← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 85

Sashe 56

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Ciɓiri nannagi kenan
Mu kwana anan sai in Allah ya kaimu gobe.
Amman ba lallai in yi sabon shafi gobe ba ƙila sai monday, idanuna ya tasamma ciwo yana buƙatar hutu, amman sai yadda ta kaya dai.
Mrs BUKHARITSURON TSIRIN...
TSANDAURI...

LITTAFIN
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI

LAMBA TA GOMA SHA BIYAR

INA GODIYA A GAREKU MASOYANA NA FAÆŠIN DUNIYA.
IDANUNA ALHAMDULILLAHI INA SAMUN SAUƘI. NAGODE SOSAI DA ADDU'O, INKU SON SO💪🏼

MIJINYAWA:

Asibiti_

Yana zaune idanunshi sun kaɗa sun yi jawur kanshi ya ɗauki zafi sosai, duk wata fireja ranar tana kanshi ba sauƙi.
Ga Mijinyawa Babba da Gambo duk ya kirasu sun baro wajen aikinsu suna tare. Mijinyawa Babba ya É—aga wayarshi ya sanarma Æ´an jama'are halin da ake ciki.
Wai Hindu ta daki Nanno da Yaya Jamila, gasu a asibiti cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai.
Sai huci kawai yake yi, yana ji tamkar ya rufe Mijinyawa da dukan mutuwa ko hankalinshi zai kwanta da ɗan samu sassauci na dangane da abinda yake ji, ga wutar ɗaukar fansa sai ruruwa take yi a zuchiyarshi. Gambo kuwa dake shi a ƙasansu yake ya birne abunda ke ranshi, kawai ya ɗauki idanu ya zuba.
Gashi Mijinyawa sai kiran Azgar yake yi yana jin ya jikin Hindu, lamarin daya fusata Mijinyawa Babba yake jin an ƙure gejin haƙurinshi ya ƙare, ya zare wayar a kunnen mijinyawa ya rakaɗata da ƙasa ta fashe.
Da idanu kawai ya bishi bashi ba tacewa.
"Sabida iskanci mahaifiyarmu ba lafiya tana ciki likitoci na kanta, bamu san halin da take ciki ba amman ta matarka kake yi sabida tambaÉ—aÉ—É—ene, kai sallamamme, wanda Hindu ya rako duniya. Matar da itace silar faruwan duk abinda ya faru, har baka jin tsanarta a ranka sai kiran yaro kake kana tambayarshi jikinta me kake nufi, nace ubanme kake nufi damu ne Mijinyawa. Anya kana da kai kuwa?"
"Amman kai baka san aljanunta ne suka yi wannan aikin bane? Nayi imani da Allah ko giyar wake Hindu ta sha ba zata iya ma Nanno wannan abun ba, gara ma Yaya Jamila tunda taƙi fur ta kama girmanta, sannan akanme zanga lefenta ai wallahi ko ina akace muddin iyakar gaskiyar za'a tsage to bamu da tace wa. A wannan halin da Hindu take ciki babu wanda ba zata iya duka ba. Kada ka shiga surutan mata har suyi maka tasiri ɗan uwana. Ka fahimceni, ka fahimci Hindu."
"Wallahi baka isa kareta akan abinda ta aikata ba. Gawata ko dai da gasken dai asirin Hindu tayi makan kamar yadda aketa faɗa ne? Ahh asirine wannan nima yau na tabbatar da haka. To bari kaji in faɗa maka aurenku dole ya ƙare, babu wanda zai karɓi abinda tayi kana taci gaba da zama a cikin rigar alfarmar aurenka ba, kana ta hidimta mata, dukiyarka da rayuwarka duk akanta ka ƙarar. Sarki mai Hindu jibi yadda ka rame dan jarabar son Hindu daka ɗaurama ranka. Inna hanga na hango sai ince ribar mai ka tsinta a wannan ƙaddararren Auren. Ya zame maka dole ka rabu da'ita ko kuma a tsameka a dangi, wallahi sai dai ka zaɓi ɗaya ahh iskancinku yayi yawa, ina mahaifiya fa"
A fusace ya miƙe cikin ɗaga murya yace.
"To sai me a tsameni mana Nawata. Hindu dai a ko'ina akaje zan kareta tunda uwar ƴaƴanace, kuma bata cikin hayyacinta tayi abinda tayi. Sannan in an bi ta ɓarawo abi ta mabi sahu. Yaya akeso in yi ne, wai me muka yi muku ne.
Shikenan sabida dai Hindu ta yadda ta aureni ina ɗan ƙauye, wanda na kaita ƙauye muka rayu.
Ko kawai sabida ta samu jinkirin haihuwa a farko kuma daga biyu haihuwar ta tsaya shine matsalarne, ko kasancewarta ma'aikaciya shine matsalarne Mijinyawa, ko sona da take yi nima nake sonta muna zaune babu mai jin kanmu shine matsalar ne?
To bari kaji kada ka sake shiga sabgata da matata, domin bana shiga sabgarka da Uwatale. Bama kai kaÉ—ai ba, bana son kowa ya sake shiga sabgarmu ni da iyalina. Ni dai a barni in huta in ba haukacewa kuke da burin kuga nayi ba, ace muku gani ina yawo tsirara ba. Haba haba, wallahi turarnan ta riga da tai kuma kaini bango.
Ohh so kake in dena kira ina tambayar jikinta, tunda ba hakkina bane kula da lafiyarta ba ko, in uwatalene kenan ba zaka yi ba? To ni zanyi kai da kake bagidaje ɗan ƙauye a soyayya sai kar kayi.
Dan kana abokin tagwaitakana ba yana nufin ka takani son ranka bane. Bama ka isa bane.
"Ƙarya kake wallahi saika saketa maras mutumci, wanda baya kishin dangi"
Mijinyawa yace.
"Tunda kaine Ubana ba ai dole ka haƙiƙance, kasa in rabu da matata, sannu Baba"
Ya koma ya zauna ya adana layin wayarshi a ajjihunshi.
"Ni kake faÉ—ama haka ina matsayin Yayanka? "
"Laa gware muka yi muka zo duniya, Nawata kana mantawa son girma na rufe maka idanu, baka girmeni da komai ba. Kayi haƙuri kayi shiru bana son jin muryarka wallahi Allah, ka riƙe matsalolin iyalanka sun isheka, ka barni inji da ciwon mahaifiyata da matata"
Ya ja bakinshi ya tsuke ba tare daya sake cewa uffan ba.
Mijinyawa Babba kuwa ai da wa Allah ya haɗashi in ba Mijinyawa ba, yaita amayar da maganganun da suka jima a ƙasan ranshi wanda uwatale take tattarewa tana faɗa mishi, ya jima da jin haushin ɗan uwan nashi wannan haihuwarsu da akayi tare, tasirinshi ke danne jin zafin da yake yi akan ɗan uwan nashi. Burin uwatale ya gama cika yau sai dai ta saka ruwa a ƙasa ta sha.
"Gambo kaine shaida in har Gawata zaici gaba da auren Hindu babu ni babu shi har gaba da abada, kuma bana fata da sake ganinshi a rayuwata, bazanje inda yake ba, kar ya sake ya sake zuwa inda nake. Ku in zaku yi zumuncinku kuyi"
Gambo ya buÉ—e baki yace.
"Nima h...... "
Kallon da Mijinyawa ya watso mishi ne yasa ya tsuke bakinshi yayi shiru bai ƙarashe ba, likita ne ya fito da zummar komawa ofishinshi, suka miƙe du su ukun suka nufeshi.
"Dakta ya cikin nasu? "
"Da sauƙi ita Mama sai anyi mata hoton bayanta inda take kukan ciwonshi gashi ya kumbura sosai ma. Mun dai mata allurai yanzu haka tana bacci, amman a gaskiya tana jin jiki, ayi ta adda'a. Ɗayar kuma Dr yana kan dubata zai fito ba da jimawa ba. "
Haka wannan ahali sukai ta zama cikin maganar kurame har kusa da Azahar, Uwatale ce ta kawo abinci bisa umarnin mijinyawa Babba, da goyonta a baya.
Ta zuba ma Mijinta, kana ta zuba ma Gambo, tana ƙoƙarin zaran wani kwanon taji amon muryar mijinta irin amon da ita kanta bata san ya mallaki irin muryar ba.
"Wa kike yinƙurin zuba ma abincin nace? "
Cike da mamaki tace.
"Abokin tagwaitakarka wanda bashi da tamka a rayuwarka"
Sai da ya haÉ—iye abincin bakin shi kana yace.
"Kul kika zuba mishi kamata yayi daga gidansu Hindu a kawo mai abinci, su gatantashi kamar yadda ya ƙare a ƙarƙashinsu, baya ji baya gani."
Har a fuska Uwatale ta kasa ɓoye farin cikinta, wannan ranar take jira sai gashi yau ranar tazo Mijinyawa Babba ke cewa kada a sama Mijinyawa abinci? Tab duk abinda zaisa Mijinyawa Babba yace haka ga Usainin da bashi da tamka, to babbane. Cike da jin daɗi gami da kannewa tace.
"To amman Baban Zainab mijinyawane fa naka, kuma naji shima ance wai Hindu na kwance babu lafi... "
"Kada ki sake kiran sunan Hindu a gabana in ba haka ba zaki karɓi hukunci mai tsanani, kinji na faɗa miki. Ki shiga ki tadda matar Gambo ku zauna tare da su Nanno, ba ki zauna kina son jin ba'asiba Munafukar banza da wofi."
Murmushin gefen fuska Mijinyawa yayi kawai yaci gaba da ƙoƙarin kiran abokinshi Qasimu, yana hanyar zuwa tare da su Yaya Zakiya. Labarta mishi yadda ƴan jama'are suka ɗauki lamarin yake yi, sakamakon sun tsaya cin abinci a wani gidan mai shike riƙe da tuƙin motar, ɗan sanyin da Mijinyawa yaji jin an tawo tare da Kawu ne kawai, duk da ƙasan zuchiyarshi cike da taraddadin ya kawun zai ɗauki lamarin yake, ta yiwu ya ɗauka da sauƙi kamar dai yadda ya saba, ta yiwu ya ɗauka da zafi kasancewar yasan dole al'amarin da girma. Amman bawai kare Hindu yake yi ba, kare gaskiya kawai yake yi.
Hindu bata da laifin komai ko sanda aka shiga da'ita gidanma bata san inda kanta yake ba.
Wucewa yayi zuwa masallacin cikin asibitin yayi nafila, ya jima goshinshi a ƙasa yana munajati da Ubangijinshi.
Haka a zaman tahiya yaita faɗama Allah damuwarshi kan ya shiga lamarin ya taɓa, kafin dai ya sallame. Yayi sallah azahar yana kan sallar tare da tsirarun mutane su Mijinyawa babba suma suka shigo ko da ya sallame zama ya gyara, yaci gaba da ambaton Allah, can kuma yai kurum yana tuno irin rayuwar da suka shinfiɗa a baya.
Wata rayuwace tamkar ta turawa tsabaragen fahimtar junansu, amman kash yau gashi ya rusa duk yaddar dake tsakaninshi da Hindu. Tuno wata rana yayi da rana ƙwal ya dawo daga wajen aiki da cefane Hindu na zaune a tsakar gida tana mishi wankin kayanshi, Azgar na tsaye a dokin ƙofa da motar roba mai ruwan omo a hannunshu, Asma'u kuwa tana bayanta tana ta sheƙar baccinta.
Ganin shigowarshi yasa Hindu ta taso da saurinta tana goge kumfar hannunta a zaninta.
"Sannu da zuwa ya akayi ka dawo da wuri haka? "
Ta tarbeshi da kayan ta kai madafinta na langa langa dake manne a ƙofar ɗakinta.
"Wash Allah ke dai bari Tutar so ai dole in dawo nasan ban ajjiye miki komai a gidan ba, in ba garin kwaki ba, cefane na cefano mana ki ɗakko ki bubbuɗa. Azgar tawo to" Ya ƙarashe zancan da miƙa ma Azgar hannu, yana zaune a kan kujera ƴar tsugunno ya tawo ya hau cinyarshi ya zauna. Hindu kuma saida ta kawo mishi ruwa mai sanyi, kafin ta ɗakko ledojin cefanen da tiren silba, kujerar da take kai tana wanki ta jawo ta zauna ta soma bubbuɗa cefanan. Kayan miya ta soma gani tattasai, attaruhu, tumaturi, albasa mai lawashi. Ɗayar ledar shinkafa ce gongoni huɗu da wake gongoni ɗaya, sai farin mai rabin gongoni, maggi mai tauraro guda goma sha biyu lokacin yana shida goma sai maggi ajinomoto leda ɗaya lokacin yana nera goma baidan kuma nera biyar yake. Sai bushasshen kifi karfasa.
"Ahh yau dawar tayi mai Mijinyawa Ubangiji Allah ya ƙara maka buɗi da wadatar dukiya data zuchiya."
Murmushi yayi mata yana kallonta da kyau.
"Hindu baiwar Allah ban kawo miki abinda ya taka kara ya karyaba, ba jan nama, ba kaza amman sai murna kike yi wai harma dawa tayi mai. Hmmm Ubangiji Allah ya nuna mun ranar da zan dinga cika kaji da naman kasuwa a gidan ƙanƙara da kayan miya, abinci cikin sito, sai yadda kika so haka zaki yi. Ga injin ganin haske ga komai na ƙawar rayuwa, Hindu kici ƙoyi ki kora da haɗin murtuk, ki daki mummuƙi yadda kike so"
Dariya suka yi dukkansu daidai lokacin Asama'u ta tashi a bacci ta shiga canyara kuka.
"Suntota macen duniya, ga kuma soja an sai laɓewa yake a jikina, wannan yaron anya zai zama sojan kuwa? "
"Aiko dai yana da sanyi da yawa fa. Kuma Akarami da gaske so yake Azgar ya shiga soja hatta Baba sojanmu haka yace"
Ajjiyeta tayi a cinyar uban, ya karɓeta ya shiga yi mata wasa yata dariya. Hindu kuma ta tsaya kallonsu tana ayyana wani abu a ranta dangane da Mijinyawa da yaran duka.
"Yau kam na tashi aiki, har Shehulle ya fita da motar. Sai dai zanje kantin Alhajiji kamar dai yadda aka saba ko na karin safe ma samu ko tutar so, ko bakya son ɗan ƙoyin da Alhajiji yake ƙunsowa yace a kawo ma uwargida ta soya ma yara"
Dariya suka yi dukkansu mijinyawa ya miƙe yai musu sallama ya fita yana ta zuba warin rana to yanayin sana'arce dole sai da warin rana, duk tsabtar mutum danma Hindu na rage mishi ƙarfin warin ranar da ruwan alim ko ta goga mishi lemun tsami a hammatarshi ta dirje mishi, kuma bata barin hammatar tashi da gashi sam duk sati take aske mai ta yanke mishi faratunshi."
Chapter 56 · 0% Book details