Sashe 59
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jahilci akace yafi hauka ciwo inji masu iya magana. In da ranka akace ka sha kallo. Wallahi yau dangin mijinyawa sun kankaremun haddata tas. "Menene haka Yaya Zakiya kuke yi iye? " "Abu ta kazan.. Muke yi ɗan ta abu kaza kazan wanda yaima kazan dan ta kazan.... Ashe babu daɗi mu ta dakar mana uwa? Wallahi babu abinda zai hana mu bata kashi a gidannan, kai in bakai wasa ba har kai zamu haɗa mu doka wawa wanda baisan zafin uwarshi ba, sai zafin Hindu da iyayenta ko? " Tana kaiwa haka ta yo kukan kura wai zata nufo ni. Baba Sojanmu fa yana tsaye ya harɗe yana kallon komai. Innarmu kuwa tazo wuya_wuya. Mijinyawa yayi carab ya riƙeta suka shiga kokawa a ƙoƙarinshi na hanata ƙarasowa gareni. Dambe ƙaƙas a tsakaninsu, bai hanata dukanshi ba, bai kuma yadda ya rama dukan ba, kariya ce yake bani kawai. Ni ko uwatale ma nake hari wallahi. Baba sojanmu ya dubeni da kyau tare da nuna mun Mijinyawa da Yaya Zakiya. "Irin abubuwan da akaita ji miki kenan, amman sam kika kasa ganewa. yanzu in ba jahilai ba wa zai aikata abinda ƙauyawan matannan suka zo suka aikata? A ƙofar gidanki fa har maƙota sun soma leƙowa, burinsu su yi inbarasin ɗinki, wandaful ji wannan yadda take faɗa da mijinki? Wanda shal neba ent" Shiru nayi kaina a ƙasa kawai, a lokacin inda za'a tsaga jikina ba za'a tadda jini ba. Ji nake jikina na wani irin mazari. Luba na ƙoƙarin ƙarasawa wajensu Uwatale da suke zage zage suna cema mijinyawa ya sake Yaya Zakiya, Baba sojanmu yai mata daƙuwa. "Ungo naki Lubabatu, ke kika haɗa balle ki raba? Ai Hindu zata iya na turustin ɗinta" Nuna mun su yayi halamun inje. Ai kuwa tamkar alakatane a hannunshi, nayi kukan kura na finciko Uwatale, kafin ta ankara na fusge goyonta na miƙo ma Luba. Habawa, cikin rufewar idanu na hau dukan Uwatale tako ta ina kuwa, musamman bakinta na gulma daya jima yana ƙulla sharri. Tama kasa komai, sabida ta tsorata a zatonta makarainane suke aikin, amman nice haukar gangan kawai nayi. Sai dai kash ana hakan na gasken suka kawo ziyara, ni dai inata jin ihu da ele a kaina kawai. Bazan tuno komai ba gaskiya. Sai can na ganni a gefe a zaune a dokin ƙofa Akarami na riƙe dani shi da Yaya Saratu. " Gud Hindu, gud, Ku shiga ku sako mayafinku mu wuce asibiti, Hindu ta dubo surukar tata" Shigewa ciki muka yi hayaniyar sai sake tashi take yi, maƙota fa duk sun yi cirko_cirko a bakin get. Innarmu bata ce uffan ba, amman naga jikinta yana ta kaɗawa, Baba Sojanmu ya riƙe hannunta gam. Luba kina ganin irin abinda dangin mijinyawa suke yi, ssu inga kamar basu da cikakken hankali fa. Wai shin menene musamman da yawa_yawan gabar da take tsakankanin dangin mata da dangin mijine? Nifa a duk binciken da nayi, da karatukan dana yi bincikena ya nuna mun dangin miji kishine da baƙin cikin matar ɗan uwansu, da mugunta itace ta cika fal cikinsu. Muddin za'a ganki cikin suturar arziki ke da yaranki, miji na ji daku, kina zaune a muhalli mai kyau, ba'a ganinki kina cin abinci mara kyau, kina ɗaura sutura mai kyau, mijinki na da rufin asirinshi. To idanun danginshi rankatakaf yana kanki sai kiji wani a gabanki ana cewa ai wance kin miƙe ƙafa da yawa aure zamu yima wane gaskiya. In kuma aka ganka a wahale miji na wulaƙantaka, babu abun dariya da gulma da zunɗe kamarka. Wai yaushe wannan al'ummar tamu ta lalacene. Wai yau ni Yaya Zakiya dasu Uwatale suka yo zuga wai zasu dakeni har cikin gidana." Ai sai na sake zaburewa inason in fita in kuma haɗama Uwatale jini da majina. Luba ce ta ƙanƙameni. "In kina ma Allah ki rabu da Uwatale haka, Hindu duk kin farfasa mata baki fa. Wallahi da kika finciko goyonnan, kamar zuchiyata kika finciko na zaci makaranki zasu doka yaron da ƙasane, yazo ya mutu mu shiga bakin duniya, sai suka miƙo mun bayan sun karyamun ɗan hanun nawa. Wata dariyar takaici nayi ina ɗaura ɗankwalin doguwar rigar atampar dana zura. "Ni mijinyawane ya bani tausayi Hindu, bawan Allah dame zai ji ke ba shiri kuke yi ba. Da ƴan uwan nashi ba shirin yake yi ba. Ke baki lura duk ya rame ya lalace bane wai? " Kasaƙe na nayi ina hararar Luba mamakin kalaman tausayin data nuna ma mijinyawa na kamani. Ko da yake dama dai mu muke ba da kanmu. Nace shi Sunusi bakya jin tausayinshi ne Luba? Ki bashi dama mana yaci gaba da yin tamaule da rayuwarki, tunda ke ƴar iska ce. Dallah ni bani waje" Na tureta nayi wucewata ta biyoni mayafi a hannu tana dariya. Ashe Kawu ya'iso shi da mijinyawa Babba suna tare da Baba Sojanmu. Ganin Uwatale a wannan yanayin, anata wanke mata jini a fuskarta, ai sai ya cacimi mijinyawa da damben rashin mutumci. To in ƙarfine dai ya fishi, gaskiya ya dakeshi sosai, duk da shima ya daku babu laifi. Kawu sai kiran sunayensu yake yi. Baba Sojanmu yanata ambaton wandaful, wandaful wandaful. Da ƙyar ƙurar fa ta lafa wallahi Allah. Jagorantarsu Mijinyawa yayi zuwa cikin falona, bisa umarnin Kawu. Muma akace duk mu shiga Yaya Zakiya kuwa, sai da Kawu ya zazzare mata idanu ta wuce tana runtuma kuka kamar wacce akace ma Nannon mutuwa tayi, ohh in ba mutuwa bawa yayi ba yayi ta haɗuwa da abubuwan almara kenan. Baba Sojanmu da ƙyar siɗin goshi ya amince ma Kawu suka shigo, sai turanci yake sakarma Kawu, shi kuma kawu ba bihim. A ƙasa duk muka zazzauna mata_matan mazan duk suna sama sai Innarmu da take sama itama, ƙafarta ɗaya bisa ɗaya. Kawu ne yayi gyaran murya yace. "Dattijo ayi haƙuri dan Allah kasan sha'ani na mata, wani sa'in ragaggen tunani garesu. In ba haka ba taya Zakiya zata jagorancesu suzo dukan matar ƙaninsu, akan abinda su kansu sun yadda Hindu ta aikatane ba'a cikin saninta ba. Ayi haƙuri Kema Hindu, da kai Mijinyawa ƙarami, kuyi haƙuri tayar muku da hankali da akayi da safe haka. Kai kuma Mijinyawa Babba ka cika tabbatacce wato ashe kaima a bayan matarka kake. To mana daga shigowarmu dan ka ganta cikin jini sai ka hau kokawa da abokin tagwaitakarka, anya kuna da lafiya" Baba Soja yace. " Well, To wai in ba dan shi mijinyawa yananan ba dukan ita Hindun zasu yi, su zo har gidanta. Shin a doka sun san menene hukuncin ka biyo mutum har gida kace zaka dokeshi kuwa? Shiga gidan wani wanda a turance muke kiranshi da ( Housebreaking/Burglary) In da ranane mutum ya shiga gidan wani da zummar ya dokeshi, ko aikata wani babban laifin zai iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekaru tara zuwa goma a kurkuku. In da daddare kuwa ya shigo, kuma akaci sa'a laifin da yazo da zummar aikatawa ya aikatan to fa doka na kiran wannan da Burglary, kana hukuncin na iya kaiwa ga ɗaurin rai da rai ma baki ɗaya. Duk da basu aikata abinda suka so ba, ma'ana basu taɓa jikinta ba, tana da hakki a bisa ɓata mata sunanta da suka so yi, sabida dukan ƙofarta da sukaita yi, da hayaniyar zage_zage yasa maƙota sun firfito ga firgitata da suka yi, dis is an insolt, Sannan ko kotu muka kaisu sai anci tararsu kana kuma su sha ɗauri. Bazan yadda da wannan ƙasƙancin ba. Shi nou ha rait, kuma zan tsaya mata, Yayanta zai tsaya mata. An den ko da Hindu ta kashe waccan baƙar ta kar banza, sabida su suka take doka suka shigo mata, ai sun shigone da zummar dukanta wanda hakan can tek ha lif u nou" Murmushi nayi dan naji daɗin wannan bayani na Baba Sojanmu, kuma gabaki ɗayansu babu wacce bata ruɗe ba. Bare suna ganin Akarami da kakin sojoji a jikinshi,sun san duk abinda yake faɗa zai iya samun su. Kawune yace. "Assha Dattijo ayi haƙuri, ai rashin hankaline kawai irin na mata da shashanci in ba haka ba ina Zakiya, ina yin zuga da zummar dukan matar ƙaninsu. To yanzu da abinda suka zo da niyyar yi ya yiwu kuma fa? " "Ai Baba da yanzu wani labarin akeyi, domin gaskiya da wallahi ba zamu yadda ba, sabida Hindu abinda ta aikata a bisa rashin lafiya ne, kowa ya sani. To damme su da hankalinsu zasu zo suce zasu doketa, sabida itace mara gata ko me ake nufi? Tana da cikakken gatanta wallahi, da sun taɓata a nanne zasu gane gatan nata dan wallahi gidan yari kam sai sun cita ko wanne matakine zai biyo baya na dangane da aurenta bazai dameni ba. A yanzun ma sun taro mach tunda ai sun shigo, sun kuma yi yinƙurin dukanta, basu ci nasara ba ita wacce ta daki mijinta, shima wannan ai ya dakeshi on ha bihaf, sabida haka ba zamu bar wannan maganar sasakai ta wuce ba" Cewar Akarami da ranshi yai masifar ɓaci, Mijinyawa yace. "Balle wannan lamarin bazai taɓa auren Hindu ba, muddin nine mijinta. Zan iya shaidar tarbiyyar Hindu a gaban idanunta da bayanta, da gangan kuma cikin hayyaci ba zata taɓa aikata abinda ta aikata ba. Suma rufewar idanune abinku da an taɓa mahaifiyarmu. Amman ni da Kawu muna masu bada haƙuri Baba Sojanmu Innarmu, Akarami, Yaya Saratu, Luba, da ma Hindun ayi haƙuri" Baba Sojanmu yace. "Am furoud ob u Mijinyawa, ka nuna mun kai tsayayyene akan Hindu, kuma kana da ra'ayin kanka. Amman uhmm lallai zamu ɗau mataki." Kawu ya daka ma Yaya Zakiya tsawa wacce jikinta duk ya mutu yace. "Ki ba Hindu da iyayenta haƙuri yanzunnan, ko kuma in sassaɓa miki. Jamila tana can wuya a kumbure amman bata dena haɗa husuma ba. In banda neman sale salin magana ma, a wajen Uwatale da mijinta yafi cancantar su zaunane ko a nan wajensu Mijinyawa ƙarami domin Allah?" Sai nace dashi. Ballantana Kawu wannan gidan nawane, nice mamallakiyar gidan, ba gidan Mijinyawa bane, takaddun gidan sunane a jiki, lokacin dana sai gidan shi baima sani ba. Yana da kyau ku sani, sabida halin rayuwa naga abun ya wuce gona da iri" Mijinyawa ya dubeni, kafin ya dubi Kawu yace. "Gaskiya ne, gidannan, da motar da take