Sashe 31
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saudatu Mustapha ta ɗanyi murmushi a ƙoƙarinta na kawar da damuwar dake ranta, sai dai masu azanci suka ce labarin zuchiya a tambayi fuska. Tuni fuskarta ta tona asirin damuwar ƙasan zuchiyarta. "Kafinnan bari mu saka odar abinda, ya dace ana tauna ana labari abun zaifi daɗi" Luba ce ta sauke ajjiyar zuchiya tare da cewa. "In labarin masu daɗinne ba Saudatu Mustapha. Ni a halin yanzu, da kuma yadda duniya take jujjuyawa sai inga mata kamar rabinsu da kwata a cikin rayuwa mai ƙunci suke" Sumayya tayi carab tace. "Sati ɗaya dana soma bin shafukan Hindu ya ragemun damuwata gaya, dan ada gani nake nafi ko wacce mace tarin matsaloli da shiga damuwa a gidan Aure. Saida na karanta labarin wannan matar da silar Hindu ta samu wanda ya aureta, ya riƙeta da yaranta, na fahimci matsalar gidan aure ko matsalar ɗa namiji nawa na sani. Hindu na taɓo abubuwa muhimmai sosai, a gaskiya tana ƙoƙari, duk da dai tun can mai ƙoƙari ce, gata da nacin karatu na masifa. Akwai tarin matan da wala Allah in suka ji labarina suce daɗine yayi mun yawa. Kamar yadda sukaita ganin daɗine yaima Lolo matar Babangida Kacigari yawa" Saudatu Mustapha tace. "Ai ni ina ganin a wannan zamanin ko duk macen da ta samu miji nagari ta godema Allah, kuma itace mace mafi sa'a a duniyarnan wallahi" Hmmmm" Shine kaɗai abinda ya fito bakina na rasa kalma kwata_kwata zukatanmu sai ƙonewa suke yi suna mai cike da ƙunci da damuwa mai yawan gaske. Saudatu Mustapha ce da kanta taje tayo mana odar abinda zamu ci, mu sha. Dariya nayi nace. Wannan teburin da alama yayi kama da teburin tattauna matsaloli da gani" Dariyar suma suka saka Sumayya tace. "Wala Allah in muka tattauna mu samu sauƙin nauyin zuchiya. Wallahi a gidanmu babu wanda yasan a cikin rayuwar da nake. Kinsan yanzu a cikin ɗakinku ma sai ki samu mai son ganin bayanki. Shi yasa matsaltsalun gidajen auren suka dawo yanar gizo_gizo ai kune malama haid my id Hindu, ke kinsan komai. Da yawa_yawa matsalar cin rayuwarsu take yi. Sun kuma kasa fuskantar gidansu, ko ƴan uwansu, bare ƙawa da wannan batu. Ku kuma sai kuka sauƙaƙema mata hanya. Kuma ana samun maslaha. Ina Bibiyar Lubna da Aisha Falke sosai. Ina son matar, turancinta da yadda take wuji_wuji da turanci yana burgeni. Gata da fahimtar juna sosai da mijinta, yakan taya ta abubuwa da dama. Hindu ma naga Mijinta yana taya ta abubuwa, akwai bidiyoyi da yawa dana ganku tare ke da mai gidan naki. Dariyar muka kuma sakawa harda tattafawa taf tamkar bamu da wata damuwar komai. Mai kawo abinci ne ya dure mana ƙaton tire ɗauke da shinkafa irinta larabawa mai nama gashasshe manya manya harda bushasshen inabi a cikin abincin. Sai lemo da ruwa, da soyayyen dankalin turawa mai gashasshen kifi tarwaɗa lafta lafta biyu. "To Bismillah mu soma ci ana hirar yaushe gamo. Luba na dai san gidanki a baya, na kuma san kina aikin gidan rediyo yaronki ɗaya na sani Baba Sadiq naje suna ma. Daga nan na bar ƙasar bamu sake ji daga juna ba. Ya rayuwarki ta kasance wajen faɗi tashin cimma gurin abinda kike so ki zama, ga aure ga yaro a lokacin ga miji? " Cewar Saudatu Mustapha fa kenan murmushi nayi mata bakina cike da kifi da dankali nace. Saudatu Mustapha kenan kaga manyan lauyoyi irin wannan tambayar haka? " Luba tace. "Rabu da'ita in dai fagen tambayane da ƴar jarida da lauya ƙwaryar sama ke dukan ta ƙasa nima zan yi mata nawa. Mu da muke rufta mutum yai suɓul da baka ma" Mu kai ɗan dariya, duk hankalinmu akan abinci yake munata yaga muna ƙona yatsunmu. "To gurin zama ƴar jarida ya ginu a zukatanmu ni da Hindu tun muna yara gaskiya inga ni tun ina da shekaru goma sha biyu. A lokacin kullum a gida ana sauraren Bbc Hausa safe da yamma. Babban abinda yafi komai birgeni a lokacin dake da yarinta yadda suke karanto labaran ba tare da ɓata ko gargadaba shi yafi ɗaukata sosai. Ita kuma Hindu abinda yafi burgeta shine wannan muryar da Bbc suke kwaɗa hira da'ita mai taken landan take kira sashen hausa na Bbc. Kinsan Bbc sha ƙundumce, ta tattare ƙunduna, kuma abar koyice, Bbc masu gaskiya da yaɗa labarun gaskiya, ingantattu. Dan ko labaraine a da, da ma yanzu muddin kace ai a shafin Bbc ka gani, ko Bbc ne suka faɗa, musu ya ƙare kawai an gama yadda. To ina ya Allah babu ya Allah. Mun soma sakandare duk da haka muna hira gurin bai canja ba saima, sake ƙaruwa da yake yi. Toh mun yi Aure da Sunusi dama ya riga ya san da zaman gurin nawa, kana yayi alƙawarin barina in cimma gurina, kuma inaso ya barni in yi aiki duk kuma ya amince ko da bashi zai biya mun kuɗin karatun ba. To muna auren kuma sai ciki kunsan ciki da goyo na daga cikin manyan dalilai masu ruguza gurin ƴaƴa matan da sukai sake, da yawa. Ni ban bari hakan yayi tasiri ba duba da Innarmu mahaifiyar Hindu da nake kallo a matsayin allon kwaikwayo, da yadda tayi zarra ma sauran abokan zamanta da Jama'ar gidansu, a cikin malamanma bata da tamka kun san wannan dai, ta iya koyarwa, ta iya duka. Sadiq na da wata takwas lokacin na soma zuwa jami'a. Sabida tsabar son karatun a ƙafa nake zuwa in dawo a ƙafa rana, ɗaɗɗayane nake samun kuɗin abun hawa a wajen Sunusi. Rijistireshon ma da ƙarma_ ƙarma ya biya na farko aka barshi da biyan bashi da mitar tsiya, ya doshi mita, yaita mita yana ciccika yana batsewa. Na soma karatuna da kamar shekara ɗaya na samu wani ciki mai laulayin tsiya wanda dole ya taɓa karatuna na dakatar dashi na shekara guda, akan inna haihu sai inci gaba. Na haihu ina yin arba'in na koma karatu, a wannan lokacin Sanusi a gida yake babu sana'ar ma bare in yi tunanin ya biya mun rijistireshon sai ƴan atampopina na siyar na suna, na gagganɗa na biya naci gaba da karatun a wahale. Me yasa nace a wahale? Babu kuɗin mota, babu abinci ishasshe da zanci in tafi makaranta, ga jego, ga tunanin inna dawo gidan me zan zo in tarar in ci, ga rana na shawo, in kika ga ƙafata a lokacin duk ƙura. Sabida tafiyar ƙafa da nisa tsakanin gidan Aurena, da makaranta har faso saida ƙafata tayi. Ina tafe kawai naji ƙafata kamar an sa reza an tsaga mini kes, sai ga jini. Shikenan ya zama ciwo, a haka dai. A haka akaita bugawa ina ya Allah babu ya Allah, duk na rame na fita hayyacina kafin shekara ta zagayo nayi lalacewar da koni bana sha'awar kaina wallahi, in kalli madubi bana so. Gidanmu kuwa bana son zuwa sabida ƴan uwana sai suita magana akan ramata. Ni kuma nayi gum naƙi faɗa musu sirrin gidana, haka muke ɓoyewa, haƙawa, mu burne tare da Sunusi, soyayya kam muna bugawa, duk da rashin kuɗin, yarona na biyu ma ba'ayi mai haƙiƙa ba. Baba Sadiq ɗinma firjina na siyar a lokacin duba goma sha biyar, na bashi a ciki aka siyo rago dubu takwas, ragowar kuɗin dashi ya fiddani kunyar abincin suna, dake akwai kayan akwati, ni kuma na ɗiba na ɗinka kayan fitar suna. A hakan akaita turawa har Allah yasa ya samu gadi a zangon baƙi, wataran aikin safe, wataran aikin dare na kwana, sai muka ɗan samu sauƙi har Sadiq ya shiga makaranta shima. A haka na gama karatuna na shiga faɗi tashin neman aiki hmm Da ƙyar na samu aiki a wani gidan jediyo, haka bayan wasu shekaru kenan fa. Ko kuma ince na nuna ni ko kyautane zanyi musu aikin sai aka ɗaukeni akan wani shiri sabo, na soma ana ɗan tsakuramun abinda ba za'a rasaba, koma in kirashi da na mota. Kafinnan na ɗan yi koyarwa a wata makarantar sakandare, ana biyana dubu huɗu da ɗari uku. Sai mu haɗe da kuɗin Sunusi muyi hidimarmu ta yau da kullum. Kunji yadda akayi a ɗan taƙaice kenan, har aka iso wannan matsayin da ake a kai yanzu, sai dai mu miƙa godiya ga Allah" Ajjiyar zuchiya Luba ta sauke tare da ɗiban shinkafa da nama ta zuba a bakinta tana taunawa. Sumayya tace. "Toh yanzu da kika cimma gurinki ya rayuwarki da Sunusi taci gaba?" Dariya tayi tana kallon Sumayya data kafeta da idanu. "To bayan komai ya warware shekaru sun sha sosai, Sunusi shima ya samu faraga daidai gwargwado muna rayuwarmu babu matsala harma Allah ya huwace mishi ya sai filinshi babba, ko ince dai muka sai filinmu babba, dan inajin in ban mance ba. Ni na kawo miliyan ɗaya, shi kuma ya saka dubu ɗari huɗu, da dubu biyar akai, muka mallaki fili da sunan zamu gina, mu shiga ni da yarana mu wataya. Tare dani dashi muke zuba kuɗi mu ka yi ginin dai, ko kuma ince da kuɗina ni na soma ginin kafin ma shi Sunusin ya soma zuba nashi kuɗin. Dani dashi muka zauna, mukaita tsara yadda zamu yi gidanmu, har dai muka cimma matsaya. A wannan matsayarne muka kira masu zane suka zana mana hmm. Ragamar gida data yara kusan saba'in talatin muke yi a lokacin (70/30) ban damu ba duk wani nauyin kaina a hankali ya singa sakarmun ƙaƙas. Wataran ya biya kuɗin makarantarsu duka, wataran ya biya rabi, ni in biya rabin, duk ban damu ba. Hindu ma cemun take yi ai babu komai dan mun taimaka ma mazajenmu in akayi duba da cewar sai da yaddarsu da amincewarsu za kayi karatun, kuma duk namijin daya barka kana aiki kana samun kuɗaɗenka baida mugunta. Dan a cikin maza akwai baƙaƙen mugaye masu hassada da samun matansu, masu dankwafar da matansu. Lokaci guda Sunusi ya sauya sabida Aure da ya saka a gabanshi, ya dena mana komai. Ya shiga karantamun shafukan rashin mutumcin daya buɗe bai biya mun ba a baya. Naci gaba da jurewa har na tare a sabon gida amarya tazo itama. A lokacin na gane Allah ɗayane, na kuma yadda ba kowanne namiji ake goyawa ba wallahi. Sunusi ya nuna mun ni ba kowan kowa bace, ni ba komai bace a