← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 85

Sashe 40

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

karanta. Na kuma danna muryar Salamatu a lokacin da take mayar da martanin da yasa har Innarmu saida ta sako a ciki, dashi kanshi ba tace yana tsoron Innarmu ba, da muryar Nanan Lungun Baba Nagoɗi da take ƙara zuga Salamatu tare da kambaba abun. Na kunna mishi muryar Yaya Saratu na martaninta ga Salamatu, da muryar Yaya Zubaina itama na martaninta, da muryar Khadijan Innah Mairamu duka dai. Na ɗaura da cewa. Iyakar abinda nasan na rubuta kenan. Dake akwai wani ƙulli a zukatansu shi yasa ta fassara kalmar da wani abun daban. Da kuma kike maganar baƙin ciki akeyi miki tunda aka kawo akwati, to ai Salamatu munsan ba ke kika yi akwatin da kuɗinki ba, kawo miki akayi banga abun baƙin ciki ba kowacce tana da nata rufin asirin daidaiya. Koni zan iya ma Azgar wannan akwatin ai. "Ungo naki ƴar nema. A gabana ma faɗan zaku ci gaba ke Hinduwa? " Cewar Baba Sojanmu kenan. Sai nayi shiru tare da cewa. Aimun afuwa Baba Sojanmu. Itama Salamatu tayi haƙuri bana nufinsu da komai wallahi" Su ba haka suka so ince ba, shi yasa nace hakan. So su kai mu tada rikicin da zasu tabbatar ma mutane baƙin cikin mukeyi da Auren, shi yasa na bada haƙuri dan in kashe maganar gabaki ɗayanta. "Ni ki dubi tsabar idona da girmana kice wai ina tsoron Ruwayya, sabida Abidah na saki a keken ɓera. Sannan Ruwayya da kike magana a kanta, sa'arkice, ba uwarki bace?" Nan turancin sojoji ya tashi, ya kaima Salamatu mari, yasa ƙafarshi ya take mata yatsu ya kuma murza. Ya saba yi mana haka tun muna yara, lallai ranshi ya ɓaci gaya. Yai ta manya_manyan turanci yana nuna Salamatu da Innah Abida. Sai haƙuri suke bashi, da ƙyar yayi shiru da Innarmu ta tausheshi. "To maganarnan bana so a sake tadata a cikin gidannan. Ke Salamatu duk sanda wani abu ya sake faruwa kika sako Ruwayya a cikin maganarki, balle ni, zaki sha mamakin hukuncin da zanyi miki ni yaro baya girma da duka a hannuna, sai in zaneki ciki da bai, ko in sa sojojin gidannan su baki kashi wallahi. Kuma kiyi gaggawar basu haƙuri sabida uwarsu da kika taɓa. Maganar kuma na kasheta wanda ya kuma tadata ni da shine mutuniyar banza, mutuniyar hofi. Ke Khadijan Mairamu ashe kema baki da mutunci, daku su Nana ko? In na kuma jin bakinku akan abinda babu ruwanku, sai na sa Qazzafi ya ɗaure mun ku a bishiya kun wuni" Tunowa da irin hukuncin gidan soja da Baba Sojanmu yake ma su Akarami nayi, lokacin yana ganiyarshi. Bafa haka Inna Abida taso ba. Ni suke son aima kaca_ kaca sai ya ƙare musu a kansu, Salamatu sai kuka ƙaƙas. Taso tayi magana Baba Sojanmu ya ɗaga mata hannu dolenta tayi shiru. Salamatu kuwa dole ta bamu haƙuri ta kuma ba Innarmu haƙuri. "Babu komai Salamatu. A dai shekarunki yana da kyau ace kina da ladabin magana. Gashi zaki shiga babban famili dole sai kin dinga tauna magana kafin ki fesar dan ke Magana kike yi kamar kashi, baki da tarbiyyar magana sam. Babu mamaki abinda ya rabaki da mijinki ma kenan" Da haka dai taron ya watse duk muka yi ɗakinmu muka ci gaba da tattaunawa musamman akan maganganun Goggo Shirwa da kuwa yaji zafinsu. "Ga ɗinkunan biki nan na karɓo mana sunyi kyau zamu ci waje gaskiya." Cewar Yaya Saratu da take buɗe ledar kayan. Innarmu tace. "Gashi naji ana batun akwai dina ranar da muka isa katsinan. Su kamar biki sosai suka shirya a katsinan fa" Nace da Innarmu. Ni ba wannan ba me akeyi a ɓarayin Baba Dogara naga duk matan gidan suna can? " Innarmu ta taɓe baki tana ɗaga ɗinkinmu tace. "Aure auren daya saba yayi wannan karon a ƙauye yaje ya kwaso matar. Jere dangin amaryar suka zo yi. Wai bazawara mai yara takwas kuma wannan karon ya auro. Kai wannan Baba naku bashi da dama." Mamakine ya lulluɓemu dukkanmu. Bamu muka bar gida ba sai daf magriba na tarkata yaran muka leƙa ɗakin Innah Abida nayi sallama dasu Goggo Shirwa sun amsa basu amsa ba Allah masani ni dai banji amsar tasu ba. A ƙofar gida muka tadda motar Mijinyawa, data mijinyawa Babba. Azgar ya fita ya buɗe mun get muka shiga. Ashe harda Nanno ma da Yaya Jamila akazo, da Musa yaron Shafa. Falon na shiga da sallamata mijinyawa Babbane kaɗai ya amsa sallamata mijinyawa kuwa sai sake sunne kanshi ƙasa yayi na zame mishi kamar suruka. Nanno ya jikin naki?" "Jiki da sauƙi bamu daɗe da shigowa ba munje asibiti shine nace a kawoni nan in kwana ɗaya in fa kin amince kenan dan ke kike juya gidan. Ki mun wannan alfarmar sabida gidanki yafi kusa da Asibitin, inci albarkacin su Azgar, kwana ɗaya zamu yi. Wannan yarinyarce ma ta kawo tunanin hakan, ni da a ɗakin Uwatale zan zauna. Ina jin haya_hayar jikoki" Ɗan murmushi kawai nayi, dan jiki kam tana jin jiki, sai nishi take yi. Dan dai su kwana su wuce, zan barta a wannan karon, sabida ciwo, sannan ita uwa koma yaya take uwace. Duk yadda misali zan takurama matar Azgar misalifa. Bazan so ace naje gidan Azgar matarshi ta koroni ba. Duk da nasan su Nanno basa ƙaubata a mataki na ƙololuwar ƙarshe. Yau in muka rabu da ɗansu ai shikenan. Na gaishe da su Mijinyawa Babba a jam'u shi kaɗan ya amsa Yaya Jamila kuwa bata ko kalli ma inda nake ba bare ta amsa dan ko gaisuwar su Azgar bata amsa ba. To bari in shiga daga ciki in yi sallah. Azgar ka shiga da jakunkunan su Nanno ciki" Na miƙe na fita Azgar ya biyoni da jakar su Nanno ya saka a ɗakin Sabira. Saida nayi wanka nayi sallah a tsanake kana na fito. Saina tadda Yaya Jamila a Kicin tana yinƙurin kunna gas ni kuma shigowata kenan. Zaki ɗaura girki kenan jamila? To bari in shiga daga ciki" Harna juya ta kira sunana a gadarance. "Ke malama in zaki zo ki ɗaura girki kizo ki ɗaura dama ruwan shayi zan dafa ma Nanno. Meya aikeni yin girki a gidan ƙani" Taja dogon tsaki tare da kwaɗama Sabira kira ta tawo a guje. Ita ta kunna mata gas ɗin ta dafa ruwan zafin, kafin ruwan nata ya tafasa na jona ruwa a buta ina jingine da firji ina jiran ruwan ya tafasa. Nima shayin zan sha. "Ciromun kayan shayi in haɗama Nanno Sabira yinwa saita kashe mutum a wannan gidan naku na ma'aikata." Cicciro mata gwangwanin madara dana milo tayi, ni kuma na juye ruwan dana tafasa a kofi. Ina tsaye ina kallon ikon Allah manyan cokula huɗu harda tsoro Yaya Jamila ta juye a shayin, haka taima milo ma ta wuce tana hararata Sai bayan isha na kammala girkin indomi na zuba ma su Sabira, na haɗa komai nawa a tire, na wuce falon, na nemi waje na zauna. Nanno tana zaune tana kallon wani shirin hausa da ake gudanarwa a tashar hausa bakwai, tana shan ti a hankali a hankali. Ni ko ina cin indomina ina danna wayata.. Har zan miƙe in fita su Mijinyawa suka dawo masallaci. ina kallon mijinyawa irin kallon da Yasan dalilin da yasa na mishi, sauke kanshi yayi a hankali. "Hindu kinji Haihuwar Uwatale kuwa, baki zo mana barka ba? " Cewar Nawata harda fara'arshi. A gintse nace dashi. Naji labari" Iyakar abinda nace kenan. Yaya Jamila ta ja dogon tsaki tace. "Azgar kai da ɗan uwanka da Sabira ku bamu waje zamu tattauna" Zamana na gyara jin tace haka, da ina bakin kujera, yaran kuma suka fita jikkunansu a mace har cikin ransu basa jin daɗin abinda dangin mahaifinsu suke yi mun. Tun basu san me ake ciki ba, yau da gobe da girma gami da mallakar hankalin kai yasa sun gane irin zaman takun saƙan dake tsakaninmu. Nanno ce tayi gyaran murya irin na girma kafin tace. "Hindu nayi duk yadda zanyi domin Mijinyawa ya sake Aure tunda ke ba haihuwa kika sake yi ba, ga yarinya har ta kai aure, amman yaƙi fur sabida tsoronki. Ya auri yarinya kun shiga kun fita kin musu farraƙu saida kika tabbatar aikin ki yaci... " "Nanno.... " Mijinyawa ya kirayi sunanta da sigar roƙo" "Kaci gidanku dan abu ta kazanka. Wato so kake in zuba idanu in barka da yara biyu alhalin matsala ba'a jikinka take ba, kana da ƙwayayanka na haihuwa ko? Jibi wanka yaranshi nawa ga Uwatale ta sake haihuwa. Matar Gambo haihuwa ko yau ko gobe, amman kai sai yaushe zan sake ganin jininka saina mutu kake so? " Ni dai kasaƙe nayi ina kallon Nanno ina haɗiye wani abu mai tauri daya tokare mun maƙoshina. Ni da ai tausayi ta bani a matsayinta na uwa, ga ciwo naga bai dace ace na koresu ba, ga dare. Ashe a hakanma tijarar zatai mun. Allah mai iko. Juyowa tayi kaina. "Alfarma nake nema ki umarceshi dan Allah yabi umarnina ya ƙara aure dan Allah na roƙeki wannan alfarmar a karon farko, tunda kece kaɗai ishasshiya a wajenshi tsoronki yake ji, da an yo maganarki zai soma baki kariya. Ni na rasa wannan wanne irin so mijinyawa yake yi miki ke ba yara kika cika mishi da gida ba, bare yace albarkacin yarane. A wannan karon matsawar baki barshi ya ƙara aure ba, kema zaki rasashi dan zai sakeki kinji na faɗa miki ehe. Duk sabida ke ciwona ya tashi. Ki duba halin da nake ciki, ki barshi yayi aure tun ina da raina in ga daɗin yaranshi. Ai ko su Azgar zasu so ganin ƙannensu" Illahirin mamakine ya hanani ko da haɗiyar yawune, sai kawai Nanno nake kallo da irin son zuchiyar da tazo dashi. Yanzu tsakani da Allah ita ta saka kanta a matsayina, surukarta ta mata abinda tayi mun yanzu wanne hali zata shiga, ace ana zaune lafiya fa kawai yara biyune ake ganin sun yi kaɗan. Shin ko auren dole muka yi ace in roƙeshi ni da bakina yayi mun kishiya? Kishiyar da na taso naga irinsu iri da kala a gidanmu, kishiyar da ko yau saida naga sharrinsu, kishiya kishiyar kishiyar. Ai sai dai miji yace zai yi aurenshi da kanshi kai mishi fatan alkhairi. Ina
Chapter 40 · 0% Book details