← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 85

Sashe 12

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

in suka tafi da kaina zan haɗa kayan in kai mishi har gidan. Shayi da biredi da taliyar yara mijinyawa ya dafa mana a Kicin ɗin na fito cikin shirin aiki na sameshi, shima a shirye yake. Cikin sut baƙa, da rigar ciki mai ruwan omo, sai baƙin takalminshi kwaba shu shayi yake tsaye yana haɗawa" "Barka da fitowa Tutar so, ki shiga falo kayan karinki yana ciki" In na je office zan karya acan" Na faɗa a taƙaice na leƙa falon a tsaye. Azgar kana da lekca da safe kenan?" "Eh Ammi takwas na safe zuwa ukun yamma" To shikenan inka dawo ka tafasamun kaza kai mun tuwon semo ni zan yi miyar inna dawo. Ke kuma ki same ni a mota in kai ki makaranta. Kai kabi Mijinyawa" "Adawo lafiya ammi Allah ya tsare hanya" Ameen Azgar nagode. Na saka kai na fice zuwa mota Sabira bata jima ba ta fito rataye da jakarta a baya. Ita ta buɗe mana get ɗin na fitar da motar. Ta koma ta rufe kafin ta shiga motar muka tafi. Na sauke ta a makaranta ni kuma na wuce wajen aikina Takwas a farfajiyar gidan rediyonmu tayi mun. Dai _dai zan fito saƙo ya shigo wayata ta akwatin turo saƙo. Da kamar ba zan bi ba ina tunanin ko kamfanin layin wayane sukai mun saƙo, sai dai na duba naga baƙuwar lamba ga abinda saƙon ya ƙunsa. _Rana da ruwa da iska sunyi kaɗan wajen raba auren soyayyar da ilahine ya ƙulla. Tattabara uwar alƙawari a wannan safiyar kinyi kyau irin kyan da harshe da haƙori ba zasu sarrafu ba wajen faɗa ba. Ina roƙon Allah ya haɗaki da dukkan Alkhairi ya rabaki da dukkan sharri, kiyi aikin ki lafiya ina miki fatan wuni cikin farin ciki. Ga dubu talatin ayi maneji kuɗin cefanen wata. Mijinki har a Aljannah in sha Allah_ Hmmm mijinyawa kenan kayi wasa da damarka ka fesamun dafin da har in mutu babu makarinshi. Bana buƙatar kalaman soyayya a wannan ƙadamin basu da amfanin komai, raina ƙara ɓaci yake yi inna buɗe idanuna na ganka kusa dani. A zuchiyata nake maganar ina hango sanda Asama'u ta shiga ɗakin Aurenmu kan shimfiɗar sunnah. Take sambatun da mijinyawa yake ma yarinyar da bata da maraba da ƴar cikinshi ya soma yawo a kaina. Da sauri na fito a cikin motar. Luba ce ta dafa ni. "Hindu Duwaf yau an dawo bakin aiki kenan, da kika rame sai kika ɗan ƙara tsayi fa. Duk da wannan shegun takalman naki masu tudu basa bari a tantance asalin tsayin naki" Da wannan abun dariyar Luba ta mantar dani baƙin cikin da nake ciki. Luba kenan da halama daren jiya Sunusi ya saki cikin farin ciki kunje aljannah kun dawo? " Dariya muka saka mun kasa cewa komai sai da muka yi muka gaji, ba amsa muka shiga ma'aikata. Office ɗin shugaba na wuce nafi awa guda muna tattaunawa dashi kafin na fito. Abokan aikina sai suka mayar dani nama, masu nuna hassadarsu kuma a lokacin suka bayyanata ƙarara, dama dai tun daga lokacin da labarin fitata landan ya fasu mahassadan ɓoye suka fito fili, ga kuma rifota dana zama da wasu hakan baiyi musu daɗi ba. Wannan sunnar rayuwace dama duk wata ma'aikata ana samu, wani ma haka kurum yaji baya ƙaunarka, wasu ma a ƙulla musu sharrin sata, ko sharrin wani abun. Yau dai bani na karya ba sai sha biyun rana da muka samu birek naci taliya da kifi da Luba ta dafo mana da shayin na'a na'a. Luba jiya baki san yadda muka ƙarke da su Nanno da Yaya jamila ba" Idanu Luba ta zazzare tace. "Sun zo ganin gida da neman ta da zaune tsaye kenan? " Har muka gama ina bata labarin yadda muka yi dasu, da kuma dawowar mijinyawa gidan. "To ke wanne hukunci zaki ɗauka akan dawowar tashi? " Da nace zan haɗa mishi kayanshi in kai mai can gidan da kaina. Amman a halin yanzu na rabu dashi sabida magana yake nema dani kuma bazai samu ba. Dawowar tashi kusa damu ɗin zai bani sauƙi wajen rabuwa dashi. Luba ina da hanyoyin shiru da halin ko in kula da zan tuƙe mijinyawa dashi da zai sa in ya gaji ya sakeni, ko nan da shekara nawa ne bani da matsala. Amman wallahi_tallahi tunda nace na gama to na gama ba wajen bane Luba. Ai aure ma Nanno take so yayi shi yake ta zulle musu. Ita kuma Asama'u ashe yayi mata saki uku kamar yadda suka ce. Hmm dake maza basu fiye kunya ba shine yake biyo ni yana ce mun tunda ya aureta sai ya gane bai kyauta ba, kuma bai kusanceta ba. Tuni na tsayar da zancan tare da jaddada mishi takaddata zai bani inje in yi auren farin ciki sabida bana jin ɗigon sonshi. Kinga wai yadda jikinshi yake rawa wai shi kishi Luba? Ni wallahi sai yanzu ma abun ke bani dariya. A jiyan baƙin cikine ya kuma turniƙeni" Mun yi dariya sosai wallahi in muna wajen aiki mancewa mutum yake yi da komai. Duk macen da ke aiki, ko sana'a tafa wuce ƙananun iskancin maza na zalunci. Azzaluman maza inji Lubna kai Lubna bata ji. Sai mace taso ya dameta wallahi in taga zai tayar mata da hankali tuni zata jingineshi gefe taci gaba da harkokinta. Ƙarfe huɗu muka baro wajen aiki. Kasuwa Luba ta rakani nayo cefane da kuɗin cefanan da mijinyawa ya turo mun. Daidai abinda ya turo dashi na sai abinda zan buƙata. Na sauke Luba a ƙofar layinsu na dawo gida a mugun gajiye sosai a Kicin na tadda Azgar yana tuƙa tuwo. Tsayuwar da nayi dashi bata shige ta mintuna ba, na wuce ɗaki. Ban zauna ba nayo wanka na gabatar da sallar la'asar kana na faɗa gado gashi gobe sassafe nake son fita ina da asament a ƙauyan wudul da zanje ɗakko rahoto. Bacci na kwanta nayi magashiyan saida kiran waya ya shigo mun na farka a lokacin ƙarfe shida har tayi. Assalamu Alaikum." Na faɗa bayan na ɗaga wayar tare da karawa a kunnena. Sai naji sautin kukan baƙin ciki da ɓacin rai a muryar matar da tayi kiran nawa. Gashi babu suna. Baiwar Allah kiyi haƙuri ba kuka bane magani, buɗe baki kiyi mun bayanin matsalar taki in sha Allah sai mu haɗu mu shawo kan matsalar in Allah ya dafa mana" Shine Allah ya taimakeni tayi shiru cikin shessheƙar kuka tace dani. "Dama Na'ilatu ce ta cikin Zaurennki ta bani lambarki shawara nake nema ki bani. Amman abun yafi ƙarfin waya in kin bani dama in tawo yanzu gidanki dan Allah bazan iya bacci ba in banzo wajenki ba" Ajjiyar zuchiya na sauke. To shikenan ina zawa ciki in babu nisa kina iya zuwa" "Ina da nisa amman zanzo yanzu in sha Allah. Inna zo wanne gida zance?" Ki kirani zansa yaro yazo titi ya jiraki inna kimanci kin kusan isowa. Daga wacce anguwar zaki tawo?" "Daga gandun Albasa zan tawo nama fito yanzu titi zanje" To shikenan nan da minti goma sha biyar zai fito bakin titi zan bashi lambar wayarki sai kin zo" Da haka na sauke wayar a kunnena na fito na tura ɗakin Azgar baya ciki, Sabira kuma tana aikin gida na makaranta jarabawa zasu soma sati mai zuwa. Kinata aiki ba? Sannu ya karatun" "Lafiya ƙalau Ammi tun ɗazu na dawo Yaya yace mun kina bacci kar in sake in tasheki a baccin" Dariya nayi mata kawai na ɗan tsaya a tsaye muka ɗan yi hira kafin na wuce Kicin na tsayar da sanwar kuɓewa ɗanya, ina cikin zuba ɗanɗano mijinyawa ya shigo da sallama, na amsa mishi ciki_ciki ban sake waigowa ba. Baice mun komai ba ya shige ciki da jakarshi ta aiki. Bai wani jima sosai a ciki ba ya fito saye da jallabiya da laptop ya wuce falo lokacin ina falon muna hira da yara. "Tutar so ya aikin ya wunin ya kasance? " Alhamdulillahi" "Masha Allah. Azgar Sabira yaya karatun ke sati me zuwa zaku soma jarabawa ko? Kai kuma jarabawar ƙarshe na tunkaroku ko? " "Eh Abba a saka mu a adda'a" Cewar Azgar. Kai ya gyaɗa yace. "Sai dai a kuma dagewa da adda'ar amman ai kullum a cikin yi muku adda'a ake. Sabira dafo mun shayi marar madara ki kawo mun" "To Baba" Ta tashi da sauri ta fice, Azgar ma ya miƙe. Azgar kaje ɗaki ka ɗakko kin mota ka fita titi zaka ɗakko mun baƙuwa. Ga lambarta ka kwafe a wayarka" Na miƙa mishi wayar ya kwafe ya miƙo mun. Falon ya rage mu biyu, yana danna laptop ɗinshi da halama aikine ya sha mishi kanshi sosai. Ni kuma zaurena na shiga sabida akwai saƙwannin wasu mata biyu da suka turo mun masu neman shawara na tura musu. Kuma inason da daddare na ɗanyi rubutu na jan hankalin maza a shafina na Facebook in sha Allah. "Tutar so kinga kuɗin dana turo miki na cefane ko?" Yi nayi kamar banji ba, saima tashi da nayi na koma Kicin na yi zamana. Magriba ake kira ma, kuɓewa na zuba dana buɗe tukunyata naga ruwan yayi ƙasa naman ya faffashe yadda nake so. Na zuba da minti biyu saina kashe wutar na tafi yin sallah. Ina tsaka da sallah baƙuwata ta shigo Azgar ya wuce masallaci. A falo na sameta a zaune yarkace_yarkace cikin ƙazanta da damuwa da gani bata da ishasshiyar lafiyar kirki. Da sallama na shiga na nemi waje na zauna. Sannu da zuwa baiwar Allah kin iso lafiya? " "Lafiya lau malama" Mrs Bukhari ce To yau kuma kunji yadda aka sha ɗauki babu daɗi da su Nanno. Sai mu kwana anan in sha Allah sai kuma gobe.
Chapter 12 · 0% Book details