kinfi kishiyarki komai da komai, wallahi tsab zata kai ki ƙasa. Innah Mairiga ba ita ta shigo ba sai washegari da azahar tazo ta sameni ina naƙuda na kasa neman tallafin Asabe sam, tare suka shigo suka taddani a durƙushe babu yadda nake.
Chapter 70 · 0% Book details