Sashe 20
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fa harda masu saka ɗari biyu. Mutanen da sukaimun magana ta manhajar WhatsApp kuwa Allah yayi yawa dasu harda wata lauya da tace mun tana da ra'ayi akan kes ɗin in za'a shiga kotu. Wannan saƙon nata yayi mun daɗi sosai da sosai. Amsa mata nayi tare da yi mata godiya mai tarin yawa. "Inason ganin yarinyar yau in babu damuwa, domin in tattauna da mahaifiyarta" Ta rubuto mun. Sai na bata amsa da. Mu haɗu a asibitin malam Aminu Kano da misalin ƙarfe huɗu zuwa biyar na yamma" A gurguje na fito daga ɗaki shayinma a tsaye a Kitchen na sha da yara suka matsa lamba. Ina kan sha mijinyawa shima ya fito cikin shirin fita ganinane yasa ya tsaya. "Giwa kin tashi lafiya? Naga bidiyon da kika yaɗa na tausayama Khadija gaya, ai itace yarinyar da suka zo jiya tare da mahaifiyarta ko? Itace" Na faɗa tare da kurɓar shayina ina tura biredi. "To Allah ya bata lafiya, shi kuma Musa In mai shiriyane Allah ya ganar dashi. Nima na tura da nawa gudunmawar duk da babu yawa dai. Ni zan wuce aiki amman inna dawo inaso zamu yi magana dan Allah" Kallon tsana nayi mishi, da sauri yayi ta hanyar haɗe hannayenshi dukka biyu halamun ban haƙuri" Bani da lokacine abubuwan da suke kaina sun sha mun kai. Kana iya bari ƙarshen sati amman a ranakun aiki bani da lokacin ɓatawa" Rai ya haɗe da halama abinda na faɗi yayi mishi zafi. A tsaye a wajen na yi ficewata na barshi cike da ta'ajibin abinda nace dashi. Nasan mamaki yake da har aka samu wani lokaci da ni Hindu bani da lokacin shi aikina yafi mun komai mahimmanci. Ina shiga motata na tayar da'ita ina zaune ina ɗan womin ɗinta. Sai kiran wayata akeyi lambobi daban daban. Azgar na buɗe mun get na fice ina ɗaga mishi hannu. Tunda na fito nake amsa wayoyi duk akan kes ɗin Khadija lauyoyi uku ne suke da ra'ayi akan kes ɗin dukkansu mata ne. Hukumar kare hakkin ɗan adam ma sun mun magana akan zasu shiga kes ɗin. Da murna da farin ciki na isa office aikinma cikin karsashi da jin daɗi na gudanar dashi. Da muka yi birek ne nake labartama Luba abinda ake ciki. "Ai naga bidiyon ya yaɗu fiye da tunani Hindu. Gaskiya kes ɗin khadija kes ne da duk mai imani sai ya tausaya ma yarinyar harma da uwar yarinyar. Yanzu nasan dai kotu dole za'a shiga kuma dole a hukunta Musa, amman ita Maman Khadija zai yi wuya aurenta yayi ƙarko da Baban khadija tunda dai ya nuna yana bayan ɗan uwanshi." Ai wannan aure ya daɗe bai rabu ba Luba. Ya saketa mu shigar da shi kotu ba. Ai hakkin ci, da sha, da tufatarwa, da neman lafiya, da baya iya musu yanzu. Wallahi daga lokacin da ya saketa zai sha mamaki" " Hindu maza sun shigo hannunki ai wallahi sun zama nama" Dariya muka saka. Bayan mun tashi a wajen aiki kuma. Sai nace da Luba taje gida akwai inda zani, inna dawo zan zo har gida in ɗauketa muje asibiti. Haka akayi, ita ta wuce gida ni kuma kai tsaye na bi adireshin gidan Talatu Ibrahim first bank. Na ko ci sa'a maigadi ya buɗe mun get na shiga harda motata, sakamakon mun yi waya da Talatu Ibrahim First Bank tun dana taso. Yadda na tsammaci gidan ba haka na tarar ba, gidan yafi mun kama da gidan matar aure, ba mai zaman kai, ko mai zama gaban iyaye ba. A haka dai na kutsa kaina na shiga. Ilay sai ga hoton Talatu, da mijinta, da yara biyu maza a bango. Ko wanne hoto mutum ɗayane a jiki. Girgiza kai nayi kawai ina ta'ajibin ashe Mijinyawa har matar aure kenan yake mu'amala da'ita. Ni dai ina zaune bayan na gama ɗaukar hoton hotunan Talatu dake jere dana mijinta a waya. Sai gata da fara'arta ƙaƙas. Ta zauna sai muka gaisa, harja jus ta ajjiyemun. "Bismillah ga ruwa ki ɗan sha" Murmushi nayi mata. Kar ki damu da ruwan Talatu Ibrahim. Nace ashe mijin naki soja ne ma, gaskiya mana" Sai ta ɗan haɗe ranta kaɗan tace. "Me kike nufi ne? " Yanzu in nace miki mijinki yana zinace zinace da abokiyar aikinshi kuma matar Aure, ke kuwa Talatu ya zaki ji? " Wannan jus dai ita ta ɗauka ta kurɓe. Murya na rawa tace. "Me kike nufi da hakan, ni na ɗauka da gaske ƙawata da muka yi karatu tare ce ke, kamar yadda kika ce mun? Taya zaki haɗa mijina da irin wannan alkaba'in. Wacece ke me kuma ya kawoki?" Murmushi nayi na ɗakko wayata na tura mata wannan hotunan chart, nace da'ita. Duba wayarki zaki ga saƙo sai kiyi mun bayani" Da sauri ta shige wata ƙofa ta ɗakko waya ta dawo ta zauna. Data buɗe ta gani, kuma na haɗa mata da hotonmu da muka ɗauka ni da mijinyawa. Sai kawai ta sauke kanta tana zufa. Can ta zabura ta dawo kusa dani. "Ki mun rai wallahi muddin mijina yasan halin da nake ciki, kashina ya bushe bindigeni zaiyi" Kallonta nake yi ƙur yadda take hawaye, jikinta na wani irin mazari. Hmmmm Talatu Ibrahim. Yaushe kuka soma nema ke da Magawata Ɗan safiyo? In kika mun ƙarya komai zai iya faruwa" Sai carab ta rirriƙemun hannayena tana godona. "Ki yi haƙuri. Wallahi zaman kaɗaici da rashin mijine yasa na soma neman mijinki wallahi. Mijina Soja ne, bashi da lokacin iyalinshi sam, kuma bani kaɗai bace matarshi ba. Kuma kinji na rantse miki Magawata Ɗan safiyo bai san ni matar Aure bace, nace mai mijina rasuwa yayi. Bazan mai ƙazafi ba, wallahi tabbas na tabbatar mishi babu aure a kaina. Kuma ni na nemeshi da kaina" Ta wacce hanya kika nemeshi to? " Kanta ta sauke tace. "Ta hanyar waya, na jima ina tura mishi tsaraicina tun baisan wacece ba. Har na bayyana mishi ni wacece, daga nan ne muka soma haɗuwa dashi. Kiyi haƙuri dan Allah. Akwai sanda muka haɗu da Ƴarshi Asama'u a zango baƙi ma. To kusan tun daga lokacin alaƙarmu ta yi baya. Daga baya yazo ya janye mun gabaki ɗaya. Ko na je ofishinshi koroni yake yi. Shikenan dai muka yanke alaƙar tamu. Nayi nadama tunda nake ban taɓa jin kunya da tsoro irin na yau ba. Ki rufa mun asiri" Shiru nayi kawai ina kallon yadda take rusa kuka tamkar ranta zai fita. Ni kuma a lokacin zuchiyatace take ta yinƙuri tamkar zan yi amanta. Mun fi mintuna goma tana kukanta, ni kuma ina rarrabe kalmominta, da batun Asama'u da tayi. A wanne zangon baƙinne kuka haɗu da Asama'u, kana a cikin irin wanne yanayin ku kuke a lokacin data gankun?" "A harabar shiga zangon baƙinne, mu kuma mun fito, hannunmu na sarƙe dana juna, har muka shiga mota shi bai ganta ba, amman ni na ganta a lokacin. Kuma taga abinda muka yi a cikin motar, a nanne Magawata ya ganta duk ya ruɗe, shine ma nake tambayarshi wacece ita, yace mun ɗiyarshi ce ta biyu" Murmushine ya suɓucemun kawai. A wanne yanayi ta ganku kuma? " A kunyace ta faɗamun, Asama'u ta ganshi a lokacin yana yamutsa Talatu, bakinsu a cikin na juna. To a lokutan aiki kenan kuke zuwa ku sheƙe ayar taku, ko ya kuke haɗuwa. Na dai san sau biyu ya taɓa fita a ranakun da ba aiki" Idanuna na zuba mata. Ina jinki, in kin zaɓi in turama mijinki ai shikenan, ina da lambarshi, harda lambar mahaifinki daya haifeki ma" Muryarta na rawa tace. "Ranakun aikine ne muke haɗuwa, sau ɗaya muka taɓa haɗuwa ranar wata asabar" Itace asabar ɗin da yazo daidai goma sha ɗaya ga wata ko?" Kai kawai ta gyaɗamun. Murmushi nayi nace. To sau nawa kuma kika kawoshi gidanki kuka kwana ne?" Kuka ta fashe dashi tace. "Sau biyu ne, kaɗai muka kwana. Daya kwana ɗaya washegari ya tafi Jama'are, daya dawo ya kuma zuwa ya kwana, washegari ya wuce shikenan wallahi, ban ɓoye miki komai ba." Kai kawai na girgiza ina jinjina girman rashin mutumcin Mijinyawa. "Dan Allah zaki rufa mun asirina, ki duba yarana" Na duba su, kuma bazan yaɗa sirrinki ba. Ke dai kiji tsoron Allah ki kuma sani Allah bazai taɓa barinku ba. Kinci amanar mijinki da yaranki, shi farkanki yaci amanar matarshi da ƴaƴanshi, kun saɓama Ubangiji kun yi zina kuna da aurenku, zina mafi muni, wa'iyazubillah. Shekararku nawa kuna wannan sheɗancin?" Shiru ta kasa magana, kuka take yi tamkar ranta ne zai fice, tana yi tana tari, ga majina ta haɗa. Miƙewa nayi na fice a falon. Wallahi itace har gaban motata, tana rusa kuka mai gadi yana kallonta. A wajen na tafi na barta. Ina tuƙi idanuna na lumshewa da kansu. Sai murmusawa kawai nake yi, ina haɗa dalilan haɗuwar iskancin mijinyawa da Asama'u. Wato ashe duk irin tarbiyyar dana ba Asama'u har tasan taje zangon baƙi, har kuma tasan yadda ake zarge wuyan wanda aka kama yana aikin da baya son a sanshi. Amman dai mijinyawa an yi baƙin ɗan iska, ƙaton banza da wofi. A daidai ƙofar layinsu Luba na tsaya, na kirawota ta fito muka wuce. Asibiti muka wuce kai tsaye isowar baristan da muka yi zamu haɗu kenan, tace tana cikin wata jar mota tana shirin fakin mu kuma muna kusa da motar. Tana gaba muna bayanta muka shigo asibitin. Tare muka fito a motar. "Wai Hindu Nagoɗi ashe da gasken dai ke ɗince, naga sunan, amman inata tantamar ko sunane ya zama ɗaya. Ga Lubabatu madaki ma wannan ƙawance da girma yake ashe har yanzu kuna tare" Saudatu Mustapha wai dama kece lauyar da muke waya dake? Luba kinga ikon Allah" Saudatu Mustapha ƙawarmu ce tare muka gama sakandare da'ita wajen zamansu ɗaya da Luba. Yawan zuwa wajen Luba ne yasa nima na zama ƙawar Saudatu. Amman dake mu gidanmu bamu fiye yin ƙawayen waje ba yasa inaga Saudatu bata taɓa shiga gidanmu ba sai dai tazo wajen Luba mu haɗu acan. Akazo kuma Aure ya rabani da Kano. "Lubabatu kinga Duwaf ai ba zata canja ba baki ji wai Saudatu take kirana ba? " Luba ta kwashe da dariya tace. "Ai sai ta tuno mun da lokacin da a makaranta in