← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 85

Sashe 57

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Dawowa
Murmushi yayi ya girgiza kai kawai ya sauke ajjiyar zuchiya mai cike da kewar rayuwarsu ta baya. Miƙewa yayi cike da rashin ƙarfin jiki ya fita, ya koma can wajen zaman nasu suna leƙawa duka su dubo marasa lafiyan amman basu farkaba har magriba, a hanyar dawowan mijinyawa daga masallacine ya hango su Kawu su biyar shi yai musu jagora har zuwa ɗakin da su Nanno suke kwance, Yaya Zakiya da Innah sai hararar mijinyawa suke yi."
Inna Akulu data kasa haƙuri sai cewa tayi.
"Ina fata marar mutumcin i yanzu tana gidan iyayenta an bata dai takaddarta ko? "
Uwatale mai neman ayi sai firit tace.
"Inaa ai yace babu wanda ya isa ya.... "
Kallon da mijinyawa Babba ya watsama Uwatale shi ya tilastata jan bakinta ta tsuke kawai.
Kawu yace.
"Wanne irin saki dan dai ku yaran zamani sakin aure babu wahala a wajenku ko. Shin yarinyarnan ba makaranta bane suka tashi ba, koko da gangan tayi hakanne Mijinyawa? "
Mijinyawa yace.
"Ko kusa Kawu ai ita kanta har zuwa yanzu bata farfaɗo ba, bata cikin hayyacinta har yanzu. Hindu tana girmama Nanno wallahi ko ba aure muke yi ba ba zata taɓa aikata wannan ɗanyen aikin ba, ta samu nagartacciyar tarbiyya, Kuma Yaya Jamila itace ta jawo komai, itace mai kunna wutar fitina. Amman Uwatale itace idanunsu.
Kawu ya dubi Yaya jamila dake kwance wuya a aune ya girgiza kanshi baice komai ba, su Yaya Zakiya da Inna Akulu sukaita rantsuwar sai an saki Hindu Kawu baice musu Uffan ba. Mijinyawa tun yana rarrashi har ya soma faÉ—a tamkar dambe zai kaure a tsakaninshi da Mijinyawa Babba, Kawune yace Mijinyawa ya wuce ya tafi gida duk abinda ake ciki gobe sai a tattauna ya tsawatarma kowa dai, Qasimu ya ja su Kawu zuwa gida, Uwatale da matar Gambo aka bari a asibitin kowa ya kama gabanshi.
Murna da jin daɗin da Uwatale take ciki yaƙi ɓoyuwa sam ko me Hindu ta tare mata oho, ko in an saketa me zai ƙareta dashi ita kaɗai ta barma kanta wannan sanin.

HINDU:
A hankali nake ƙoƙarin buɗe idanuna amman tsabaragen yadda ya kumbura yayi nauyi na kasa buɗeshi sam. Bakina ma da ƙyar na motsa na ambaci Allah, wallahi ko hannuna bazan iya ɗagawa ba. Abubuwan da suka faru a ofishin ƴan sanda na shiga tunowa, ni dai nasan ina zaune a motane amman yanzu kuma a kwance nake jina.
Yanayin nauyin jikina ya riga ya bani amsar abinda ya faru tunda in da ana sabawa dana saba.
"Alhamdulillahi zubaina Luba ta samu kanta fa. Hindu kin kasa buÉ—e idanun naki ne ko?. Bari a É—an gargasa miki fuskar da ruwan É—umi kumburin dama yayi yawa. Luba É—ebo ruwan É—umi da tawul."
Yaya Saratu ke magana hannunta a cikin nawa, daurewa nayi na buɗe idanun da jarumta sosai in tashi dai na kasa har Luba ta ƙaraso bance komai ba. Ita da kanta tai da mun ruwan ɗumi harma da jikina shine ma harna iya tashi na jingina a kan gado, da taimakon Luba da Yaya Zubaina. Yaya Saratu dama uwar tsoroce duk sanda ta ganni a cikin wannan yanayin to ɗari ɗari take yi dani bata iya matsowa inda nake.
Meke faruwa Luba. Hajara ta koma gidan Figo É—in ko? "
Na furta ina kallon luba.
"Hindu ajjiye wannan zancan na kunna ruwan zafi a banɗaki Muje in taimaka miki ki gargasa jikinki a kawo miki abinci kici, yanzu fa ƙarfe takwas ne na dare"
Cewar Luba dake ƙoƙarin ganin ta kamoni ta taimaka mun. Ita da Yaya Zubaina suka kaini banɗaki na zauna zaman daɓaro a banɗakin suka ja mun ƙofar suka fita. Naga hannun Luba a ɗaure da tsumma.
Tuƙuƙin baƙin cikin mahaifiyar Hajara yana kamani, Allah kaɗai yasan adadin yawan iyayen da suka tursasa ɗiyoyinsu zaman aure mai cike da zalunci, sabida kawai dalilin ƙin zawarci da kunyar idanu, ko abinda za'ace. A hankali nake watsa ruwan yana shiga cikin jikina da kyau ina tuno irin yadda Figo ke shigowa da mata har kan gadonshi kuma yasa Hajara tayi musu girki. Wallahi wasu mazan haɗuwarsu da Allah ba kyau babu daɗi, sabida irin zaluntar matayensu da suke yi.
Hmmmm Allah yasa mu dace ina fata wannan ya zamemun matattakalar nasara akan tafiyata ta tallafama ƴan uwana mata, wanda a zahirance maza ke yaƙi da mata ire_irenmu.
Na jima sosai a banÉ—akin ina gargasa jikina kana na É—auro alwala ga wata iriyar yinwa da nake ji kamar me, har wani juwa nake gani.
Na fito É—aure da tawul a jikina, Yaya Saratu na zaune suna waya da Baba Sojanmu. Yaya Zubaina da Luba tuwo suke ci sun yi mun É—are É—are a gado.
"Hindu tawo muci tuwo kafin kiyi sallah ga shayi mai zafi ki soma warware hanjinki" Doguwar riga mai sauƙi na zura a jikina.
Ke Luba ba zaki zo ki tafi gida ba koko sai Sanusi ya kiraki ya soma faÉ—a tukunna? "
Na faɗa cikin sigar zolaya ai ko ilai sai ga kiran Sunusi ina zama. Shayina na ɗauka na soma kurɓa.
"Sai kirana yake yi kuma na faÉ—a mishi zan kwana a nan, sabida yanayin jikin naki, harfa na tura Zulaiha ta kwana da yaran gudunma magana ko me yake son yace mun kuma oho"
Tsakanin mata da miji sai Allah. Yaya Saratu yaushe kuka zo? "
Gama wayarta da Baba Sojanmu Kenan.
"Hmmmn Hindu kedai bari yau ni naga abinda yafi zare tsayi. Ke dai ci abinci ki rama sallolinki sai ayi magana."
Bance komai ba nasan bazai wuce akan batun Hajara da kuma tashin da mutanena suka yi ba.
Soma cin ciwon nayi ina tambayar Yaya Zubaina banji motsin yaran ba"
"Hmmmm Surukarki tana asibiti, Azgar da Ƴar uwarshi sun tafi asibitin kai abinci. Ke dai ci abinci za'ayi miki bayanin komai Hindu.
Naci abinci sosai dan saida na ƙara cin malmala guda bayan wanda naci, na shanye shayina, jikina babu kuzari a zaune na rama sallolina ina kan daddumar ina ambaton Allah Yaya Saratu ta labartamun halin da ake ciki da abinda makarai suka sa na aikata. Ga hannun Luba data samu tsagewar ƙashi ma.
Allah shine shaidata ni banji wani ɗar a zuchiyata dangane da abinda ya faru ba, in aka duba sababin faruwar da kuma ai bani bace suma sun sani, mutum bashi da ikon hana aljanin da ya hau jikinshi aikata abinda yaga dama. Asalima makarai na yaƙar maƙiyan mutum ne, akasari in banda ɗaiɗaiku da suke aiwatar da son nasu zuchiyoyin, zagina suka yi, su kuma suka bani kariya a tunaninsu to menene na girmama abu in ba dai rashin son a zauna lafiya ba.
Haƙiƙa bance abinda ya afku daidai bane, kuma bani da iko akai adalci kaɗai nake son aimun.
Hmmm Yaya Saratu shine duk kuka damu akan abinda ni Hindu bani da iko akai, kuma ban isa in saka ko in hana ba, asalima a lokacin da abun ke faruwa bani a cikin ainihin duniyar mutane?
Ni a hangena wannan ba wani abun damuwa bane, da har zai zama babba ba, lalurace tana iya faruwa kuma da kowa, amman in suka ce zasu ɗauki mataki babu mai iko akai daga ni har ku. In dai dan wannan ne ku koma kan iyalanku babu komai abinda duk ya faru muƙaddarine na dogara da Allah shine majiɓanci al'amurana alƙalin alƙalai. Amman ni ko gezau banji ba gaskiya. Kuma na kasa tuno komai"
Shiru nayi ina ji a raina Allah yasa sanadiyyar wannan abun auren nawa ya mutu, ko zan shaƙi iska mai ni'ima. Su suna tsoron kar auren ya gutsirene ni kuma a wajena gutsirewar nake so.
Amman magana ta domin Allah na tausaya ma Nanno domin Uwace, kuma dama ba lafiya gareta ba nima bazan taɓa so hakan ya faru dani da matar Azgar ba, ko ya faru da Innarmu da Matar Akarami ba, wannan shine gaskiya amman akwai abinda baka da iko sai ido kawai.
"Hindu ai matsalar shine su Dangin mijinki da yaran É—akinsu Mijinyawa Yaya zasu É—auki lamarin, shine abun hangen. Ba lalle su yi hange irin nawa da naki ba"
Katseta nayi da faÉ—in.
Musamman in suka saka son zuchiya da ƙin karɓar gaskiya a lamarin ba. To Yaya Saratu yaya zaku yi in damuwar kuka yi? "
Luba tace.
"Daɗina dake Hindu duk girman abu a idanunki maidashi kike yi ƙarami, amman wannan lamarin fa babbane wallahi tsohuwar ta bugu sosai, ni bana ta Jamila ma dan ita a cikin hayyacima za'a iya dakuwa babu kuma abinda zai faru, girma da darajar uwane kaɗai yake tsoratamu duk da akwai fahimta tsakaninki da gogan naki"
Yaya Zubaina tace.
"Da fa gaskiyar Hindu wani abun ƙarfinka yake fi, dole ka mayar dashi ba komai ba sabida babu yadda zaka iya goge wannan abun, ya zamto babu shi.
Hindu da gaskiyarta"
Dama Yaya Zubaina tafi sauran Æ´an É—akin namu fahimtar halina, da ra'ayoyina da yadda nake tafiyar da rayuwata. An daÉ—e ana tattaunawa kafin Yaya Zubaina da Yaya Saratu suka yi mun sallama mun tsayar da matsayar gobe da safe Baba Sojanmu yace zai biyo ta nan gidana, shi da Akarami su É—aukeni zuwa asibitin mu dubo su Nannon. Ni da ta tawa za'abi wallahi da ba sai sunje ba, dan nima ko babu inda zani.
Luba na kwance a gefena tana aiki a laptop ɗinta da hannu ɗata, nima kawai sai na hau Facebook nayi rubutu mai taɓa zuchiya na dangane da halin da Hajara take ciki da irin tauyeta da mahaifiyarta tayi, ban faɗi sunanta ba, kawai labarin na bayar tare da ɗaurawa da tsokacina a bisa nazari da nayi akan iyayenmu na Arewa musamman mata_matan. Rufe laptop ɗin nayi ina shirin kwanciya na jiyo su Azgar suna kwankwasa ƙofa, Luba ce ta buɗe musu suka shigo.
Bakin Azgar nake ta kallo daya kumbura ga ciwo.
Azgar me ya sameka haka a baki haÉ—arin mota kuka yi ne, naga bakin ka da ciwo kuma har an wanke ma an saka maka jibi? "
Murmushi yayi yace.
"Ammi ya jikin naki? "
Da sauƙi faɗamun abinda ya sameka"
Luba ya kalla kamar yana mata ishara da ta sanar danine.
"Ai kuwa jama'ar taki yau basu bar yaron nasu ba idanunsu ya rufe, ta goÉ—iyarsu kawai suke, duk sun nakasamu"
Shiru nayi kawai tare da girgiza kaina, to me zance sai fatan Allah ya basu lafiya kawai. Basu wani zauna ba sukai mana sallama suka je suka kwanta.
"Umm bari nima in haɗiyi maganin ciwon gaɓoɓi hannuna duk sun yi mun nauyi ɓallo mun biyu"
Mai ya samu hannun naki, tsagewar ƙashinne? "
Madadin ta bani amsa sai muka tuntsure da dariya kamar bamu da matsalar komai.
Luba ke ai muguwace bani labarin irin dakuwar da Yaya Jamila tayi"
Dariyar muka kuma kwashewa da'ita tana hawayen mugunta, tana bani labarin yadda ta kaya.
Hmmm Allah ya kyauta ya yaye ma duk masu É—auke da lalurar makarai"
"Ai baki sani ba Hindu wallahi ni sai yaune naji dama ana aron makarai, dana ara a wajenki kinga Sunusi Allah irin dukan da zaici ko Æ´an gidansu ba zasu ganeshi ba"
Da dariyar mugunta ta ƙarashe zancan nata, nima dariyar nake yi sabida ta mugun bani dariya bata san wahalar da gangar jiki ke samu bane, a yayi da iska ya hau kanshi ba shi yasa, gani kawai take ji amman bata taɓa ɗanɗana zafin ba. Adda'a nake ma masu irin lalurata Allah ya basu lafiya.
Mun jima muna tattauna matsalolin Hajara kafin mu ka yi bacci, cikin baccin tabbas na ji dawowar mijinyawa dan har ɗakina saida ya murɗa yaji a rufe bai dai ƙwanƙwasa ba. Da tausayin Nanno na kwana wallahi a raina duk tsiya uwace, kuma ita ta haifi uban ƴaƴana ko da bama tare da ɗanta, wallahi bazan so abinda zai taɓa lafiyarta ba musamman kuma ace nice sila.
Haka dai bacci mara daÉ—i mai cike da mafarki kan mafarki garin ya waye mana, kuma ya kasance ranar asabar ne babu makaranta yara, muma bamu da aiki.
Da misalin ƙarfe bakwai na safe fitowata wanka kenan na ke jiyo hayaniya da zage_zage ana dukan get ɗin gidanmu.
"Hindu lafiya wannan doke_doken ƙofar kuma daga ina? "
Wallahi kafin ince wani abun muka jiyo hayaniya a tsakar gida Luba dai da gudu ta fice ni kuma na tsaya na zura dogon wando da riga doguwa na fito. Muka ci karo da Mijinyawa daya zuro jallabiyya jikinshi duk kumfa da halama wanka yake yi ma.
Motar su Baba Sojanmu na tsakar gidan Baba Sojanmu da Akarami, sai Innarmu da Yaya Saratu.
Masu wannan ihun kuma su Yaya Zakiya ne da matan su Gambo harda Uwatale wai dukana suka zo su yi a bisa abinda ya faru.
Uwatale da goyonta fa a bayanta, sunci É—amara.
Baba Sojanmu in ya kalleni, sai ya kallesu, ya harɗe hannayenshi a ƙirjinshi kawai, ga hula mai malafa a kanshi ta sojoji, yayi zanzaro da bel ɗin sojiji.
Chapter 57 · 0% Book details