Sashe 48
Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
iko dana zamema mata garkuwa ko da bazan iya cire dukka a matsalar gidajen aure da azzaluman maza ba, a ƙalla zan taimaka. Azzaluman maza nace, ba dukka maza ba. "Lallai iyayenki yarinya kiyi haƙuri basu san darajarku ba, haƙiƙa haihuwarku kawai suka yi. Kiyi haƙuri na shigar muku magana ba tare da an kasa dani ba. Amman sun saku a makaranta ta mahammadiyya da boko kuwa? " Cewar wannan Hajiya da muka zo muka taddata a sell ɗin. Kai na gyaɗa domin tayi mata tambayar da nima ita zanyi mata daman. Hajara ba Hajiya amsarta. Hajiya baki yi laifi ba ai ke uwace wala Allah zaki iya bamu shawara tunda Allah ya haɗamu. Kuma Allah shi yasan nufinshi na haɗamu. Komai na duniya yana da sababi" Hajara ta dubeta tace. "A_a bamu yi karatun boko ba, mun yi amman makarantar allo shima iyakar na sallah aka samu. Kasancewar mahaifinmu baya iya sauke nauyin ci, da sha, da tufatarwa, ga bashika da rikice_rikice da sukaima Ummanmu katutu a ƙoƙarinta na ganin asirinmu ya rufu, amman ina. Wannan dalilin yasa ta tafi ƙauyensu aka bata wani kaso daga cikin gadon iyayensu, ta kafa jarin sana'a. Wannan ta ɗauki kunun zaƙi, wannan ta ɗauki tallar shinkafa da wake, wannan ta ɗauki tallar dafaffen rogo, ni Awara nake soyawa a bakin kwatar ƙofar gidanmu a nan ɗinma muka haɗu da Figo, ya nuna yana sona a lokacin. Kuma ko danginshi bamu sani ba, yana dai da uwar ɗaki a garinmu, to amman da auren yazo yayyunshi maza biyu sunzo daga mai mujiya, shi ɗan asalin mai mujiyane. A kanon ma uwar ɗaki gsreshi." Allah mai iko da hikima, yanzu Hajara tallah kawai kika sani kuma a haka aka baki Figo ya tawo dake Kano, ba tare da an san danginshi ba, wannan wanne irin rashin gatane iyayenki suka gwadama Figo baki dashi, ai kusan sune silar halin da kike ciki ma. Shi figo dai bai riƙe ki da amana ba sam" Idanuna na kuma lumshewa ni wallahi zaman cikin wajen bai dameni ba kamar abinda iyayen Hajara suka yi ba. Na kuma fahimcesu su a ƙoƙarinsu na son ganin tayi aure asirinta ya rufu ne. Sai dai kash mama da Baba ba ko wanne aurene yake zama rufin asirin mace ba. Kuma juma'ar da zata yi kyau ai tun daga laraba ake ganeta. "Ai kuwa Figo dole ya dinga jibgarki iyayenki sun nuna mishi rashin mahimmancinki, duk shi yasa. Amman yarinya da kanki zaki tashi ki tsaya da ƙafarki ba da ƙafar kowa ba, ke zaki nema ma kanki gata ki maida kanki mai ilimi da sanin ciwon kai, da daraja kai. Ki tsaya kai da fata, kada ki sake bari yai miki irin wannan dukan. In bama zaki iya ramawa ba, ki gudu ko maƙotane, ki samu dattijan anguwa. In abu yaci tura sai ki haƙura. Namiji goma ba fa uba goma bane. Kin ganni anan? Nayi aure ɗai_ ɗai har goma da kike ji da gani, nayi digirin digirgir a harkar sanin maza, da harkar zama da kishiya, da harkar zawarci, da gogewa duka. Idan Allah yasa anan zamu kwana duka ni kuwa zan baku labarina kaɗan daku da masu karatu zaku ƙaru ko da babu yawa. Kuma Mahaifiyata ita ta ja mana komai a sakamakon talauci, mu namu ma bai kai irin na gidansu Hajara yawa ba, gasa da kishiyoyi kusan shi yafi yawa. Kuma duk macen da tayi aure domin abun hannun miji ta shirya ganin komai da komai. Duk namijin da aka aura domin kuɗi ya sani, bazai taɓa girmama iyayenki ba bare kuma ke, ba kuma zaki taɓa burgeshi ba. A zamanin da muke ciki mata ku tabbatar kun yi ilimi arabi da boko, ku tabbatar kuna sana'a ko aiki, ku tabbatar kun san darajar kanku, mutumta kai, ku tabbatar zaku iya rayuwa ba dole sai kun sa damuwar namiji a zuchiyarku ba. Ni dai daga mahaifiyatane laifin, da nawa kusakuran danai ta tabkawa. Ni da kaina na cuci maza, na zaluncesu basu suka zalunceni ba. Kinsan wani sa'in mu mata baki muka fi su. Jarabawa kam ina cikinta na alhakin mazajen dana zalunta. To amman Mazan zamaninnan da yawa zuchiyarsu a mace take murus, shi yasa ma suka rungumi tsarin hamsin_hamsin 50/50 wajen gudanar da rayuwar iyali, to kayi aikin ma, kayi sana'arma, ya kuka ƙare bare ana jibge. Babu laifi dan an taimaka ma miji, amman komai yana da iyakarshi, sannan ki dinga yi kina gina naki kan, da yaranki. Kuma duk abinda zaki yi, ko kike yi. Kada kiyi tunanin samun sakamako a wajen miji, kada kiyi tunanin hakan zai hanashi aure, ko ya hanashi ɓata miki ta ko wacce fuskar. Kiyi domin rabbil izzati, shi zai baki lada ba miji ba, shi dai albarka zai sanya miki. Dake dashi duk Allah kuke bautama, a wajenshi duk kuke neman gafara. Hajara iyayenki suka ja miki kamar yadda iyayena suka ja mun halin da nake cikinnan" Kunji wata sabuwa kuma ko ohh ni Hindu duwaf.