← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 85

Sashe 19

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dan duk abinda Baballe ya kuma yi mata zamu sake garzayowa" "Ƴar kwangilar yahudawa, wato kin shigo rayuwar Badia ne domin kisa ta boƙaremun? To Lubna Saleh michika ma shugabar mata boƙararru ba'a bakin komai take ba a wajena" Ai kuwa a bakin komai take da ita da ire irenta sun tsaya ma maza a wuya kamar ƙayar kifi. Kun fi so mata su kasance a cikin duhu kuita gasa musu aya a hannu ko? Ni da Badia mun riga mun zama ƙawaye babu yadda ka'iya dani." Nan dai muka gama abinda zamu yi muka baro Baballe acan sabida sai Dpo yazo kana ya basu umarni ayi belinshi. To Badia ga kuɗi sun samu a shawarce ki sai gado da katifa, sabida yaran, sai kujeru ko da rabin seti ne da abinda ba za'a rasa ba. Zan siya miki kafet ki saka a falo, zan kuma taimaka miki da jari in sha Allah." "Nagode sosai Malama Allah ya duba miki, ya raya zuriyarki, ya barki da mijinki har aljannah" Babu komai Badia nagode sosai. "To nima ina da tsohuwar katifa zan taimaka da ita ko yara sa kwanta a ƙara muku" Cewar ƙawar Arziki Luba. Nan ta shiga murna tana godiya. A gida na sauke Luba nima na nufi gida. A falona na tadda baiwar Allahn da muka yi zata zo yau. Ita kaɗaice a falon mijinyawa naga motarshi amman ƙila sabida ganin baƙuwa yasa ya tafi ɗakin Azgar. Shiga nayi a mugun gajiya. Gaisawa muka yi da fara'ata na marafceta, da ɗiyarta mace da ba zata wuce shekaru biyar zuwa shida ba. Me sunanki ƴan mata? " Na tambayi yarinyar tare da ɗan jawo hannunta. Sai kawai ta fashe da kuka. Toh ƙyuya take yi ne?" "Ba ƙyuya take yi ba. Bata da lafiya ne Hajiya bari ki gani." Sai ta kamo yarinyar ta cire mata ɗan zanin jikinta sai na ganta da ƙunguzun yara a jiki. Tana warware ƙunzugun sai wari ya cika wajen. Duburarta ta juyomun na gani a fatattake uwar sai sharce hawaye take yi, yarinyar kuwa jikinta har rawa yake yi. Baiwar Allah dena kuka waye yayi ma ƙaramar yarinya irin wannan aika aikar, ke kuma kina ina?" Sai rishin kuka kawai take yi. Mayafina na gyara na suri jakata. Taso muje asibiti duk abinda ya dace za'ayi asibitin shine farko" Kinkimar yarinyar tayi muka fito. Azgar zo ka tuƙamu zuwa asibitin malam aminu Kano dan Allah nagaji bazan iya tuƙi ba, kaina ciwo yake mun. Kema kizo muje" Duk na tattare kan yaran muka tafi malam Aminu Kano sabida nasan wata ne suka amince suka karɓemu ba tare da mun haɗa da ƴan sanda ba. Ban bar asibitinnan ba sai sha ɗayan dare, sai da na siya ma Mariya abinci, ƙanwarta tazo taya ta kwana kafin nayi mata sallama akan gobe zan shigo da safe mayi magana lokacin, dan na fahimci bata cikin hayyacinta. Ina bayan mota tunanin ƙaramar yarinyarnan ya shigeni, kes ɗinta ya gigitani inata tunanin to wanne marar tsoron Allahn ne ya hakkema yarinya ƙarama irin khadija kuma ta baya, ya fatattaka mata takashinta sosai. Kainane yaci gaba da sara mini, tamkar zai faɗo. Ni nama mance a cikin damuwar da ni nake ciki shaf. Ko da na shiga gida shayi kawai da guntun kek naci, na yi wanka a daddafe na kwanta cike da mafarkai marasa daɗi. Washegari da safe na wuce asibiti na tafi ma da Maman Khadija abinci. Khadija tana baccinta ga ƙarin ruwa a ɗaure a hannunta uwar tayi tagumi kawai. Bayan mun gaisa sai na nemi ta juya mun bayan khadija zanyi bidiyo in yaɗa. Bayan na ajjiye abincin nayi bidiyon sai muka runtuma wajen likita yarinyarnan aiki za'ayi mata nan da kwana bakwai, sabida ashe ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, aka ayi mata wannan aika_aikar ba kuɗin aiki ana neman nera dubu ɗari kusan uku da ɗoriya. Mahaifiyar Khadija ta fito a firgice tana kuka. Ki yi haƙuri maman Khadija A gurguje takwas ta kusa inaso zanje aiki shin wa yayi ma yarinyarnan wannan aikin? " "Ƙanin mahaifinta ne da yazo daga ƙauye yake zaune damu shi yayi mata wannan aika_aikar. Ki taimaka mun a ƙwato mata hakkinta dan Allah Hajiya Hindu" Kai nane naji yana ƙoƙarin bugawa da mamakin jin furucinta na wai ƙanin mahaifinta ne yayi mata wannan aikin. Lallai anyi ma zumunci riƙon sakainar kashi. Ajjiyar zuchiya na sauke murya a dashe nace. Kuma yana ina yanzu? " "Yananan tare damu Mijina baima amince cewar Musa shi yayi wannan aikin ba. Akan haka har mahaifiyarsu sai da tazo daga ƙauye taci mun mutumci sosai, kuma suka ce ko Musa ne yayi dole ayi haƙuri a zauna dashi a haka kada ayi abinda zai taɓa zumunci. Haka suka cuceni suka barni da yarinya ko asibiti ban kawota ba, wai gudun tonuwar asiri. Ni nake ciyar da kaina da kula da Khadija da yayunta" Tabbb duniya tazo ƙarshe ai yanzu lalacewar zamani har ya kai Musa yayi irin wannan abun kuma a daddanne maganar, harma a biki da sharri. Musa yana gidanku yana rayuwa kenan daku? " "Wallahi yananan Hajiya shima fa har rirriƙeshi aka dinga yi akan wai sai ya kasheni shi sharri nayi mishi" To ke ubanki kike yi da baki san yana kwanciya da'ita ba. Yarinya ƙarama irin Khadija ace ana saduwa da'ita ta baya, amman ke baki ma sani ba, har saida ta ruɓe? Zuchiyata sai naji tana tasomun tamkar zan amayar da'ita. Da ƙyar na saita kaina gudun kar in sake jefata a cikin wani taskun. Zanje aiki inna dawo zamu je dake ofishin ƴan sanda yau Musa bai isa ya kwanta a ɗakinshi ba da izinin Allah zan yi miki tsayuwar dakan da sai na ga Musa a gidan yari a garƙame kafin hankalina zai kwanta. Amman ki mun alƙawarin barazanar saki ba zata sa ki juya mun bayan da za'a soma kes kizo a zugaki ki janye ba? Zan yaɗa bidiyon Khadija tare da asusun bankina ga masu bukatar taimaka mana in sha Allah. Ki je ki zauna kuci abinci, ki kuma kwantar da hankalinki" Da haka mukai sallama na wuce aiki, a ranar ma naje gidan gwamnati na ɗakko rahoto na dawo ofis ƙarfe uku muka tashi, yau ni kaɗai na wuce Luba tana da inda zata je. Hankalina bai kwanta ba saida muka shigar da ƙara sukaimun alƙawarin Musa a hannu zai kwana gobe mu dawo. Nayi farin ciki sosai haka ma Maman Khadija tayi murmushi ko babu komai naji daɗi ganin murmushi a fuskarta. Tun daga nan ofishin ƴan sanda take bani labarin yadda abun ya faru. "Ni gidan aiki nake zuwa in yi wanke _wanke da girki da yamma in dawo gida. Ɗan abincin dana tawo dashi shi zamu ci da yarana. Ina da kishiya itama ita ke ciyar da kanta sai yaronta dake tallar fiya wata ya ɗauke mata abincin dare. Yarana ukune Khadija itace ta biyu Akwai yarsu shekararta takwas sai na goye. To inna tafi gidan aiki Rabi'a ta tafi nata aikin sai yara a gidan, Salma ita ke kula da Khadija shi na goyen tare nake zuwa dashi wajen aiki. Da rana Musa yake dawowa gida yaima khadija wannan aikin. Ranar da nake tunanin itace ranar farko naga jini a wandonta a tunanina bayan gidane nasa Salma ta wanke mata tana ta kuka nayi tunanin kukan rigima ne kawai na yara. To washegari da zazzaɓi muka tashi tayi zazzaɓi sosai daga baya ta warware, har Rabi'a na mata tsiyar daga yin ciwo tafiyarta ta canja. To sai ranar da yayi mata wannan wallahi har Yayarta tace ta ganshi itama kuma yana cewa ta sha mishi kuma tana sha" Tai ta bani labarin daki daki da irin rayuwar da suke yi wacce bata da maraba da zaman kai. Kuma da sunan aure suke yi mijin aska na cin ƙwaryar kanshi, anma ya bar rayuwar iyalinshi a haɗari. Ayi magana ace mune masu hure ma mata kunne. Yanzu dan Allah masu karatu da irin Auren da su Maman Khadija da kishiyarta suke yi ba gara zawarci ba, mace tasan bil haƙƙi dole ita zata kula da kanta ba? Tabbb Allah ka gyara mana. Wannan lalacewar zamani da lalacewar wasu mazan da yawa take. Nayi mata tambayoyi masu yawa a matsayina na ƙwararriyar ƴar jarida. Akwai kuskurenta da sakaci sosai. Ace kamar Khadija yarta ƴar shekara takwas ita ke mata wanka yarinyar da in da gata bata wuce a wanke mata kashin mazaunanta ba, wai ita ke kula da ƙanwarta. Nayi mata faɗa_nayi mata faɗa. Na nuna mata laifinta ta kuma yadda tabbas tana da lefi. Daf magriba muka iso asibitin naje na duba jikin Salma na basu kuɗin siyan abinci nayi musu sallama na shiga gida ana kiran isha. Sabira kawai na tarar a ɗakinta tana sallah. A banɗakinta na ɗauro alwala nazo na gabatar da sallah. Muna hira da Sabira ina tambayarta makaranta da gida su Azgar suka shigo. Jin muryata a ɗakin yasa suka shigo harda Mijinyawa da kwana biyunnan nake ganinshi kamar marar lafiya sai sake tsomarewa yake yi. "Tutar so kin dawo barka da dawowa ya aikin? Ban ko kalleshi ba Ɓoyayyar ajjiyar zuchiya ya sauke. Ya jima yana hira da yaranshi yanayi yana kallona ni laptop ma na buɗe na yaɗa bidiyon Khadija tare da taƙaitaccen rubutu da lambar wayata da lambar asusun bankina, masu son zuwa suga khadija domin tabbatarwa su kirani ta waya sai in kaisu su ganta. Ban faɗi asibitin da take ba gudun kar a damesu da zuwa, ban kuma yadda fuskarta ta fito ba sabida watarana zata girma itama ta zama mace, hakan zai iya zama mata tarnaƙi wajen auruwa. Ina ɗago kaina naga Mijinyawa ni kawai yake kallo ya shagala sosai yana mun wani irin kallo. Rai na haɗe tare da tura labtop ɗina a jaka na miƙe na fita zuwa ɗakina. Ina fitowa wanka Sabira ta kawo mun jallof ta taliyar manja da bushasshen kifi sai ruwan shayi na Ahmad. Zama tayi ina ci muna hira duk da na gaji amman data buƙaci hirar take so muyi saina zage nasan suna kewata, kwana biyunnan kaina yayi zafi sosai. Washegari da asuba dana tashi wallahi tallahi naga kuɗaɗe da suka shigo fin nera dubu ɗari biyar, kuma
Chapter 19 · 0% Book details