← Book details Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 85

Sashe 83

Tsuron Tsirin Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mijinyawa:.
Bayan sun yi doguwar magana sosai da Qasimu bai shigo gidan ba sai bayan Magrib yana haÉ—e hanya kanshi ji yake yi tamkar zai tarwatse dan ciwo, babu É—anÉ—ano a harshenshi ko É—is, yana zama ya shiga kiransu Azgar lokacin sallah bai basu damar zaman ba har saida sukai sallah suka dawo, ya tarasu a É—akin Azgar.
Yana bakin gado su suna zaune a gabanshi.
Shirune yaita wanzuwa a ɗakin wanda a ƙalla saida aka shafe minti goma baice uffan ba. Sautin numfashinsu kaɗai suke ji. Can yace.
"Gobe zamu koma Katsina kamar yadda kuka sani. Abinda baku sanin ba shine ba da Hindu zamu tafi ba. Ita zata ci gaba da zama anan.
Kuyi haƙuri nasan dole zaku tuhume mu, ni dai ta ɓangarena zan muku dukkan bayani in muka isa, ku yi biyayya, nasan kun samu tarbiyyar da bani da haufi.
Kuyi haƙuri ƙaddarace kawai zan iya ce muku.
Wallahil Azeem ina son mahaifiyarku har gaba da abada bazan iya dena sonta ba. Tana da matsayi mai girma a rayuwata. Amman a yanzu kune zaku maye mun gurbinta.
Sabira kije ki kwanta, kai kuma ka kawo mun ruwa in sha magunguna bana jin daÉ—i sam"
A sanyaye Sabira ta fice, Azgar ya fita ya kawo mai ruwan ya ɓaɓɓalli magunguna ya watsa yabi da ruwa.
A wannan daren a cikin wannan ahali babu wanda ya runtsa. Amman babban abinda ya zama abun burgewa da ƙawa a kan sallaya suka kusan kwana.
Kowanne cikinsu ganawa yake yi da Ubangiji babu hijabi, sai dai akwai babbanci adda'a.
Asussubar fari Mijinyawa ya tattaɓa Azgar dake bacci a zaune da carbi.
Sai yaji jikin yaron kau, shima yaron yaji jikin Baban nashi kau. Babu wanda yace da É—an uwanshi komai.
"Kaje ka yi wanka kayi alwala"
Sai da Azgar ya shiga banɗaki mijinyawa ya jawo takadda da biro, yayi shiru ya rasa ya zaiyi hannunshi na ɓari ƙirjinshi na dokawa yayi rubutu ya nannaɗe.
Azgar na fitowa Mijinyawa ya faÉ—a banÉ—aki, alwala kawai yayo ina ya kasa wanka jiri É—ibanshi ma kawai yake yi.
"Muje masallaci Azgar. Da mun dawo zamu wuce Qasimu zai zo shi zai tuƙa mu."
Suna fitowa ya nufi ƙofar ɗakin Hindu ya soma ƙwanƙwasawa a hankali.
Ganin haka yasa Azgar ya fita zuwa tsakar gida yana jiran uban nashi.

Hindu:.
Ina sallame sallar ra'aka tanil fajir naji ana lillisa mun ƙofa a hankali.
Nima a hankalin na tashi na je na buÉ—e, ina da tabbacin mijinyawane ne babu makawa.
Ilai ina buɗewa muka haɗa idanu baki na ɗan taɓe kaɗan haka.
Hannu ya saka a ajjihu ya ciro takadda ya miƙa mun.
Allah na ambata na sanya hannu na karɓi takaddar, ya juya ya wuce da sauri.
Illahirin jikina sai yayi sanyi kamar an watsamun ƙanƙara. Take sai sanyi naji yana huda har ɓargona. Wallahi hannuna har jiƙewa yayi da ruwa sharkab.
Juyawa nayi na koma ciki, na buÉ—e durowar gefen gadona na adana takaddar sakin, ina wani murmushin da ni ni kaÉ—ai nasan fassararshi.
Sallah na kabbara, na yi adda'a nayi adda'a nayi ma Allah kirari, nayi godiya, na nemi nasara a rayuwar gaba.
Ina zaune ina sauke ajjiyar zuchiya a hankali a hankali sai na jiyo magana a tsakar gida kamar dai Qasimu, da gagamniyar yara suna fitar da kaya suna sanyawa a mota.
Sai can naji an buga mun ƙofata.
Wani abune ya tsirgamun daga kayina zuwa babban yatsan kafata ta hagu.
Ina buɗewa naga yaran a bakin ƙofa kawai jikinsu kamar an watsa musu ruwa.
"Zamu tafi Ammi"
Rungumesu nayi du su biyun a jikina, wallahi ina jiyo yadda jikin Azgar yake ɓari, Sabira ita kuma kuka take yi abunta kashirɓan.
Kiran da mijinyawa yayi musu ne ya tilastamun sakinsu tare da jan hannayensu har filin tsakar gidan. Qasimu yana ta jijjera kayan nasu a mota cikin dabara, dan motar tayi ma kayan kaÉ—an.
"Hajiya Hindu ta Gawata ikon Allah. Tsuron tsirin tsandauri Allah ke fidda shi."
Murmushi nayi haƙorana yana wani irin rawa. Da ƙyar nace.
Qasimu ashe baku tafi ba?"
"Dama yau zamu tafi. To sai ga kiran Gawatanki akan ni zan kaisu Katsina shi jikin nashi babu daɗi, yana ganin Azgar kamar bazai iya tuƙin ba"
Azgar ɗin? Kallon yaro yake yi mishi. Ai kuwa shi ya tuƙamu lokacin bikin Salamatu har katsinan, kuma shi ya tuƙo ya dawo da mota"
Mijinyawa dai baice damu ci kan ku ba asalima kanshi a juye yake, ko me yake kallo oho.
Yaran naja na shigar dasu cikin mota, na ɗan ƙara musu nasiha.
Shigar mijinyawa da Qasimu gaban motar yasa na musu sallama na matsa, ga get an wangale.
Ina gani suka ta da motar, gabana na dukan uku_uku ƙafafunane naji suna neman gagarar ɗaukana, ba shiri na yi saurin ƙoƙarin barin wajen.
Ina zuwa daf ƙofata sai naji Azgar ya kwaɗamun kira da ƙarfi, muryarshi na wani irin rawa.
Juyowa nayi da saurina.
Mrs Bukhari.TSURON TSIRIN...
TSANDAURI...

LITTAFIN

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI
LAMBA TA ASHIRIN DA UKU ( 23)

YAR UWA MENE MATSALARKI

KINSAI MAGUNGUNAN NONO DA NA KARIN MAZAUNAI HAR YAU ALLAH BESA AN DACE BA TO INSHAA ALLAHU MATSALAR KI TA KAU INJINI NI AUTAR AMBATO

MAGANIN NONO
Kina fama da zubewar breast komai lalacewarsa kokuma dai Allah be azurtaki dasu sosai ba to ni na baki guarantee kwana 7 kachal zakiga chanji idan har kikai amfani da magani na 🥱🙅🏽‍♀️🤌🏽🙌🏻

MAGANIN HIPS
Kinasan ki kara mazaunai ki kaddara matsalar ki takau DOMIN maganin mu sadidan ne inkinyi amfani dashi Saikin dawo ko kin kawo wata wannan shine taken maganin mu masu bukatar karin bayani ko samun maganin mu zaku tuntubemu akan wannan number ta WHATSAAP number 0812 681 3773

SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA 🤭INJI AUTAR AMBATO

Ina juyowa naga Azgar a tsaye akan ƙafarshi ya fito daga mota.
Wani abune ya tsirgamun. Allahu Akbar Azgar na Ammi, dama nasan zai yi wuya Azgar ace ya tafi ya barni.
Yana ƙarasowa ya durƙusa a gabana ya fashe da kuka.
"Ammi ko ki zo mu tafi, ko in zauna in ƙare rayuwata dake, ko Abba ya zauna tare damu"
Kafin in bashi amsa Qasimu da Mijinyawa sun ƙaraso inda muke a tare suka ɗaga Azgar. Mijinyawa na shirin juyawa dashi, yaron sai ya turje. Da mamaki gami da tsoro ya dubi yaron.
"Me kake nufi Azgar a hannun Amminka kake son in barka. Ko ko me kake son faÉ—amunne?"
Qasimu yace"
"Abi a hankali Mijinyawa. Azgar menene yake faruwa. Menene matsalar?"
Ya kasa magana sai ajjiyar zuchiya kawai yake yi. Ni dai ina tsaye ina kallon ikon Allah.
"Nace ne tazo mu tafi. Ko ni in zauna a wajenta, ko kuma Abba ka haƙura da zuwa Katsina. Bazan iya barin kusa da'ita ba wallahi, bazan iyaba. Kuyi mun rai"
Qasimu ya dubeni, ni kuma Azgar nake kallo. Inaji da ana iya kyautar rai a bawa wani. To raina fansane akan Azgar, akan wannan abun da yayi. Ya burgeni sosai.
"Hindu kinji abinda Azgar yace. Me zaki ce game da abinda yace"
"A'a Qasimu kada mu yi haka da kai, Azgar dole zai bini, bai isa ya juyani ba wallahi bai isa ba. Shi da Hindu ai ba haifata suka yi ba. Kai nafi Hindu taurin kai da ƙwaƙwaduba"
"Ya ko isa tunda yara na uwane a musulunci, har sai sun mallaki hankalin kansu suke da zaɓi kamar dai Azgar da yake da cikakken hankali. Ai ko kotu akaje baka da ikon tursasama Azgar. Tunda dai yaro ni ya zaɓa baka da iko. Wallahil Azeem naso su zaɓeka kamar yadda suka nuna. Ni da kake ganina babu wanda dan ya shigo rayuwata, fitarshi zai girgizani kai ka sani. Amman yaro a barshi da kamilin hankalinshi ya zaɓama kanshi abinda yake so shine kawai"
Kallona Mijinyawa yayi da maɗaukakin mamaki, ni ko ko gezau ina kallonshi sheƙeƙene dan bana mishi kallon mutumci sam, ina raga mishi domin yaranshi ne kawai, da kuma alkhairan baya.
Fuuu ya isa wajen mota ya jawo Sabira yazo ya dure mun ita ya juya, cikin maÉ—aukakin fushi marar misaltuwa
"Baba"
Sabira ta kirashi, cak ya tsaya bai ko iya juyowa ba. Sai itace ta isa inda yake. Muna tsaye muna kallon almara, wallahi yarinyarnan ta rufe idanunta ruf.
"Ni kai zan bi Baba"
Hannayenta ya riƙe ya kaita mota, har yana murmushi, tare da juyowa ya dubi Azgar, ya dubeni.
A sanyaye Qasimu yace.
"To shikenan yara sun raba kansu. Sai dai kash naso ace Sabirace ta zaɓeki ba Azgar ba. Riƙon mace sai mace Hindu. Kash ni banso wannan tarihi ya yanke a iyakar haka ba. Amman a jikina inajin tarihin rayuwar soyayyarku hutu kawai zai tafi, da zaran kun huce, zukata sun yi kewar juna, zaku yi mannewa iriyar wacce zaton wani bai zata ba"
Hannayen Azgar na riƙe kawai ya dawo gefena.
Qasimu ne ya sauke mai kayanshi daga motar, suka ja suka wuce. Muna tsaye mun yi shiru.
Juyowar da zanyi sai naga Azgar na layi zai faɗi ƙasa. Kafinma in tallafoshi ya faɗi ƙasa sumamme.
Nan na shiga jijjigashi ina ambaton sunanshi, ina jin kaina na yamutsewa makarai na neman dokeni, ga yarona sanɓal a kwance. Sai jijjigashi nake yi ina ambaton Allah.
Kawai sai naji na dena ji, na dena gani É—if na rasa numfashina.
Kunji wani ƙudurar Allah.
Chapter 83 · 0% Book details