← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 85

Sashe 54

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

istigafi nan ki tayi a rana kiyi sau fam taɓa sama, wallahi ko baki ɗaga hannu kin roƙi Ubangiji komai ba, Allah yana ji yana gani zai zama majiɓancin al'amuranki, abubuwa za suita zuwa da sauƙi a rayuwarku, harma aita cewa asiri kake yi nan ko Allah ka riƙe, ki ƙara da sallar walha, da tsaiwar dare, to Hajiya ai kin gagara ba dai mutum ba sai dai Allah wallahi, shi yasa surutun mai surutu baya tasiri a kaina, kushen mai kushe baya taɓa ni. Wannan na daga cikin sirrin Hindu wanda muka koya a wajen Innarmu, madallah da iyayenmu nagartattu, masu natija. Masu tambayar munyi Islamiyya wai ko bamu yi ba, kunsan Kanuri wajen karatun addini mun cire tuta. Tun muna ƙananun yara ƴan firamare mukai sauka, a gidanmu sai yaro ko yarinya ya haddace Qur'ani kafin ya shiga sakandare. Amman bama zuwa islamiyya, a gida aka samar da karatun, dama sauran littattafan da su wannan lokacin muns sakandare. Amsar ta fita? To shikenan. Innarmu ta koyar damu riƙo da addini a aikace, shi yasa ta gagara. Da Allah ta dogara, sai sanin darajar kai, sanin sirrin ƙamshi, gyaran jiki, ado da kwalliya, da girke girke baraitis wanda gidan yawa baisa tace ba zata yima mijinta ba, wai dan sabida mun yi yawa. Wannan kenan. Bayan mun yi sallah ina zaune inata lazimi, a cikin inda ɗakunanmu suke ƴan sanda su kai su kawo, mu dai mun yi shiru kamar ruwa ya cinyemu kwatsam ga yinwa ga wani irin rashin daɗi na jiki dana zuchiya sai wajajen tara da rabi aka zo aka buɗe mu. "Ke da ke da ke kuzo mu je" Ƴar sandannan ta nunamu muka taso saida na taimakama Hajara ta miƙe. Hajiya Biba tace. "In ta ɗauro ba'a dawo daku ba, gidana yana ceɗiyar ƴan gurasa layi na biyu gida mai lamba tamanin da tara, ko yaro kika tara kika ce a nuna miki gidan Hajja Biba komai da ruwanka, za'a kawo ki, nima ki bani adireshinki inma baki ɓullo ba ni da kaina sai in zo ai" A gurguje na bata adireshina muka fito. Luba da mijinyawa su na soma hangowa a tsaye, mijinyawa idanunshi a kaina, ni ko nayi kicin_kicin da raina ita kanta Luba sau ɗaya na dubeta ma, a wannan gaɓar ita nafi jin haushi. Ga Figo, da wani dattijo haka da wata mace kamar tafiyarsu ɗaya. "Zo ki saka hannu anan daga yau babu ke babu Hajara, kada ki sake shiga rayuwar gidan Figo, da ba dan mijinki ba da kotu ma za'a turaku ungo nan" Ya miƙo mini alƙalami, mijinyawa na kalla, na dubi Luba naƙi karɓan wannan alƙamalin dan wallahi sai naga abinda ya ture ma buzu naɗi. Yallaɓai na fi so a kaimu kotu, Hajara tamkar ƙanwa take a gareni cutarwar da wannan bawan Allah'n yake mata yayi yawa. In ban shiga kotu akan Hajara da Figo ba, zan shigar da ƙaran Figo akan ƙagen da yayi mini, ko kuma ya janye yanzunnan anan" "Hindu ki karɓa ki saka hannu tunda dai mijinta baya son alaƙarku. Hindu dubeni kinji? " Banza nayi dashi idanuna akan Hajara da take kuka. "Yarinya so kike ki gutsire mata igiyar auren nata ne? Ni mahaifiyarta ce, mu muka ɗaura aurenta da Yahuza dan haka ki fita sabgarta. Irinku ne masu hure ma mata kunnensu kar suyi zaman gidan miji, masu ta'adar yahudawa maƙiya Allah da ma'aiki." Murmushi nayi kawai na zare alƙalamin daga hannun ƴar dokar. Kinga a ina zan saka hannun, Mama Allah ya baki haƙuri? Amman wallahil azeem sai nayi sharia da Figo. Bazan kwana cikin sell a banza haka ba" Nayi tambayarne cikin zafi da ƙunan zuchiya. Wajen da zan sa hannun zan sa kenan, Hajara ta riƙe hannuna tamau. "Anti dan Allah kar ki saka" Ƙur nayi mata ina kallonta, tausayinta kamar zai halakani. "Kunji ba ta riga tayi mata huɗubar shaiɗan, tana son kashe mata aurenta alhalin ita ga nata soloɓuyon mijin shanyayye. Dan shanyayyene kaɗai lusari zai iya barin matarshi na wannan aikin" "Ya'isheka kada ka sake aibatani, ya ana ƙoƙari shawo kan matsala kana ta maganganu tun ɗazu, dan kaga ina tausarka" Nan rikici ya ɓalle tsakanin mijinyawa da Figo, saida ƴan sanda suka tsawatar musu. "Ki sake mata hannunta ko in miki baki wallahi" Cewar fa mahaifiyar Hajara. Hannuna na fisge dan baƙin ciki, inata tausar zuchiyata kada in mata rashin kunya, duk da haka bayan na saka hannun Maman Junaidu ma ta saka hannun ana bamu kayanmu nace. Mama ga Hajara nan a maidata gidan miji, in ya halakata sai ya kiraku yace sa'i yayi, ku sai kuzo ayi jana'izarta daku. Ku sani mu ababen kiwone da Allah ya baku, kuma akwai ranar da zamu tsaya a gabanshi ya tambayeku kiwon daya baku" Na fito daga cikin bayan kanta na fice waje ina ji tamkar in haɗiye zuchiyata in mutu, ni sai yafi mun, ga Hajara tana ta kuka sai kiran sunana take yi, nayi mata banza. Motata da na gani a can gefe wajen na ƙarasa na jingina, sabida tausayin da naji na Hajara kada in ƙara sata a cikin masifa yasa na jaye ƙudirina na son maka Figo a kotu, amman wallahi da ni dashi har kotun Allah ya'isa. Ina hangosu Mahaifiyar Hajara sai zaginta take yi, Figo kuma sai rikici suke yi da Mijinyawa, har yana dukan ƙirjin mijinyawa, Luba nata aikin ban haƙuri, bakina na taɓe na kawar da kaina kawai. Mijinyawa yazo da sauri ya buɗe mun motar na shiga baya, na zauna tare da rufe idanuna ko'ina a jikina rawa yake yi mun a haka Luba ta shiga motar mu ka ja. Tun suna maida zance ina jin muryoyin nasu a sama, wallahi kamar wasa kafin mu isa gida bana ganin komai sai duhu, ana haka inata ambaton Allah ni dai ban sake sanin inda kaina yake ba daga wannan ɗaukewar ganin, mutanen sun kawo ziyara sakamakon ɓacin rai su dama haka suke ko da yaushe. Kunji wannan ai ko?
Chapter 54 · 0% Book details