← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 85

Sashe 8

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

rasa Hindu mu kwana muna bata haƙuri inna rasata komai zai iya faruwa dani" Ai kuwa abinda ma zai faru da kai yadaɗe bai faru dakai ba ma. Dan Hindu ai shekararku biyu da rabuwa, na faɗa a zuchiyata. Daga cikin dogayen rigunan dana siya ma kaina na saka ɗaya a leda da dabino naba Azgar nace yakai ma Qasimu daga nan ya rufe mun gida in sun fita sai ya zo. Bai jima da fita ba ya dawo yazo ya zauna a ƙasan kafet ni kuma ina zaune a bakin gado. Murmushi nayi mai sauti nace. To ina jinka kada ka ɓoye mun komai Azgar. Ni mahaifiyarka ce inason ka sani cewar babu wacce ta fini kusanci dakai, kuma ni zanfi fahimtar abinda ke damunka" "Hakane Ammi dama akan Kubra ne sai wahala take bani kwana biyunnan. Shekaranjiya da daddare dana kirata ma namiji ne ya ɗauki wayar. Ko da sake kiranta bayan awanni shine sai take ce mun saurayinta ne yazo daga najeriya lokacin dana kirata" Tausayi ya bani ainun. Nasan zafin soyayya da wahalhalunta gaya. To amman Kubra ta dace da Azgar kuwa rayuwarsu ba zata zama daidai da juna ba sam, sannan zata yadda inya aurota ya kawota Najeriya kuma ta zauna tayi biyayyar Auren ma?" Ajjiyar zuchiya na sauke nace dashi. Naji daɗi sosai daka tunkareni da maganarnan ba tare da ka rufe mun ba. Dama akwai tulin tarin tambayoyin da nake son yi maka na bari ne inna dawo sai mu tattauna. Yanzu Azgar tana ƙasar Landan kai kana nan Kano a haka zaku yi Auren ne? Shin kana ganin kun dace da junanku kuma sa'annin auren junane ku? Amman bansan yaya kuka tsara yadda zaku rayu ba" Dariya yayi mun ya ɗago yace. "Ammi ai akwai yarta dake Aure a Gombe. Mahaifinsu baya musu sha'awar auren turawa sam. Sannan ni ban rufeta ba na faɗa mata mu ba masu kuɗi bane, kuma inna gama karatuna soja nake son zan shiga da izinin Allah sabida in cika burinki. To wannan ma ya ƙara mana kusanci yadda ta nuna tana son jarumin maza sosai. Kuma a yanayin yadda take ina kyautata zaton zamu zauna lafiya bata da dogon Guri" Gashi kai ba jarumi bane amman in ka shiga soja zaka koyi jarumta dolenka Azgar. To shikenan Allah yasa mu dace, sannan kayi ta adda'ar neman zaɓin Allah akan aikin sojan in akwai Alkhairi Allah ya tabbatar, in babu ya maye maka gurbinshi da mafi alkhairi. Itama Kubra ka haɗata da Allah ka nemi zaɓinshi in itace shikenan sai kaga kunyi aurenku, tana da hankali gaskiya. Amman ka rage yawan damuwa dan kawai kaji saurayi yaje mata. Ai macece kuma kyakkyawa mai ilimi. Azgar baxai yiwu ace kai kaɗai ne saurayinta ba. Kai dai kayi naka bakin ƙoƙarin ka sace zuchiyar tata, shikenan fa a cikin dubu sai kaga ta zaɓeka. Kaima yana da kyau in biya maka kaje ka dubota iyayenta su sanka kuyi magana ido da ido. In sha Allah zanyi ma adashen kuɗin jirgi in Allah ya yadda shekara mai zuwa sai kaje ku gana lokacin ka kammala digree ɗinka, itama ta kammala nata. Dariya yayi mun sosai da sosai nasan na farin ciki ne zallah. To wa nake dashi bayan su. To shikenan damuwa ta ƙare ko akwai wani abun?" "Akwai Ammi. Zainab nake so ayi ma magana dan Allah ta dena damuna da kira ko saƙon karta kwana. Bana so in rufe layinta ne sabida zumunci" Wallahi mancewa nayi wacece Zainab ma wai ashe Zainab ta wajen Uwatale yake nufi. Ni dariya ma abun ya bani wallahi. Toh ikon Allah Zainab kuma Azgar. Yayarka fa Zainab ta wajen Uwatale? Kada ka damu zan ji da wannan amman ka sani ko bayan raina ban yadda ka auri Zainab ba, bama ita kaɗai ba duk wata mace data fito tsatson mahaifinka ban yadda ba" "Me yasa kika ce haka Ammi ko dan kina tunanin basa sonmu ne kika ce hakan? " Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Azgar kai yarone ba zaka gane ba. Amfani suke so suyi daku kawai ba wai soyayya domin Allah ko dan haɓaka zumunci bane. Wallahi ko zan yadda da auren dangi banda yaran cikin ɗakin Uwatale. Azgar ko Zainab ɗin kake so in bar ɓata lokacina akan Kubra ne? Ka san dai ta girmeka ko " Dariya yayi yace. "Allah shi taimaki Giwar Abba ranki shi daɗe Tutar so da girman kujerarki duk abinda kike so shi nake so billah" Dariya muka yi tare ina son Azgar sosai wallahi. To shikenan jeka ko akwai wani abunne? " "To Ammi kada kiga kamar na dameki akan Abbane dama. Kinsan Asama'unma bata nan tun washegarin da sukai wani faɗa da Sabira akan ki akace washegari Abba ya ɗauketa suka fita wai tana gidansu" Labari ya kwashe ya faɗa mun duk yadda akayi, ya ɗaura da cewa. "To Ammi Abba tunda kika tafi yake cikin damuwa, ramarki da tashi suna da alaƙa sabida tun tasowarmu bamu taɓa riskarku a cikin halin faɗa ba" Azgar kenan yanzu dai kazo ne mijinyawa ya turoka, yayi amfani dakai wajen shawo kaina ko? " "A'a Ammi wallahi baisan zan miki zancan ba. Ammi jiya ya daɗe a falo yanata zurga_zurga ya goya hannunshi. Tsoro nake yi kar wani abun ya sameshi" Ba shakka Azgar, ni kuma baka tsoron wani abun ya sameni ko, sabida kaima namijine kamar mijinyawa ko? To yayi tashi kaje ka kwanta kaina ciwo yake yi, ina fatan ka rufe mun gidana? " "Ammi ki mun aikin gafara. A cikin ku bana kare kowa bana ganin baƙin kowa dukkan ku nawa ne" Dariya yasa nayi dole yadda ya marairaice shi tsiyata dashi rauni, nakasune a wajen namiji rauni. Namiji a dake aka san zuchiyarshi sai wajen daya kamata yayi rauninne ya dace ace yayi. Banyi fishi ba ɗan albarka. Amman bana son ka sake saka bakinka a wannan ƙadiyar, ka rufe mun ƙofar? " "Abba ya rufe yananan bai tafi ba, yama kwaso kayan sawarshi mun jera a sib ɗin ɗakina" Kai kawai na girgiza Azgar ya tafi ya barni a tsaye ina gaban mamakin mijinyawa mai kwaso kaya. Ya kwaso kaya fa Azgar yace wai har sun jera a sib ɗin ɗakin Azgar. Na fahimci so yake mu raba abun faɗe tsakanin ni dashi kenan a gaban yara. To shikenan wallahil azeem gobe zai sha mamaki, irin wanda ya shayar dani, zai ga tambotsai na haƙiƙa kuwa. Hiye ba shakka wannan ƙarfin hali da yawa yake. Hmmm maza kenan in sukai wani abun kamar kaita dukansu. Kamar wasa bacci ya ƙaurace a idanuna abubuwa da yawa naita tubkewa da warwarewa. Ina hango rayuwarmu ta baya ni da mijinyawa, da yaranmu, a lokacin suna ƙananan yara da Azgar da Asama'un da ya mayar da'ita matarshi. To naji Qasimu yace Asama'u bata nan. Ga labarin da Azgar ya bani kuma? Gidan haya ya kama mata ya sakata a ciki kenan koko yayane? Inma gidan hayar ne tunda ita itace sai ya kama mata ai babu mamaki a ciki. Amman ni nayi juyin duniya mu sake gida, mu kama haya ko dan kaucema gori, da ƙananan iskancin Uwatale. Amman sai yace Nanno ta hana, umarninta ne dole sai dai mu zauna a gida ɗaya. Hmmmm Allah dai ya kyauta in ana cin ɓaure ba'a tona cikibshi. Ga maganar Zainab ya tsayamun a raina sosai Wannan fa duk sharrin mutuniyarku Uwatalene. Yarinya ta gama kwantai sa'anninta suna gidajen mazajensu, shine ake so a jona ta wajen Azgar ƙaninta abun kunya. Da maganganun Qasimu suma sai nuƙurƙusata suke yi da yasan irin baƙin cikin ban haƙurin da yazo yayi mun da nayi, da baima soma ba, a tunaninshi shi ya shiga yayi sulhu ne, baisan sake damalmala al'amarin yayi ba. Harda cewa in koma ɗakina sabida Nanno gobe tana hanya. To sai me dan tana hanya, ni da gidana akwai wani ikon da za'ayi munne. Ashe gobe za'a kwashi ƴan kallo kuwa tab. Karatun Qur'ani na saka a wayata idanuna a rufe inata ambaton Allah bansan bacci ya kwasheni ba sai jin kiraye_kirayen sallah kawai nayi. Na faɗa banɗaki saida nayi wanka na iya ɗauro alwala idanuna har yaji suke yi tsabaragen baccin da nake ji. A daddafe naje na tabbatar yaran sun tashi, na haɗu da Azgar tare da mijinyawa a daidai Kicin suna shirin fita. Jin motsin ƙofata yasa suka juyo. Sosai mijinyawa ke kallona. Zai ga abinda zan yi mishi, yadda ya kwaso kaya haka zai ɗebe kayanshi, yaga ina mishi sanya ne hmm. Ƙila saina shaƙeshi idanunshi sun firfito zai gane ba wasa nake yi ba. Tabb maza wallahi akwai soyewar idanu. "Kin tashi Tutar so? Mu mun tafi masallaci Sabira ma na tasheta" Adawo lafiya na faɗa a ƙasan maƙoshina ya sakar mun lafiyayyen murmushi mai muni yace. "Allah yasa mun gode da adda'a" Suka fita nabi bayanshi da harara. Ɗakin Sabira na leƙa dan tabbatar da ta tashin kuwa, tana kan sallaya tada kabbararta kenan. Ƙofar na mayar mata na rufe na koma ciki na yi sallah ido a rurrufe na koma gado ko minti biyu banyi da hawa ba bacci ya kwasheni. Mrs Bukhari. To mu jira mu ga abinda gobe in Allah ya kaimu zata zo dashi kuma....TSURON TSIRIN... TSANDAURI..
Chapter 8 · 0% Book details