← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 85

Sashe 80

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sallama na shiga na sameta a gurfane tana sharar hawaye. Shekarunta a ido ba zata wuce shekaru arba'in haka ba dai. Ga wata ƴar takadda a hannunta. Waje na samu na zauna muka gaisa. To gani nasan zai yi wuya ace lafiyace zata sa ki dogo irin wannan muƙu_muƙun sammakon. Ina saurarenki" Na ƙarashe maganar ta ƙarshe haɗe da jan numfashi. Tun jiya gabana yake faɗuwa, a kan dadduma na kusan kwana ina sallah, da yin salatin ma'aiki Arrasul s a w, kan ya sassautamun, ya cire mun kewa, ko jin ƙulafacin yarannan da zasu tafi a zuchiyata. Na ɗaga hannu nace da Ubangiji na. Allah kana gani ni akaima laifi, kuma nayi haƙuri. Allah duk macen kirki biyayya dole ne a gareta taima mijinta, Allah kai ka haliccemu, ka yomu jinsi biyu. Allah kai ka ce muyi Aure domin bin sunnar ma'aiki arrasul s a w. Allah kai kasan dalilin da yasa ka sanya saki a tsakankaninmu. Kuma aurenma ya kasance ba dole ba, madamar mace ko na namiji, zasu iya riƙe kansu ba tare da sun aikata zina ba. Allah kai mai adalcine baka son azzalumi, Allah kana gani bazan taɓa iya ci gaba da zama Mijnyawa ba, bazan taɓa iya sonshi a karo na biyu ba, bazan yarda dashi ba. Ya Allah kana ganinshi yanaso ya ruguzamun rayuwata, ta hanyar rabani da ƴaƴana. Allah ka bani haƙurim rasasu da zanyi, Allah ka ƙara ƙarfafamun zuchiyata kasa kar in raunata. Allah kai musu albarka, ka sadasu da mutanen arziki ya Allah" Nayi adda'ar da bansan iyakarsu ba. Muryar baiwar Allahn dake gabane ya dawo dani daga dogon zango dana tafi. "Anty haƙiƙa na zalunci kaina, na cuci ƴaƴana, gashi rayuwata tazo ƙarshe shikenan." Kaico, me ya faru da har kike yanke tsammani da ci gaban ruwaya? Tsanani ba mutuwa bane. Faɗuwa ba yana nufin gazawa bane, jarabawace daga Allah, in kikai tawakkali in Allah ya tashi ɗagaki zaki yi tsaiwar da babu mai iya kai ki ƙasa. Duk abinda kika ga rayuwa ta baki, ɗaukeshi a matsayin jarabawa, ko ƙaddara. Kinga wannan biyun? Sune abokan tafiyar rayuwa, dole dasu muke rayuwa" Kuka ta fashe dashi na raɗaɗin abinda ke mata zugi a ruhinta. Shiru nayi ina lumshe idanuna gabana yana ci gaba da tsananta bugu, yarane sune rayuwata amman bana jin mijinyawa zai karyani ya tanƙwarani ta hanyar amfani da yarana. Nayi imani da Allah yayi ne kawai domin ya tilastamun binshi Katsina. Hmmmm maza da yawan san kansu shi ne matsalarsu. "Anty na jima da sanin mijina yana biyar matan banza na kama a waya. Abun tashin hankalin shine yadda naga mata da yawa da yakemu'amala dasu, da yadda yake biyansu kuɗin zunuban nasu. Babban kuskuren da nayi shine rasa tudun dafawa, da tuno makomata data ƴaƴana. Anty ban rasa duk wani jin daɗin rayuwa ba a gidan mijina ba. Ina samun ci sau uku a rana, kuma ko abinci ba nama bana ci. Sutura ta alfarma inna shiga cikin matan abokai nasan ba'a fini gata ba. Gidana mai kyaune, yarana suna karatu mai kyau. Naso daya aureni tun kan nayi haihuwar fari in koma makaranta, sai ya nuna mun baya sha'awar macen da tayi digiri, sabida buɗewar idanu. Dalilin da yassa ya auroni kenan. Masu digiri ɗin nemanshi suke ya auresu yaƙi. Na haƙura, sai nace zanyi sana'a bayan na haifi ɗiyata ta fari har ina da cikin ta biyu. To nan ya dinga mun faɗan wai zan zubar mishi da mutumcinshi, da kamarshi, ace matarshi na siye da siyarwa." Majina ta ja sama idanunta kaca_kaca da hawaye. Saida ta saisaita kanta ta ɗaura cewa. "Anty kasancewar nasan bani da gata kuma gani a cikin rufin asiri. Yasa dana kamashi a waya da ƴan matanshi na kasa magana. Shi ban tunkareshi ba, a gida ban kai kukana ba. Ƙawata dana faɗa mata sai cewa tayi ita mijinta da maƙociyarsu bazawara ta kamashi a kan gadonta. Amman tana zaune sabida bata da inda zata je, kuma inta rabu dashi ƴaƴanta fa. Hmmm shawararta nabi na ja bakina nayi kurum Anty, sai na dinga tashi ina mishi adda'a, duk na rame na fita hayyacina. A sanadiyyar damuwar dana shiga da rashin baccin da nake fama dashi na kusan shekaru uku cur, dan na kamashi lokacin da ciki a jikina, harna haihu shekara biyu na yaye na samu wani cikin na haife. Ina dakon baƙin ciki, na kusan shekaru shidda. Kwatsam ciwo yaita cina, inata sunturin asibiti jiki yaƙi daɗi to jiya dai aka tabbatarmun ina ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki wato cida, ƙanjamau, HIV Anty." Ai sai kuka ya kubce mata tai ta rabzarshi, har saida mijinyawa ya bar abinda yake yi ya leƙo. Ni nayi jigum na tusata a gaba. Ita tana zaune ta cusa kanta a tsakankanin cinyoyinta kawai kukan fitar rai take yi mai zugi. "Hindu lafiya take irin wannan kukan? " Wani mugun kallo na bishi dashi wanda wallahi saida na hango ɗan tsoro a fuskarshi. Lamarin shi da Asamu'u ya dawo ɗanye. Kunsan dai tashin miki tsoho yafi sabon miji zugi, dama wuyar sha'ani. Sai naji numfashina har wani karkatsewa yake yi. In buɗe baki inyi magana na kasa, ji nake uwa in nayi magana mutuwa zan. Wucewa yayi babu guiwa, nabi bayanshi da hararar baƙin ciki. Kinga kuka duk ba naki bane. Amman kinyi kuskure irin kuskuren da nake ji tamkar in rufeki da duka ko zan huce. " Miƙewa nayi tsaye naje na kulle ƙofar falon na shiga zagayawa hannayena goye a bayana. Sabida baki da tudun dafawa kika zauna da miji mazinaci, har yaje ya kwaso cuta ya kwasa miki kina ji kina gani, ke ba ƴar iska ba, ke ba komai ba. Sabida ana baki ci da sha da tufafi mai tsada ko? Wannan duk abubuwan da kika lissafo ba hajja bane na ki zauna da miji mazinaci, kuma kinsan mazinacine ba. Ba gara ya sakeki, dangi da iyaye su ƙi ki ba, amman kina da lafiyarki. Kinsan matsayin lafiya da arzikin lafiya kuwa? Kin zauna kin kamu da hawan jini, kin samu cutar ƙanjamau, kuma gashi a yanzu na tabbatar sakin kike nema, wanda a baya ya kamata ki nema da lafiyarki. Wai mata me muka ɗauki zawarci, da mutuwar aurene? Shikenan su maza duk kwaɗon da suka daka haka mata zasu shanye. Ko sun ƙi ko sunso ne. Me yasa muke kashe rayuwarmu, sabida makomar yaran da ke idoce a tarbiyyarsu kawai, shiriya kuma a hannun Allah take. In kika faɗi kika mutu shin kinsan yar'dda zasu rayu ne? Cikin faɗa nake maganganuna, ina jin matarnan kamar wani ɓangarene ita na jikina, ina jin makamancin irin zafin da take ji a ƙirjinta. Sassauta muryata nayi tare da cewa. Yanzu ga abinda kika samu a sakamakon haƙurinki, cikuwa biyu masu durƙushe rayuwa. Bance Allah ba zai saka miki, ko ya duba miki akan haƙurinki, ko zaluntarki da akayi bane ba. Amman wannan ƙaddarar kusan ke kika gaiyatota, da a lokacin da abun ya faru kin nemi sakin ki, kin kuma sa a zuchiyarki zaki fita kina da yaƙinin Allah zai miki mafitar da ya fi miki wannan baiwar Allah. Nayi mamakin ƙawarki data baki wannan gurguwar shawarar, kuma itama ta zauna da mijin data kama da mace a gadonta. Mun mayar da kawunanmu dabbobi, jahilci, da ƙauyanci yana farautar rayuwarmu, ya subhanallahi. To yanzu me kike so in miki? " Na faɗa muryata a maƙoshi, tare da neman wajen zama na zauna. "Shawara nake nema dan Allah ya zanyi. Ji nake yi na tsani kaina" Ai dole ki tsani kanki, shawarata kai tsaye shine ki nemi lafiyarki kawai. Domin a wannan gaɓar sakin bazai miki mafita ba. Amman mudding kika ci gaba da zaman to zaki iya mutuwa lokacinki bai ma yi ba, sabida baƙin ciki. Duk macen data kana mijinta yanaa zina ita da jin sanyi in dai a zuchiyane to har abada. Ko da rabuwar akayi kuwa, abun zai ci gaba da bijiro mata. Da za'a buɗe miki zuchiyoyin da yawa_yawan mata, da kinga mikin zinar mazajenshi cunkushe a ciki. A halin da ake ciki da yawa _yawan maza mazinata ne. Banfa ce duka ba bare a sanya mun jakar tsaba aita caccaka. Nasaan me nake yi sarai, kuma da ilimina, nasan duk yadda al'umma ta kai da lalacewa akwai nagari a cikinta. Musulunci bai yadda kayi kuɗin goro kace al'umma kaza dukka masu laifine ba. Ki nemi takaddarki ya sakeki in kina ganin haka kike so, amman ni banga amfanin rabuwar ba a wannan gaɓar da kuka kai ba. Ciwo dai ya shafa miki, ki haƙura ku ƙarashe juna kawa. ki mayar da kanki a kan shan magani, da zuwa asibiti akai_akai. Ciwon Sida ba ƙarshen rayuwa bane baiwar Allah, sannan duk tsanani sauƙi na bayanshi. Zan rubuta miki addu'o'in kije ki durfafesu, sannan in so samu ne a rana kiyi istigifari dubu, in zaki iya fin haka kiyi wannan sirrinane, zaki ga yadda rayuwarki zata sauya. Duk abinda kike buƙata zaki iya zuwa ki sameni. Sannan zan tallafa miki da jarin da zaki ɗan godara da kanki. Amman kiyi haƙuri ƙila har iyayenki su nuna miki ƙyama sabida lalurarki, amman in kika daure zai zama labari" Mun daɗe ina bata magana, ban barta ba saida ta karya ta huta, kana na bata dubu goma nace ta tafi gida. Alhamdulillahi a kullum ina godema Allah daya bani baiwar iya magana, da bada shawarwarin da al'umma suke amfanuwa dashi. Gani face_face cikin damuwa, amman gashi wannan baiwar Allah na sa ta fita harda musmushi a fuskarta duk da nauyin ƙirjinta. Wucewa ciki nayi, ina ji su Mijinyawa suna ta ɓuruntu, yana ɗakin Sabira ƙila taya ta haɗa kaya yake yi ohon mishi dai. Haka ranar na wuni tuntunini akan lalacewar wasu mazan da zinace_zinacennan da ya zame mana bala'i, tarbiyya ta lalace, na rasa daga ina aka samu gazawa daga iyaye mazanne, ko daga iyaye matanne, ko gwammatice, koko dattijan unguwane? Mu faɗama gaskiya matsalar daga tushe take tun farkon fari, a tarbiyyane matsalar, sai kuma wajen zaɓan miji ko matar auren. Ai tunda mukai watsi da koyarwar ma'aiki Arrasul S A W to matsala ma bamu ga komai ba gaskiya. Wajajen la'asar ina zaune ina shan magani, zazzaɓine naji yana tasomun tun
Chapter 80 · 0% Book details