Sashe 64
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
suna karyawa, nima Azgar ya bani nawa a kula na kwashesu nayi ficewata aiki abina, bayan na saukesu a makaranta mutuminku bamu haɗu ba sammako yayi yau. Duk da ya kasance ranar sunan kishiyar Lubane amman itama hakan bai hanata zuwa aiki ba, sha biyun rana muka baro wajen aiki zuwa gidan Luba inda gida ya cika, cikowa bata wasa ba mata har ƙofar gida ana zazzaune. Sunusi da abokanshi kuwa suna gefe a wajen an shinfiɗa babban tamfol saniya ce shinkafe a kai suna ta aikin daddatsata. Tsakar gidan kuwa a lokacin an sauke tukwanen abinci guda biyu ɗaya alala ce akayi, ɗaya kuma jallof ɗin shinkafa taji kayan lambu kamar ba abincin suna ba tsabaragen kyau. Ga raguna tiƙa tiƙa a rataye a ƙusa a wajen wanke_wanke anata suyar kayan ciki, ga masu suyar kifi nan kusan katan uku ni dai na gani, gida ya kaure da ƙamshin gidan suna. Dangin Sunusi kuwa har daga ƙauye suka zazzo bikin wannan suna. Ga rumfa an kafa guda biyu harda fararen kujeru kamar dai ƙaramin biki za'ayi ba mamaki. Haka mukaita ratsa mata muna wuce wa idanu a kanmu. Muna shiga muka tadda ƙannen Luba a Kicin suna ta yankan kayan lambu. Tabb Nasiba sinasir kike mana ashe duk kun hallara? " "Wallahi Anty Hindu sinasir nake yi muku da farfesun kan saniya, har na kammala farfesun sannunku da zuwa Anty Luba an zo fa an karɓi kula wai za'a zuba abinci. Baban Sadiq kuma ya turo wai a bashi ƙaramar robar fenti za'a zubo miki nama" Na kalli Luba itama ni take kallo. Kafin ma tasan me zata ce sai ga Sadiq da nama cikin ƙaramar robar fenti, da kifi sukumbiya ɗanye guda shida. "Mama gashi inji Baba wai namu ne" "Hmmm ba Nabila su gyara su soya muku, in zasu iya. In sun gaji su saka a firji. Hindu mu je ciki in samu in yi wanka, kai kuma in ka fita ka rufemun ƙofata." Hannuna ta figa muka yi ciki ta zube a gado tana tunani kawai. Ni nasan sunan yaranta take tunowa ta haihu a talaucin, ta haihu a kuɗin, hidima kwatan wannan Sunusi bai taɓa yi ba. Luba karma ki damu kanki akan komai, ita rayuwa haka take da yawan mata matan da akayi gwagwarmaya tare dasu yawanci bama morar dukiyar, wata ce ke samun mijin a ɓagas aita kashe mata dukiyar ke kina jin zafi, amman zafin zai illatakine in baki da abunyi na aiki, ko sana'a shiyasa Luba mu dage mu nemi kuɗi kawai ni sana'ar motoci inaga zan soma" Dariya wajen Luba harda hawaye, a guje ta shige banɗaki nayi murmushi kawai mata wallahi mu dage mu miƙe tsaye da neman kuɗi kada ki sake kice wai dan namiji na ɗauke dukkannin buƙatunki zaki kwanta ba zaki nema ba. Ke bakya son kuɗin kanki ne? Kuɗin kai daɗi garesu, kiyi abinda kike so a lokacin da kike so babu mai ce miki sai wata ya ƙare ko a.a yanzu babu kuɗi a hannuna. Wajajen bayan azahar muna zaune da ƙannen Luba muna hira muna cin sinasir sai ga kiran Saudat a waya cewar gata ta taso, ta iso baifi da minti goma sha biyar ba sai ga Sumayya Sadiq yayi mata iso har uwarɗakin Luba ita da Mariya Habibu, da Nana Kabiru, tsofaffin ƙawayenmune wanda mukai makaranta tare, mun kuma yi ƙawance sosai, Mariya Habibu zaku santa ƴar wasan kwaikwayoce tayi tashe a zamaninta sosai, duk da ta daina daga baya sanadiyyar Aure da tayi. "Mene Mariya Habibu wai dama kina garinnan Sumayya ina kika samo wannan? Ga kuma Nana Kabiru" Cewar Luba kenan ina dariya nace. Wai Mariya Habibu kina garinnan ko ko dai shigowa kikai garinne. Nana Kabiru idonki kenan?" Duk mun cikasu da tambayoyi, Mariya Habibu kuma sai dariya take yi mana ta rame ta lalace sosai. "Nayi kewarku sosai ƙawayena. Shegiya Hindu kece kika zama Hajiya haka? " Dariya muka yi ta miƙo hannu muka tafa taf ta zauna kusa dani, Nana Kabiru ta miƙo mun hannu muka gaisa zukata fal farin ciki. Sumayya tace. "Wallahi ni na neme ta a waya nace ta shirya muzo. Na samu lambartane sakamakon asibitinmu da tazo wata huɗu da suka wuce, bata da lafiya. Nana Kabiru jiya ta shigo gari. Wannan fitar ma da muka yi mancewa nayi ban sanar mata ba. Amman ai a jihar Delta tayi Aure kun manta ne?" Mariya Habibu tace. "Hmmm da labari mai zafi a bakina wallahi. Hindu da Luba ashe dai kun cika gurikanku na son zama ƴan jarida? Na muku murna daga cikin gurina huɗu ɗaya na samu na cika, na son zama jaruma a masana'antar wasan kwaikwayo, ashe ɗaukaka zuwa take da tarin ƙalube iri da kala. Ashe ɗaukaka marmarine daga nesa. Ashe ɗaukaka wuya gareta. Hmm da zan shigo gidannan rufe fuskata nayi a hakan a kunnena naji wasu suna cewa wannan kamar Mariya Habibu. Ku duba yadda na lalace na zama tsohuwa. Gashi banyi zurfin karatu kamar ku ba ɗaukaka ta ruɗeni banyi wani abu mai amfani ba" Shiru muka yi muna dubanta. Nice ma nayi ƙarfin halin cewa. Abinda za'ayi Mariya kuzo a zauna aci asha, ayi sallah, sai a soma wannan labari dama muna bin Saudat bashin labari nima gani a layi" Ai kuwa haka akayi muka haɗu akaci abincin zumunci ga sinasir ɗin yayi daɗi sosai, abincin suna dai ko da aka kawo bamu ci ba. Bayan mun yi sallar azahar ƙarfe biyu dot muka zauna zaman jin labari, Luba ta kawo mana sassanyan zoɓo da soyayyan naman saniya da aka gama soyawa yanzu. "Wa zai soma labarin? " Cewar Luba. Har kin tuna mun da hadisin ummu zar'in, da naga wannan zaman namu. Inaga Saudat ta soma ko Mariya Habibu ce, ga Nana Kabiru" "Saudat ta soma nawa da tsayi sosai" Cewar Mariya Habibu. Zama Saudat ta gyara da kyau domin somawa. To mu kwana anan sai zuwa gobe in Allah ya amince mana. Ina godiya, ina muku fatan alkhairi. Mrs BukhariTSURON TSIRIN... TSANDAURI...