← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 85

Sashe 61

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

gama suka wuce masallaci ni kuma na yinƙura na ƙule ɗakina,naci gaba da harkokina. Wajajen taran dare naji bugun ƙofata a hankali nayi tunanin Azgar ne shi yasa nace a shigo, dake na leƙo nace ya dafo mun ruwan zafi inason shan bunu. Ƙamshin turarenshi yasa na juyo muka haɗa idanu ina bakin mudubi ina taje gashin kaina ɗaya daga cikin abinda Mijinyawa yafi wasa dashi a jikina kenan, ya nutsa kanshi cikin gashin yaita shaƙar ƙamshin dadaɗan ƙamshin makhmariyyar gashi da jiki, da nake sakawa mai suna JAMRAT AL DHAHAB MAKHMARIYYA, daga kamfanin mrs BUKHARI. Kallona yake ta faman yi daga tsaye inda yake. Kafin yayi magana Azgar ya shiga bubbuga ƙofar shima, mijinyawane ya bashi izinin shigowa ya turo ƙofar da turen shayi a hannunshi ɗauke da kofi cike da ruwan zafi. "Abba sannunku da hutawa" Azgar ya faɗa yana wani murnar ya ganmu a tare. Shima ya saki wani fara'a harda wani dafa kafaɗar yaron. Ajjiye a kan taburi Azgar nagode ko?" "To Ammi sai da safenku zan ɗan yi karatune in kwanta." Juyawa yayi ya ficewarshi, ni kuma na ɗakko sikari da ganyen shayin Ahmad nazo na zauna a bakin gado, jikina ko ina ciwo, zazzaɓine mai mugun zafi a jikina. mijinyawa ya zauna a kujera muna fuskantar juna. "Hindu" Ina saurarenka" Na faɗa a taƙaice sai yayi shiru idanunshi ƙur a kaina. Ina jin kaifin idanun nashi amman dai ban ɗago ba. "Na samu canjin wajen aiki kamar yadda aka saba kinsan sha'anin aikin banki, yau kana wannan gari gobe kana wancan garin. To shine nace bari in sanar dake ke da yaran ku zauna cikin shirinku karshen wannan watan in sha Allah zamu wuce. Katsina wannan karon aka lulamu kuma" Ya ƙarashe yana guntun murmushi. Allah sarki Allah yasa ka koma a sa'a, Allah ya ƙaro dubun nasarori" Na faɗa a taƙaice tare da ɗaukar shayina na soma kurɓa a hankali. "Ban gane ba Hindu, amman kinsan tare daku zan tafi ko, kinfi kowa sanin babu inda zanje in bar iyalina a nan ko?" Aikin nawa sai in yi yaya dashi, in ajjiye gani ƴar daɗi mijin da baisan darajata ba, ƴar daɗi mijin da bani da abinda nake burgeshi dashi ko me kake so ne mijinyawa? Bagidajiyarnan mai yamutsattsen nono ce a gabanka, ba Asama'u Sweet L ba, ba kuma Talatu Fist bank bace, wacce tafi tutar so matsayi ba" Kallon ƙuda muka shiga yima juna idanunshi lokaci ɗaya suka sauya launi daga fari zuwa ruwan ja. "Hindu wai ke wacce iri ce da ba kya yafiya bare mantuwane, yanzu duk irin sauke kaina da nake yi dan mu dawo mu sasanta bakya gani. Yanzu duk irin yadda nake sonki bakya gani Hindu sai gasani kike yi. Amman ai kinsan a ko wacce jiha akwai gidajen rediyo, a irin ƙwarewarki abune mai wuya ace kin nemi aiki kin rasa Hindu, kuma kinsan zanyi iya kacin iyawana akan aikin naki taya zan samu wani nutsuwa bana tare da iyalaina? " Bance mai komai ba dan a lokacin in nace zan buɗe baki in yi magana wallahi komai zai iya faruwa ji nake yi kamar in dira a wuyanshi in kekketa mishi kayan jikinshi. "Dake nake magana wacce iriyar zuchiyace dake, baƙa wacce bata yafiya ne? Nace kiyi haƙuri nayi nadama bazan sake ba, inata istigifari ban dena ba to Hindu saina kashe kainane zaki gane nayi nadama koko mai kike so ne, jibi iriyar rayuwar da muke yi ina matsayin mijinki amman tare da ɗana nake kwanciya ke kuma hankalinki kwance bakya ko jin nauyin haka yara na kallo. Shin haka rayuwar aurenmu zata ci gaba da tafiya ko me kike nufi Hindu, tura na neman kaini bango haba dame kike son inji, da damuwar dangina, ko da halin da muke ciki ni da ke akan wani kuskure dana aikata. Wannan ƙananun iskancin sun isheni na gaji, nace miki nagaji." Sai kuma ya sauke murya tare da furta "Hindu Asama'u wallahi Allah ɗaya kenan tunda na aureta ban haɗa shinfiɗa da'itaba. Tun sanda kika turomin saƙwanninnan Hindu har zuwa yanzu ban sake farin ciki ba, Hindu ba farin ciki kaɗai ba ban sake lafiya ba, a kullum da baƙin ciki da damuwa nake kwana nake tashi, ga ciwon gangar jiki shima shirin kayar dani yake yi, sai neman rayuwata yake yi, kuma duk a kan ki Hindu dan Allah na roƙeki ki yadda dani a karo na biyu bazan baki kunya ba. Kinsan ina sonki kin sani Hindu shi yasa ma kike ta wahalar da rayuwata." Fasali ya ja tare da miƙewa tsaye ya juya mun bayanshi yace. "Sai azabtar dani kike yi ki buɗe baki ki amayar da abinda yake cikin ki Hindu kin ƙi, sai faɗuwar gaba nake ciki a duk sanda zan kalleki, kina ta mun gashin ƙuma, Ki tausayama zuchiyata Hindu" Miƙewa nayi ina murmushin da wallahi yafi kuka zafi da ƙuna, taku biyu nayi kawai na ja na tsaya. Mijinyawa kenan bari in tambayeka mana. Da ace Asama'u namiji ne, ka kawoshi na rene shi, sai ka kamamu da irin abinda kuka aikatamun kai da tsohuwar matarka kuma ɗiyar amininka, shin yafe mun zaka yi inna ce maka nayi nadama kenan, sai ka mance komai ka sasankance kaci gaba da rayuwa dani cikin yadda da aminci. Mutumcina bazai taɓu a idanunka ba, sona da ƙaunata zasu ci gaba da guda.... " "Hindu ki dena irin wannan kwatancen kafin kisa kaina ya juye mun, kasheni kike son yi ne wai? Gani kasheni Hindu ki kasheni" Ya juyo a fusace harda nuna ni da yatsanshi jikinshi na rawa na iskanci, wai kishi ne ya kamashi. Dariya ma ya bani amman banyi ba sai cewa nayi. Batun tafiya Katsina babu inda zani ina mahaifata. Aure na faɗa maka na gama, na shigar da batun ma kotu" Sai na koma na zauna naci gaba da shan shayi na. Shima dawowa yayi ya zauna. "To yaya kike so ayi Hindu, wallahi bazan iya tafiya ko'ina in bar iyalaina ba kinsan bazan iyaba Hindu" In kaje sai kayi aure tunda iyali kake nema ai. In kaso kuma sai ka maido Asama'u ko, ka ajjiye daduro.... " "Ya'isheki haka Hindu. Naga halama kin rainani, to bari kiji dole ki bini, ko kuma in kwashe yarana in tafi dasu wallahi" Bazan bika ba, kuma yara in kaga ka fice dasu a gidannan to takaddata ka bani, kana da damar da zaka ɗaukesu tunda ba dasu nazo ba, basa gabana daga kai har su" Na faɗa cikin ruwan sanyi. "Takaddar kike so, burinki mu rabu ko Hindu? " Burina kenan babu amfanin aurenmu mijinyawa, babu in akwai amfani ka faɗamun, dan haka ka sauwaƙemun ka kwashi yaranka in birnin sin zaka koma ka koma" "Shikenan zan miki abinda kike so Hindu. Amman wallahi in muka tafi ba zaki sake ganinmu ba a rayuwarki ba, na faɗa miki kenan sai dai hotuna su zama ababen kallonki, kuma ba zaki sake waya da yara ba kin yadda? " Yara sune rayuwata, amman babu yadda za'ayi mijinyawa ya shiga rigar yara yayi mun barazana wallahi bai isaba. Duk da nasan sharia zata ba yaran zaɓin inda suke so, amman bazan yi faɗa akan duk abinda ya shafu mijinyawa ba. E na yadda, ka kwashesu, ni ka bani takaddata in ba dai so kake in shiga wuta ba" Na furta a ido ko a jikina, amman ta ciki hantar cikina kaɗawa kawai take yi. Taya za'a raba uwa da yaranta tana raye ace ko a waya ba zan sake jinsu ba. Taya haka zata kasance ni Hindu? Amman in dai wannan shine sharaɗin da zai sa mijinyawa ya rabu dani ya sauke mun ƙaddararren aurenshi, na yadda ba gudu ba ja da baya. Fita yayi a ɗakin fuu ya barni ina karanta wasiƙar jaki Tabbb to mu kwana anan sai gobe
Chapter 61 · 0% Book details