← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 85

Sashe 3

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

take yi. Wannan Khumra akwai mannewa a fata ƙamshinta ya riƙe jiki da kaya. ( Sunan wannan Khumra. (Khumrat al khaltat) Tana zuwa a 30mill cikin mazubi na ƙasaita mai nuna daraja da tsada. Tasirin ƙamshinta yana da ƙarfin riƙewa na kimanin awa arba'in da takwas. In bata miki wannan awannin ba, ki yi magana in dawo miki da kuɗin Allah. Ta samu aiki da sinadaran gargajiya masu ƙarfi da daraja. Wannan khumra sabuwar zuwa ce, wanda na shafe shekara guda ina aiki a kanta dominku. Duk mai so tayi magana) na buɗe durowata na ciro riga da wando falazo na saka, dubu arba'in na siye su masu santsi ko sawa ban taɓa yi ba, ribon ɗin kaina na sunce ina bin gashin da oil ɗin Oriflame na gashi, fuska, da jiki mai ƙamshin fiya. Wanda nake siya a hannun Mamanmu Hajara Aliyu dattijuwa mai girma da karamci. Ni sake lakuto man gashi na Mrs Bukhari gidan ƙamshi na ƙasaitattun matan da suka gane sirrin dake cikin ƙamshi. ( Sunan wannan man gashi na larabawan usil (Makhmariyatul Oud Al nafis) ke daji ba'a magana. Gashi tazo a mazubi kyakkyawa mai daraja lamba ɗaya. Wannan makhmariyya ƙamshinta na da ƙarko sosai ta yadda hatta matashin kai in kika kwanta ƙamshine yake kamashi. Masu so suyi magana. Wannan ma sabon aikinane dana jima ina aiki a kanshi, ban fito ba sai da shirya) "Hindu naga gashinki ya ninka na da me kike mishi haka. Sannan naji kin buɗe wasu kayan ƙamshi duk sun cike ɗakinnan da ƙamshi, daga Saudiyya kika tawo dasu hala? " Cewar Luba data fini maitar gashi harta taso tazo inda nake tana taɓa gashina dake kan kafaɗata gashi sai sheƙi da ƙamshi yake yi yana shan lele gaskiya. Maganin tayar da komaɗa (Supplement) na kamfanin Oriflame nake amfani dashi, da kuma wannan oil ɗin duk na kamfaninne. A wajen Hajara Aliyu nake siya" Yaya ta matso tace. "Gaskiya gashinki yayi yawa gashi ya kuma cika ni kamar har duhu ya sake yi fa, man kamfanin Oriflame ɗinne ya dawo miki da fatarki haka itama?" Wallahi Hindu kinyi kyau sosai kinyi rama naga babu tumbi a jikinki ko idanunane Luba?" Dariya muka saka kawai Yaya har tana ɗaga mun rigata dan su shaida. Fatata da ta shafa kuwa wani ƙamshine ya kama mata hannu. Nan na basu labarin mai maye gurbin abinci na kamfanin Oriprame da nake damawa in sha mai suna mil rifilesment, gwanin narka kitse, ya fatattaki tymbi da duk wata ƙiba kenan. Shima dai duk akwai a wajen Mama Hajara Aliyu. Dangane da kyan fata kuma, harda man fata na ƙamshi sirrin matan sudan na wajen Anty Badiat Mrs Bukhari, da kuma basarakiyar dilkhar ta ta asali mai dogon tarihi. Sunan man ƙamshi, da gyaran fata na mrs Bukhari shine (jamrat al dhahab makhmariyya) sarauniyar ƙamshi, taushi, da hasken fata kenan. Hajiya babu dana sani cikin wannan tafiyar ƙamshin. Shima sabon aikinane wannan) Luba tace. "Ai ta kwana gidan sauƙi, tunda ina cikin Taskar Anty Badiat. Mamanmu ma ai ta sanni, ba ta dai san ni ƙawarki bace. Anty Badiat tamu ce itama. Duk zan neme su, irin wannan ƙamshi mai ƙima" Yaya ma tace ba za'a barta a baya ba. Ai kuwa ku shirya, ku malkaki kaya masu daraja, kuma zaku canja kamar yadda na sauya. " Nan sukaita ɗaga kwalaben kayan ƙamshi na alfarma na Mrs Bukhari suna mai rantsuwar da ba dan ga sunanta a jiki da lambar wayarta ba, ba zasu taɓa yadda cewar a Najeriya ake wannan kayan ba. Yafi kama da kayan ƙamshin larabawa, wallahi ba yao bane darajarsu ta wuce yadda na faɗesu. "Zan gyara domin daɗin jikina. Hindu tuni na dawo daga rakiyar maza, ke nifa abunda mijinyawa yayi miki kaɗai yasa na gane ba'a iyama namiji wallahi. Da ace kuɗaɗenmu mu muka ci abinmu da yanzu mu hajiyoyine wallahi. To a hakanma Alhamdullilahi in da rabo kuma zamu yi. Ke wai kinga iskanci da kaɗifirin da Sunusi yake yi shi da mandiyarshi? Ummm ai tananan haihuwa ko yau ko gobe Hindu kya zo mata suna. Yaya Saratu ya kamata muje ko dare ya soma yi" Hala yau kece da turakar Sunusi, ke kike mulkin birnin zuchiyarshi" Duka ta kawo mun na kauce munata dariya kamar babu damuwa tattare damu. Kaina na taje ko tubkewa banyi ba ban kuma sa ɗankwali ba muka fito tare dasu. Mijinyawa mun baroshi a banɗakin korido dake a buɗe ya bari yana alwala. Har bakin get na rakasu mukai sallama akan gobe zan tawo musu da tsarabarsu, na dai basu su dabino da bagaruwa. A Kicin muka ci karo da mijinyawa, da Azgar zasu tafi masallaci. "Zamu je masallaci mu dawo yanzu" Ganin Azgar yasa nace Sai kun dawo" Na ratse na wuce mijinyawa sai kallona yake yi. Nayi imanin ƙamshina ya dakeshi sosai. Nima dana shiga nawa ɗakin bonar turaren wutan mrs Bukhari na kunna kawai, na zura hijabi na tayar da sallah. Ban tashi a inda nake ba sai da nayi isha tukunna. Na fito na kira Sabira muka shiga Kicin. Shayi na dafa mana kawai na tawo da kayan shayina shi na zuba mana kofi uku na buɗe robar dambun nama mai yawa na zuzzuba mana a kwano. Ɗauki naki dana Yayanki, in Abbanku yazo kice ni na kwanta kuyi adda'a ku kwanta kuma Azgar ya rufe gidan in Abbanku ya tafi" A sanyaye tace "To Ammi" Kamar tana son tace wani abun amman sai ta haɗiye, gudun kada mijinyawa yazo ya sameni yasa ban tursasa mata ba nayi shigewata, na saka sakata na baje a gado harda kunna siris ɗin da nake kallo mai suna The train ina shan shayi ina tura dambun nama bakina. Ina mamakin film ɗinnan sosai da yadda aka samar da aiki ingantacce, kuma na ƙagu inga ƙarshen yadda zata kaya. Bayan na gama nayi gyatsa sai kuma na miƙe na shiga jera kayana a cikin sib tsab. Ina tsaka da jerawanne na jiyo bugun ƙofa nayi imanin mijinyawane dan dai yara ba zasu buga mun ƙofa ba musamman da na barma Sabira saƙo. Guntun tsaki na sake ko in kula da bugun ƙofar na soma ware tsarabar ƴan gida na ɗakinmu kenan. Gobe dole saina shiga kasuwa kafin in iya zuwa gida kenan, na mance zan siyo tsarabar matan gida, da ƴan gida. Saida na wauware dukkan abinda ya dace na sake kayan jikina zuwa na bacci. Nayi hayewata gado adda'ar bacci nayi na saki ac na bi lafiyar gado zuchiyata fal farin ciki haka na wayi gari. Ashe haka gidan kai yake da daɗi gaban mamaki? Hmm mata mu dage wallahi mu saka Allah a farkon lamarinmu ko baki zauna a gidanki ba mallakar tana da amfani. Yanzu yaci ace mu waye mu dena gasar haihuwa, ko cika gida da ƴaƴa, da sunan kafin wata ta shigo, duk don sabida gado, shin ke bakya fatan samun naki kuɗin sai dai a mutu a bar miki, mu shikenan bama son mu yi kuɗi, muna jira har sai an mutu, wani mijinma sai yayi shekara ɗari bai mutu ba, har lokacin gado kike jira kina ruwa kuwa. Me yasa mu ba zamu tashi mu nemi namu kuɗin ba, ke ba kya fatan ki mutu a baje dukiyarki a kasaftama yaranki ne? Sannan wa yace miki mijinki ne zai soma mutuwa kafin ke? Kina da aiki, kuna da aiki kar ku tashi haiƙan ku nemi gumin halak ɗinku. Zuchiyata fes wasai na wayi garin ranar. Ƙat ƙat na buɗe kin ɗakina na fita, ɗakin Sabira na soma shiga, ta riga ta tashi tana kan sallaya. Azgar dai sai da na tasheshi nace yayi alwala ya tafi masallaci. Kana na dawo nayi wanka tare da alwala bai ɗaya. Nazo na gabatar da sallah, nayi azkhar ɗina na safe sannan na tashi na shirya cikin doguwar rigar yadi kwatin mai laushin gaske, na taje kaina na kuma tubkeshi da ribon na feshe jikina da turaruka bayan khumra dana shasshafa saina fita da tsarabar yara. A falo naji muryarsu saina nufi falon da fara'ata da sallama. Turus na tsaya ganin mijinyawa a kwance a ƙasan kafet yayi matashin kai da fulon kujera wandon shadda da singileti ce a jikinshi yana bacci. Idanu su Azgar suka zuba mun, Sabira ta miƙe ta karɓi kayan hannuna. Gaisawa muka yi cikin kewar juna sosai. Wannan ledar naki ne, wannan na Azgar ne. Kai Azgar zo ka ɗauki mota kayo mana cefane maza" "Ammi Abba ya kawo kayan Shayi tun jiya da daddare har da ƙwai ma" Shiru nayi ina nazari can nace. To shikenan kuzo muje Kicin ina zaune ku yi mana abun karyawa." Sabira tace, itace Zata yi, Azgar yace. "Ammi rabu da'ita kinfi son girkina na fisu iyawa ai ni zanyi mana" Muna dariya mijinyawa ya farka carab muka haɗa idanu dashi, ga matsananciyar kunyata a idanunshi ainun. "Abba barka da tashi" "Barka Azgar. Tutar so kin tashi ashe? " Ashe baka tafi ba? " Ficewa yaran suka yi, ai sai nayi yinƙurin bin bayansu yace dani. "Hindu" Juyowa nayi na zuba mishi idanuna cikin kallon ido cikin ido kallon ƙurulla, tuhuma, da takaici. "Inaso ki aramun lokaci dan Allah mu zauna mu yi magana. Duk da bansan ta ina zan soma miki ba" Nuna kaina nayi da yatsana manuniya nace. Wai ni da kai muyi magana? Kayi haƙuri ina girmamaka sabida yaranka. Sannan kayi ƙoƙari ka tafi gidanka ina buƙatar in kaɗaice da yarana kaɗai. Ina buƙatar takaddata bana son abun ya kaimu inda rai bazai yi daɗi ba" Ai jin na faɗi haka babu wasa da murya ta rashin tsoro sai ya zabura ya taso yazo har gabana daf ina jiyo ƙamshin shi balle ni da nayi wanka yanzu. Cikin muryar da yasan yana iya shawo kaina a duk yadda na hau dokin fishi yace. "Hindu alƙawari na ɗauka a gaban iyayenki cewar ba saki babu yaji. Ki daure mu sasanta muyi magana nasan nayi abinda ba zaki taɓa yafe mun ba. Hindu nasan na miki abu mummuna, amman aimun afuwa a yafe mun a bani dama" Baka yi mun komai ba ni, in kana tunanin kayi mun wani abun, to baka yi ba. Ai rayuwa ce kullum da kalan sauyin da zamani ke zuwa mana dashi.
Chapter 3 · 0% Book details