← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 85

Sashe 51

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

HINDU:
ofishin Æ´an doka.
Bayan mun gama ta'ajibinmu na labarin Hajara. Da lokacin sallah yayi na magriba a cikin wannan sell mai cike da zarni da ƙasanta, cikinshi duk mukai sallah ko wacce ta shinfiɗa ɗankwalinta. Na zauna ina lazimi har lokacin isha yayi, na ta da kabbarar sallah na yi wani irin jimawa a sujjada ina ganawa da Ubangiji na ina kai mishi ƙarar tozarcin da Figo ya tasanma yi da kuma ƙazafin da yayi mun, ina so zan nemi hakkina ta fuskar shari'a domin bazan yadda da ɓacin suna ba a matsayina ta mace kana uwa, kuma madubin mata da dama.
Wai da zaran mace ta yinƙura a arewa domin kawo wani sauyi, shikenan bata tsiraba matan ƴan uwanta iyayen hassada da shegiyar ƙeta, sune sahun farko wajen kusheta da yayata farfagandar kwangila ta karɓo a hannun turawa.
Maza kuma su tsoronsu kada a ƙwace musu ƙarfinsu mata su samu wayewa da muƙami su fito a dama dasu.
A matsayina ta mace musulma, na tashi na ƙwana da sanin kome mace zata yi namiji na gabanta, domin Allah subuhanahu wata ala shiya ɗaukesu ya sasu a gabanmu domin su zame mana wani garkuwa, ita mace a halittarta bama a yita domin shan wahala ba,
Musulunci ya gatanta mace gaya.
Namijine aka yoshi da ƙirar gwagwarmaya, da faɗi tashin neman na tuwo, da ganin ya gina ahalinshi sun samu tsayuwa da kyau, sun samu dukkan abinda akeso. Ya haɗa da yaran, da matan aurenshi ya rungume ya musu tarbiyya mai inganci.
Ni kushen maza baya gaba na sam, kushen mata yafi damuna gaya, amman ita mace Æ´ar son kaice, itama fa mace Æ´ar dama nice wance ce.
Shi yasa duk abin a yaba da ƴar uwarta mace zata yi, in ba zata iya wannan abun ba, sai ta shiga kushewa da lalata abun, hassada da ƙyashi sun cika zuchiyarta fal. Akwai wacce a kwamen sakshan ta rubutamun wallahi na tsani matarnan, mugun haushi take bani sai shegen gajarta kamar turmi. Ke me ya kaita kallon aikina, in ba sha'awar dama itace ba?
Ina fatan kun gane wannan karatun.
Bayan na idar da sallah sai na miƙe na basu dama sukai sallah ɗaya bayan ɗaya ɗaki ba girma gareshi ba, tsukukune a takure muke sosai ga sauro sun soma farautar jininmu ɓula_ɓula dasu.
Wata Æ´ar sanda ce ta zo buÉ—e wata mata da suke cikin sell É—in dake kusa da namu. Magana nake son nayi mata akan abinci ko Hajara zata samu taci ta sha maganinta, amman bansan ya tsarin nasu yake ba sai kawai nayi shiru. Allah cikin ikonshi sai ga wata Æ´ar sanda da kular abinci ta sulba mai hannu É—innan ta buÉ—emu tace.
"Hajiya ga abinci inji Alhaji Salmu yace a baki"
Da mamaki tace.
"Alhaji Salmu kika ce fa?"
Bata kulata ba ta dure abincin tare da mayar da ƙofar ƙarfe mai huji huji ta rufe tayi tafiyarta.
"Ke Hajara tunda ba daÉ—i kike ji ba kici abincin sai ayi musu magana su baki maganinki."
Jawo kular nayi gaban Hajara ina ma Hajiya godiya. Na buÉ—e tuwone na shinkafa da miyar kuka taji É—anyen kifi sosai ga man shanu.
Amman Hajiya tuwon yayi mata yawa guda biyu ne manya ko zaki ci É—ayan? "
"To saka mun a murfin kular ma ya isheni' rabi zaki saka mun kuma ku lasa zaman duk na haƙurine."
A murfin na zuba ma Hajara malmala ɗaya na zuba ma Hajiya a abun miyar rabin karin na saka a cikin kular na tsiyayama Maman Junaidu miyar, duk na mimmaƙa musu na miƙe ina buga ƙarfe da sunan neman agaji.
Ƴar doka ce ta ƙaraso.
"Ya dai Hajiya kuna buƙatar wani abunne? "
E dan Allah akwai maganin Hajara a kan kanta lokacin shan maganinta yayi sannan muna buƙatar ruwa"
Jim tayi tace.
"Bata da lafiyane kuma aka kulleta? "
Murmushi nayi kawai, na fahimci masu aikin dare ne su, dan duk bamu gansu ba É—azu.
E bata da lafiya daga asibiti ma aka sallamota amman kin ganta anan"
Na gifta ta leƙo ta ganta babu yadda take abincin ma taƙi ci sanyi take ji sabida a tantagaryar ƙasa muke ga kuma ya haɗa da mara lafiya.
"Zan kawo mata maganin Wacece Hindu a cikinku? "
Nice Hindu'
Ƙofar ta buɗe ta miƙo mun leda nasa hannu na amsa ina tunanin Luba ce ta aiko sai kawai tace.
"Mijinyawane ya kawo yace a baki"
Tana kaiwa haka ta kulle ƙofar ta juya.
Mamaki ya kamani, a hankali na ajjiye ledar abincin ina tsaye harta kawo magungunan na karɓa na ɓaɓɓalla ta wuce da sauran, da fiya wata guda ɗaya tak.
Hajara daure ki cinye tuwon ki sha magani. Ga wani abincinma an kawo bari in buɗe ko zai baki sha'awa. Saifa kin zama jaruma Hajara ki zage a ƙwatar miki ƴancinki in kuma kinsan kin zaɓi rayuwar gidan mijinki duk wuya in zame hannuna tun wuri. Bance ki kashe Auren ba, a dukkan bayananki ai ya nuna kina son Figo. Amman ayi muku iyaka ayi a rubuce ba zai kuma bugunki ba, shi nake nufi."
Na ƙarashe maganar raina a ɓace, tare da buɗe ledar abincin a roba biyar aka zuba, na ba kowa roba ɗaya, ɗayar na ajjiye in da mai son ƙarawa.
Shinkafi ce da miya da nama manyan yanka bibbiyu. Hajara tuwon taci ta sha maganinta ta takure waje guda na rufeta da mayafina, dana roƙa aka miƙo mana mu kai sallah. Maman Junaidu kuwa bata ko iya magana sauro kamar ya jamu ya fitar damu waje sabida yawansu da girmansu.
"Hmmm nace zan baku É—an labarina domin ku tsinci darasin da zaku tsinta marasa anfanin ku watsar tare da su Jamila tsafe da Mamanzee, da su Munira, da Umminmama, da fulani, da Maman Daddy.
Kun ganni kyakkyawa fara tas ga kalangu a gefe da gefen fuskata, wanda mutane da dama suna faɗin basu taɓa ganin wacce kalangu ya zauna ya zame mata ƙarin kyau kamata ba.
Allah ya yoni da farin jini duk da bai kasance daga Allah ba. Mahaifiyarmu ce take karɓo mana rubutu na farin jini a wajen wani tsoho, muna sha tun muna yara, da kwallin idanu, da turaren gogawa a goshi na farinjini. A bisa dalilinta guda ɗaya zuwa biyu.
Dalilin farko burinta mu huta mu auri masu kuɗi, mu miƙe ƙafa mu kula da'ita. Dalilinta na biyu shine tana so kamar yadda mata biyu daga cikin ɗakin Yadikkonmu wato Matar Babanmu suka auri mazaje masu kuɗi hamshaƙai, suka samu duniya suke juyata a tafin hannunsu muma mu samu.
Sun yi aure muna yara kasancewar su aka soma haifa sune manya ita babbar yayar tamu ma Hajiya Kulu a Dubai sukutum suke tare da mijinta da Æ´an yaranta.
Ta kai mahaifiyarta, umara, ta kaita aikin hajj.
To a lokacin suna ma mahaifiyarsu hidima gaya saita fito tsakar gida tai ta nunawa kishiyoyi da fariya, kasancewar mahaifinmu malam Baballe Baduku matan aurenshi huɗu, yama rabu da kusan mata goma akace ma'ana yayi aure aure sosai kafin dai ya haƙura, sakamakon tattalin arzikin nashi da ya ƙare kab ta dalilin aure aurennan da yaita fama dashi.
Wannan kenan.
to ita uwa abinda kullum take faÉ—a kunnen yaro yana saurare inma jariri inma yaro zaku ga ya taso ya tasirantu da wannan abu, ba tare da shi kanshi yasan yadda akayi ba.
Abinda ya faru damu kenan musamman ni da nake ganin nafi sauran Æ´an É—akinmu diri da hasken fata.
Kacokan sai Ummanmu hankalinta yafi karkata a kaina fiye da ragowar ƴan uwana. Mu mu shida ta haifa mata mune manya, sai maza huɗu ƙannenmu.
Amman duk wannan abun fa iyakar karatunmu sakandare ce, mahaifinmu ma a iyakar firamare ake tsayawa da karatun. Iyayenmu mata ke idasa ragowar aikin har mu kammala sakandare.
Mun taso cikin wata iriyar wayewa ta ban mamaki gamu da son maza masu mota mun raina samari daidai da ƙarfin gidanmu, yankinmu. An ɗauramu a gwadaben son maza masu kuɗi. A haya yayarmu ta auri wani mai ɗamara akayi gagarumin biki na alfahari da nuna ma kishiyoyi muma mun isa.
Haka lamuran cikin gidanmu yaci gaba da tafiya mahaifinmu bai san wainar da ake toyawa ba da safe ya fita, sai dare zai dawo a gajiye hutawa kaɗai yake buƙatar yi, da safe muka fi haɗuwa dashi gaskiya sabida baya dawowa da wuri.
Bayan auren Kande da shekara biyu taje hajji taje umara har tana tuƙa ƴar motarta ta zamanin. Sai nima Allah ya ɓullomun da mijina Alhaji Sango ɗan canji ga kuɗi ga kyau mukai aure muka tare a gidanshi dake birget. Rayuwa mai aminci, gida na alfarma katafaren gaske. Sai dai kash jarabawar data faɗomun shine ashe Alhaji Sango matsolone mai kuɗin lugudi naje na taddashi da matan aure biyu dan ba yaro bane. Sutura ma su ke yima kansu, yaya kuke ganin za'a wanye dani da mahaifiyarmu lafiya ni da mu kai auren domin abin hannunshi? "
Shiru tayi tana dubanmu É—aya bayan É—aya ido a cikin ido. Murmusawa tayi kana tace.
"Mama da taji shiru wata É—aya da aure babu wani motsi ina zaune ko a safiyar ranar munyi rikici dashi na ban mamaki akan biredin nera hamsin da yake siyamun, a ranar yake cewa shi ya gaji da sarama kare ciyawa, ni gashi ko garar da ake kawo mace daga gidan iyayenta banzo dashi ba.
Yai mun tatas yana É—aga murya matanshi sarai suna ji.
Ni gashi wata ɗaya nayi bare ince gishirine ya sire akan kaza, amman inna tuno a shimfiɗa yadda yake yabawa sai in ji dama_dama, domin a lokacin da gaske ina sonshi sai dai bana jin tafiyarmu zata iya nisa da wannan mammaƙon nashi. Burina in mallaki manyan kuɗaɗe masu kaurin gaske.
Katsaham sai ga Mama tazo gidana tare da Yayata dake Aure a Abuja, tunda dai tazo biki bata koma ba, na rasa yadda zan tsomasu dan murna amman fa jikina har rawa yake yi sabida bansan ta ina zan soma labarta musu halin Sango ba.
Abinci na girka na kawo musu babu kifi babu nama babu lemo ƙasa kamar ta tsage in faɗa dan kunya. Sabida yadda na ciccika baki, nake da dogon buri kuma.
ÆŠan kwali Mama ta turo gaban kanta tace.
"Kan Uba Bibalo me nake gani nan kin kawo mana shinkafa ce tsurarta daga magi sai mai sai kayan miya, ba kifi ba nama ba ko ƙwai?"
Nan Mama da Yata suka shiga kallon kallo, suna rarraba idanunsu a kaina
Mrs Bukhari
Mu kwana anan, sai in Allah ya kaimu gobe kumaTSURON TSIRIN...
TSANDAURI...
LITTAFIN
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI
Chapter 51 · 0% Book details